Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Toungo: Garin da ya yi wa kansa maganin masu satar mutane
Karamar Hukumar Toungo da ke jihar Adamawa na cikin irin wadannan yankuna inda kungiyar sintiri ta 'yan banga ta mike tsaye domin kare yankin wanda a shekarun baya ya sha fama da matsalar garkuwa da mutane.
Abokin aikinmu Salihu Adamu Usman ya bi tawagar 'yan sintirin yayin da suke aikin kare garinsu kuma sun yi amfani da babura masu kafa biyu wajen zuwa kauyuka dake tsakanin Najeriya da jamhuriyar Kamaru inda daga can ne masu satar mutanen ke shigowa cikin garin Toungo.
Yadda tafiyar ta kasance
Akalla matasa 300 ne ke cikin wannan kungiyar ta sintiri dake yunkurin kare garin Toungo daga barazanar barayin mutane.
Kungiyar ta samu tagomashi ne a shekarun baya-bayannan sakamakon dauki dai-dai da aka rika yiwa masu abun hannu a karamar hukumar Toungo da kewaye.
Bayan tashi daga ofishin 'yan sintirin dake cikin kwariyar garin, mun dauki babban titin da zai kaimu kan iyakar Najeriya da Kamaru to amma da mukayi tafiya kamar ta minti goma sai muka ratse zuwa wani sansani inda 'yan sintirin suka sauya tufafi dake jikinsu kuma sukayi shigar burtu domin badda kama, daga nan ne muka sake hawa Babura muka nufi daji.
Bayan tafiyar da bata wuce kilomita biyar ba sai kwamandan 'yan sintirin Khalid Muhammad ya bada umarnin tsayawa a wani fili mai fadi wanda idan ka daga ido ka hangi gabansa babu abunda zaka gani sai daji mai duhin gaske.
Ashe, gandun dajin nanne na Gashaka Gumti da ya fi ko wani daji girma a Najeriya.
Kwamanda Khalid yace daga cikinsa ne masu satar mutane ke kutsa kai cikin garuruwan Toungo da Ganye da kuma Jada su saci mutane kuma su haura da su kan manyan duwatsu da tsaunuka domin neman kudin fansa a shekarun baya, kamun tashi tsaye da sukayi suka digawa matsalar aya.
To da yake karamar hukumar Ganye na makwabtaka da ta Toungo kuma barayin mutanen na tserewa dazukan yankin, na tambayi kwamandan 'yan sintirin Ganye Idris Julde wanda ke cikin tawagar tamu yadda suke taimakawa wajen cafke bata garin.
"Muna hada kai tare da 'yan bangan Pulaaku da maharba da kuma sauran jami'an tsaro sai mu haura kan wadannan duwatsu mu farwa barayin ba tare da saninsu ba, a haka muke cin nasara kansu".
Matsaloli da 'yan sintirin Toungo ke fuskanta
Duk da tasirin aikin sa kai da sukeyi, 'yan sintirin na fuskantar matsaloli dake sanyaya musu gwiwa.
Da yake cikin tawagar tamu akwai mataimakin kwamandan 'yan bangan Toungo Umar Sulaiman Dan Rimi na bashi damar fada mana matsaloli da ke ci musu tuwo a kwarya.
Dan Rimi yace "muna da matsalar kayan aiki, abokanen gabanmu wadanda suka addabi mutane suna zuwa ne da manyan makamai yayin farwa jama'a, Mu kuma bamu da irin wadannan makaman nasu".
Na tambayi Kwamanda Khalid yadda suke samun kananan makamai da suke amfani da su.
"Sai idan mun saida amfanin gonakinmu da kuma 'yan dabbobi ne muke sayan wadannan da ka gani". Inji Kwamanda Khalid.
Ya kara da cewa waninsu yaji rauni yayin artabu suna shan wahala wajen jinya domin kuwa su kadai ake bari da dawainiyar.
Yadda zaku kauda barayin mutane a yankunanku
Bayan ganin irin nasarar da garin Toungo ya samu wajen kauda masu satar mutane wadanda a shekarun baya suka zamewa karamar hukumar karfen kafa, na tambayi shugaban tawagarmu Kwamanda Khalid yadda suka cimma wannan nasarar.
"Babban abunda yataimakemu shi ne hadin kai, Hakimin gari da wani jami'in tsaron farin kaya na SSS sun bamu gudunmawa sosai tare da karfafa mana gwiwa.
Sannan matasanmu sun nuna rashin tsoro da jajircewa inda suka shigo cikin wannan kungiyar ta sa kai." Inji Kwamanda Khalid.
Ya kara da baiwa yankunan dake fama da matsalar tsaro shawarar kwaikwayon abunda sukayi na cire tsoro da jajircewa da hadin kai da aiki da shugabannin gari da kuma sauran jami'an tsaro kamar yadda sukayi a Toungo har suka samu nasarar kakkabe barayin mutane.
A yanzu dai an karya lagon masu satar mutane a yankin kuma al'ummar gari na jinjinawa bajintar wadannan 'yan sintirin da suka tsaya domin kare kasarsu ta gado daga barazanar da a baya ta nemi durkusar da ita.
Sharhi
Dalilin kawo muku labarin 'yan sintirinnan shi ne fito da wani abu da al'umma za ta iya kwaikoyo daga wadannan jajirtattun mutane na garin Toungo da suka tashi tsaye domin kare garinsu daga barazanar tsaro na garkuwa da mutane musamman a wannan lokaci da satar mutane ke addabar duk shiyoyin Najeriya.
Idan kuna fama da ita a yankinku, sai ku gwada irin wannan salon na jajircewa da hadin kai da al'ummar Toungo suka nuna inda a yanzu suka samawa kansu maganin ciwo dake damunsu.