Yadda gyaran babban titin Gombe zuwa Adamawa ke tafiyar hawainiya

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Matafiya da ke bin manyan titunan da suka hade jihohin Gombe da Adamawa da kuma Taraba a arewa maso gabashin Najeriya na kokawa kan tsananin lalacewar hanyoyi da suka hade jihohin uku.

Lalacewar titunan dai tafi kamari ne daga garin Billiri zuwa Numan da kuma Numan zuwa Jalingo.

Ko da yake gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ba da kwangilar gyara wadannan hanyoyin biyu a shekarar 2017 kan kudi sama da naira biliyan 27 amma aikin na tafiyar hawainiya.

A ci gaba da kawo muku rahotanni da BBC ke yi daga jihohin Adamawa da Taraba wakilinmu Salihu Adamu Usman ya kasance cikin matafiya da ke bin wadannan hanyoyin ga kuma rahotonsa.