Ku San Malamanku tare da Muhammad Kabir Dan Yaya

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Muhammad Kabir Dan Yaya
An wallafa

Wani malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Muhammad Kabir Dan Yaya ya ce babban abin da ke sa masa farin ciki a rayuwa shi ne ganin ya kasance silar samar da ci gaba da taimakon juna a cikin al'umma.

Malamin ya ce akwai wasu lokuta da ya ke taimakawa mutane wajen ganin sun samu aikinyi, domin ba shi da buri da ya wuce taimakawa wajen kawar da talauci a cikin al'umma.

Sheikh Muhammad Kabir Dan Yaya ya shaida hakan ne a lokacin tattaunawa da shi a shirin Ku San Malamanku na BBC.

Sannan ya shaida cewa yana karban tambayoyi da dama daga wajen mutane musamman kan aure da batun da suka shafi saki ko zamantakewa.

Rayuwarsa

An haife Sheikh Muhammad Dan Yaya a ranar 15 ga watan Mayun 1972 a birnin Maiduguri.

Ya yi karatu a gaban mahaifinsa har zuwa ga saukar Alkur'ani sau 3, sannan ya yi karance-karancen litattafan addini da dama.

Akwai lokacin da mahaifinsa ya tura shi Potiskum domin karo ilimin addinin sannan daga baya ya dawo Maiduguri domin karantun Boko.

Malaman ya ce a cikin garin Maiduguri ya yi karantunsa na Boko har matakin digiri da digirin na biyu a jami'ar Maiduguri inda ya karanci fanin addinin Musulunci.

Haddar Alkur'ani

B

Sheikh Muhammad Dan Yaya ya shaida cewa lokacin karatunsa bai fuskanci wahala ba ko kalubale wajen hadda, ya kasance mai saurin gane karatu, kuma tun yana karami suratul Kaafiroon ke burgeshi.

Ya kasance mutum mai jindadin karanta suratul Yusuf, saboda idan yana karatu sai ya ga kamar duk abin da ake cewa ya faru a gabansa.

Sanna ya ce galibi tambayoyin da mutane suka fi masa a kan aure ne da hukunce-hukunce saki, yana samun mutane da dama da ke tambayarsa ya za su yi idan sun yi saki suna neman sulhu.

"Ba ni da wani sirri na daban duk ilimina a Alkur'ani na samo shi, duk abin da ake nema idan an zo wajena daga batun Ilimi da dukiya da aure da sauransu cewa nake amsa na cikin Alkurani.

"Sannan idan mutane na neman tsari nakan basu Ayoyin Alkur'ani wanda sai su je su karanta."

Farin ciki da kunci

Daya daga cikin abubuwan da suka taɓa farantawa Malam Muhammad rai a rayuwa shi ne tafiyarsu aikin Hajji tare da mahaifinsa, duk sanda ya tuna hakan yakan zub da hawaye.

Kuma duk lokacin da ya koma Saudiyya yana musu addu'a don yana tunawa dasu, in ji shi.

Mutuwar Mahaifiyarsa ce ta girgiza shi sosai, domin ya shiga cikin kunci sosai.

Babban abin kuma ke sa masa farin ciki a cikin al'umma shi ne ganin mutane na samun cigaba da kauna da taimakon juna.

Sannan yana jindadin ganin yadda yara ke haddar Alkur'ani amma wani lokaci yana jin takaici idan yara sun yiwa iyayensu karya kuma su yarda ba tare da bincike ba.

Abinci da Buri

A ɓangaren abinci yana son tuwon semovita da miyan kuka ko kubewa, sannn yana son dankalin turawa.

Malamin yana da aure, matarsa guda da kuma yara 8.

Burinsa shi ne ci gaba da karatu a kasashen duniya don ganin ya zama ɗaya daga cikin fitattun malaman duniya da ke da'awar addinin musulunci.