Abu shida da 'yan Najeriya suka fi kewa game da Twitter

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin 16 ga watan Satumban 2021 ne aka cika kwana 100 tun bayan da gwamnatin Najeriya ta dakatar da amfani da shafin Twitter a kasar.
Sai dai har 'yanzu yan Najeriya ba su daina nuna damuwarsu ba kan matakin gwamnatin na rufe shafin sada zumuntar.
A ranar 4 ga watan Yuni ne gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dakatar da amfani da Twitter a Najeriya.
Daga baya kuma sai hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasar ta bukaci kamfanin Twitter da ya zo ya yi rijista idan har yana son ci gaba da aiki a Najeriya.
Kuma tun a lokacin kamfanoni da ma'aikatu a kasar suka ja layi daga amfani da Twitter ta kowace hanya don gudun haduwa da fushin gwamnati.
Ga jerin abubuwa shida da al'ummar Najeriya suka yi kewa tun bayan dakatar da Twitter.
1. Tabka Muhawara
Daya daga cikin abubuwan da mutane ke kewa game da Twitter shi ne tabka muhawara a duk lokacin da wani muhimmin abu ya faru.
Nan da nan za a fara muhawara da musayar mabambantan ra'ayoyi kan wani batu da ke faruwa a kasar.
A kan kirkiri maudu'i, kuma kan ka ce kwabo zai karade shafin a yi ta fama. Iirn wannan abu kan saka wasu masu bin shafin nishadi.
A wasu lokutan irin wadannan muhawara da maudu;ai har su kan sanya hulumomi sauya wata matsayarsu ko magance wani abu, ko kuma su sa batun da ake magana a kansa ya yi matukar tasiri a kasar.
2. Tallata sana'o'i
Da dama yan Najeriya musamman matasa kan yi amfani da Twitter don tallata hajarsu.
Kuma tun bayan rufe kafar irin wannan damar ta wuce su. Duk da cewa har yaznu wasu kan shiga ta bayan fage, amma dai za a iya cewa kasuwa ta yi kasa sosai.
Ba ga masu tallan haja ba har ga kamfanonin yada labarai haka abin yake. A baya su kan samu kasuwar a karanta labaransu sosai a Tuwita, amma ga alama yanzu kam komau ya yi kasa.
3. Sanin abin da ke faruwa a sassan duniya
Wani abu da 'yan Najeriya ke kewa da rufe Twitter shi ne damar sanin me ke faruwa a fadin duniya, musamman ga wadanda suka dogara ga Twitter don sanin halin da duniya ke ciki.
Twitter na daga cikin kafafen da kamfanoni da gwamnatoci ke amfani da su don fitar da sanarwa.
Sannan kuma a nan 'yan Najeriya ke iya ganin maudu'an da ake tattaunawa da ke tashe a wasu kasashen a kowace rana.
4. Tsokana da gatse
Wani abu da mutane su ke kewa game da Twitter shi ne gatse da raha da kuma tsokanar juna.
A lokuta da dama wasu kan kirkiri wani maudu'i don takalar magana da neman a tabka muhawara.
Ana yawan yada irin kalaman gatse da 'yan Tuwita ke amfani da su wajen bayar da amsar wasu tambayoyi a sauran shafuka.
Irin wannan abu na nishadantar da sauran mutane ma da ba sa bin tuwita din.
5. Gulma
Mutane da dama sun daina jiyo labaran kanzon kurege da gulma musamman wani lamari da ya shafi rayuwar iyalan sanannun fuskoki.
Duk da a na samun irin wadannan labarai a na yadawa a shafukan Instagram da Facebook, sai dai ba sa wani tasirin a zo a gani da suke yi saboda ba a Twitter a ka bulguta su ba.
6. Zumunta
Rashin Twitter ya sa mutane sun daina sada zumunta da abokanansu a kafar sada zumuntar.
Kewar juna da kuma sauran ababen da aka saba da su sun sa yan Najeriya musamman matasa ke ci gaba da kira ga gwamnati, da ta duba yiwuwar dage dakatarwar da ta yi wa Twitter.











