Ku san Malamanku: Tare da Sheikh Atiku Muhammad Balarabe Zawiya Gusau

An wallafa

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Atiku Muhammad Balarabe Zawiya Gusau ya ce babban burinsa shi ne zawiyar da suka gada daga iyaye ta zama kamar Jami'ar Azhar da ke Masar.

Malamin ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC, a kuma cikin shirinmu mai taken "Ku San Malamanku".

Zawiyar da mahaifansa suka assasa a baya a yanzu tana da ɓangaren nazire da firaimare da sakandire, akwai kuma ɓangaren difloma da kuma sashen babban karatun addinin Musulunci na wannan zawiya.

"Mahaifunmu Shehi Balarabe ya yi bauta a wajen Shehu Ibrahim Barhama daga nan bayan da za a sallame su ne Shehu ya ce su gina makarantun al-Kur'ani a yankunansu.

"A yau wannan zawiya ta samar da wadanda suka je musabakar duniya suka ci, wasu sun yi na ɗaya wasu kuma sun ci kyautukan da za a yi ta yaba wa har ranar gobe," in ji Malam Atiku.

Ya ce ya so mahifun nasa yana da rai ya ga wannan abin alfahari.

A gaban mahaifina na fara karatu

An haifi Malam Atiku a garin Gusau da ke Zamfara a shekarar 1955, kuma ya fara karatunsa a gaban mahaifinsa, dama gidansu gidan zawiya ne.

Malam ya yi karatu a hannun malamai da dama ciki har da su Malam Boyi wani wanda ya koyar da mahaifinsa kuma daga baya shi ma ya tsuguna gabansa ya ɗauki karatu.

Akwai Ustaz Tayyib wani ɗan Sudan yana daga cikin malaman da suka koyar da malam Atiku, "Yanzu ya tsufa yana Sudan ya zama ɗan siyasa har ya zama shugaban jam'iyya a can,".

Akwai Shehu Bello da dai sauran malamai da mafi yawansu sun mutu sun koma ga Allah.

'Ko cikin dare na ga fura zan iya dauka in sha'

Malam ya bayyana Tuwo da Miyar Kuka a matsayin abincin da ya fi so a rayuwarsa, duk da cewa akwai wasu abincin da yake so amma wannan ne a kan gaba, musamman ya sha man shanu.

Haka kuma Malam yana son fura, "Ko cikin dare na tashi na ga fura zan iya dauka na sha na koma barci" in ji Malam Atiku.

Ina shekara 18 aka mun aure, bayan shekara aka kara mun ta biyu

Mahaifinsu ya mu su komai na rayuwa, da ya ga sun kai shekarun balaga sai ya aurar da su.

"Ina shekara 18 aka mani aure, bayan shekara kuma aka ƙaran ta biyu, ko da naje kwaleji da mata na biyu," a cewar Malam.

Malam ya ce mahaifinsu ya dauke musu komai na rayuwa a lokacin da su da kuma yaransu da matansu.

Yana ba su abinci da kayan sallah tare da dauke musu wasu wahalhalun rayuwa.

'Yaƴana sun kai tara da suka hadda ce Kur'ani ciki kuma har da mata biyu, Ramlatu da Sa'adatu.