Ku San Malamanku tare da Muhammad Usamatu Abbas

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Muhammad Usamatu Abbas
An wallafa

Latsa hoton da ke sama don kallon hira da Malam Muhammad Usamatu Abbas:

Matashin malamin addinin Musulunci nan da ke birnin Katsina a arewa maso yammacin Najeriya, Sheikh Muhammad Usamatu Abbas, ya ce mahaifinsa ne ya fi yin tasiri a rayuwarsa sama da duk wani mahaluki a fadin duniya.

Malamin ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC Hausa, a cikin shirinmu mai taken "Ku San Malamanku".

Ya ce bayan karatun da ya yi na Alƙur'ani da na zaure a matakin farko a hannun mahaifinsa, ko a gobe yana iya bude littafi ya durkusa gaban mahaifin nasa domin daukar Ilimi.

Ya yi karatu a wuraren malamai da dama, ciki har da yayansa da kakansa amma gudunmawar da mahaifinsa ya ba shi ba za ta taɓa misaltuwa ba.

Matashin Malamin, wanda aka haifa a shekarar 1989 a unguwar Gambarawa da ke jihar Katsina, ya ce gidansu gidan ilimi ne abin da ya ba shi damar samun karatun addini da wuri kuma ya ba shi damar tserewa sa'anninsa.

Tarihin rayuwarsa

Muhammad Usamatu ya shafe lokuta masu yawa yana karatu a gida tun daga wajen mahaifinsa da kakansa da yayansa da kuma wasu manyan almajiran gidansu da suka samu rabauta da ilimi mai zurfu.

"Da akwai malaman da na yi karatu da dama a gabansu, a yau duk sun dawo suna daukar karatu a wurina."

"Ban fara karatun zamani ba sai da na kammala saukar Alƙur'ani mai girma, kuma kaf karatun da na yi zuwa digiri na farko a Katsina na yi su", in ji Malam Muhammad.

Malamin ya ce ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar al-Ƙalam da ke Jihar Katsina a 2014, sannan ya tafi Yamai da ke Jamhuriyar Nijar inda ya yi digirinsa na biyu.

A 2016 malamin ya samu damar yin digiri na uku kuma ya kammala a 2020.

'Shekara ta 23 lokacin da na fara limancin masallacin Juma'a'

Malamin ya samu aiki a Jami'ar al-Ƙalam da ke jihar Katsina, inda yake kowarwa a Sashen koyar da General Studies.

Malam Muhammad ya fara jan sallar Juma'a a masallacin Abubakar Saddiq da ke garin Katsina, ya fara limancin Juma'a a masallacin tsakanin 2012 zuwa 2013.

"Ina ayyuka irin na gadon gidanmu wato koyarwa, da magariba zuwa isha'i a kullum muna karanta darussa daban-daban.

"A ranar Asabar ne kawai nake hutawa, amma sauran ranakun duk akwai abin da nake karantar da ɗalibai.

"Ina karantar da ɗalibai a kan irin tsarin koyarwar zaure, amma shi ba ko da yaushe ba kamar yadda ake yin na masallaci," in ji Malamin.

Ya kara da cewa da yawa daga cikin wadanda suka koyar da shi a baya, a yanzu sukan je gabansa domin koyon wani abu na daban a fagen ilimi.

Namiji ɗaya da mata biyu

Malam ya ce yana da mata biyu da yaransa uku mata biyu da kuma namiji daya.