Yadda za ka ɓata ɓat a Japan: Kamfanonin da ke taimaka wa mutane su 'yi layar zana'

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Bryan Lufkin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
- An wallafa
A fadin duniya, kama daga Amurka, da Birtaniya, da Jamus, wasu mutane kan yanke shawarar su yi ɓatan-dabo daga rayuwarsu ba tare da sake jin ɗuriyarsu ba - su bar gidajensu, da ayyukansu, da iyalansu da tsakar dare su fara rayuwa ta biyu, kuma ba tare da yin waiwaye ba.
A kasar Japan, ana yi wa wadannan mutane laƙabi da "jouhatsu". Wata kalma ce da yaren Japananci da ake nufi a Turance, wato kamar yadda tururi ke bin iska ya ɓace, kuma ana nufin irin mutanen da ke surarewa su bi iska, su kuma ci gaba da ɓoye inda suke - har na tsawon shekaru masu yawa.
"Na gaji da hulɗar dangantaka ta mutane. Na dauki ƙaramin akwatina kana na ɓace,'' in ji Sugimoto, mai shekara 42, wanda yake amfani da sunan iyalan gidansu a yayin bayar da labarainsa. ''Na kawai tsere.''
Ya ce a can karamin garinsu, kowa ya san shi saboda iyalansa da sunan da suka yi a harkar kasuwanci a garin, wanda ake sa ran nan gaba Sugimoto shi zai jagoranta.
Amma kasancewa cikin wannan matsayi da nauyi a kansa ya haifar masa da damuwa, daga nan ne cikin gaggawa ya bar garin har abada kuma ɓai fada wa kowa inda ya dosa ba.

Asalin hoton, Getty Images
Daga ƙangin basussuka zuwa auren da babu soyayya, dalilan da ke ingiza jouhatsu su "ɓace" na da dama.
Ko da kuwa wadanne irin dalilai ne, su kan nemi kamfanonin su taimaka musu hanyar da za su bi. Ana kiran su da ayyukan '' tafiyar dare'', hanyar da ke saka mutum ya zama jouhatsu.
Suna taimaka wa mutanen da ke son su ɓace gaba daya don nesanta kan su daga rayuwarsu, kana su samar musu da wurin zama a wuraren da ke asirce.
"Galibi, dalilan yin ƙaurar wani abu ne mai ma'ana, kamar shiga jami'a, ko samun sabon aiki ko kuma aure.
''Amma kuma akwai ƙaurar ta bakin ciki - ga misali, kamar kora daga jami'a, ko rasa aiki ko kuma tserewa daga wani wanda ke ta fakon ka,'' in ji Sho Hatori, wanda ya kafa kamfanin '' tafiyar dare'' a cikin shekarar 1990 lokacin da tattalin arzikin kasar Japan ya kara wata bunkasa.
Da farko, ya zaci karayar arziki ce kawai za ta ingiza mutane tserewa matsalolin rayuwarsu, amma nan da nan ya gano cewa ''dalilan zamantakewa'', kan haddasa.
"Abin da muke yi shi ne mu taimaka wa mutane su fara rayuwa ta biyu,'' ya ce.
Masanin kimiyyar halayyar dan adam Hiroki Nakamori ya jima yana gudanar da bincike kan jouhatsu har na tsawon sama da shekara goma.
Ya ce an fara amfani da kalmar 'jouhatsu' wajen bayyana mutanen da ke yanke shawarar yin batan-dabo a baya cikin shekarar 1960.
Rayuwa ta biyu
Alkaluman rabuwar aure a baya da kuma yazu ba su da yawa a kasar Japan, don haka wasu mutanen ke yanke shawarar cewa abu mafi sauki na shine bari ko kuma kaurace wa abokin zama ta wannan hanyar a maimakon bin dogon matakin raba aure a hukumance.

Asalin hoton, Getty Images
"Yana da matukar sauki ne ka yi layar zana a kasar Japan," in ji Nakamori. Ana boye sirri sosai: mutanen da suka bace kan rika cirar kudi daga na'uarorin cirar kudin na ATM ba tare da an gan su ba, kuma iyalansu ba za su iya ganin su a cikin bidiyon da kyamarra tsaro ta nada ba a yayin bacewar.
'' 'Yansanda ba sa shiga cikin lamarin ina ba da wani dalili ba - kamar aikata laifi ko hadarin mota. Abinda iyalai za su iya yi kawai shi ne biyan kudi masu yawa ga masu bincike na zaman kan su. Ko kuma su jira. Sikenan.''
'Na kadu matuka'
Iyalan da aka bari a baya - da kuma abubuwan da batun neman 'yanuwansu da suka zama jouhatsu din ke haifarwa - yana da matukar cin rai.
''Na kadu matuka,'' in ji wata mata wacce ta zabi kada a ambaci sunata, kuma wacce dan ta mai shekaru 20 ya bace kuma bai tuntube ta ba har yanzu.
"Ya gaza, bayan da ya bar aikinsa har sau biyu. Me yiwuwa ya shiga tsananin damuwa ne da gazawarsa.'' Ta tuka mota zuwa wurin da ya saba zama, ta duba bangaren kana ta jira a cikin motarta har na tsawon kwanaki don ganin ko zai bullo. Amma bai bullo ba.
Ta ce 'yansanda ba su taimaka ba, kana ta ce sun fada mata cewa za su shiga cikin lamarin ne kawai idan batun kashe kai ne. Amma tun da babu wata takarda, ba za su iya taimakawa ba.
''Na fahimci cewa akwai masu bin diddigin mutane - za a iya asarar bayanai. Me yiwuwa wannan ya zama dole. Amma kuma, masu bin diddigin da ba za su iya bincika inda 'yayansu suke ba? Duka ana yi musu kudin goro saboda kariya. Menene haka?" ta ce.
"Da wannan sabuwar doka, ba tare da kudi ba, abinda zan iya yi idan gawar ta da na ce - abinda ya rage min kawai kenan.''
Masu batan-dabon

Asalin hoton, Getty Images
Su kan su jouhats, kasancewa cikin bakin ciki da nadama na tare da akasarinsu tun bayan barin rayuwarsu a baya.
"Na kan rika yawan tunanin cewa na aikata ba daidai ba,'' in ji Sugimoto, wani dan kasuwa da ya tafi ya bar matarsa da yayansa a wani karamin gari.
"Na shafe shekara daya ban ga 'yayana ba. Na fada musu cewa na yi tafi fatauci ne.''
Nadamar da kadai yake yi in ji shi ita ce barin su da ya yi. Yanzu haka Sugimoto na zama ne a wani gida da ke nesa da gundumar Tokyo.

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin bulaguron dare da ya samar masa da matsuguni na wata mata ne da ake kira Saita, wacce kuma ke amfani dasunan iyalan gidansu don sakaya sunanta.
Ita kan ta jouhatsu ce, wacce ta taba bacewa shekaru 17 da suka gabata.
Ta ɓace ne bayan da ta sha fama da cin zarafin da ya shafi zamantakewa, kuma ta ce ''ta wani gefen, wacce ta ɓata ce - ko a yanzu ma.''
"Ina da kostomomi da dama,'' ta ci gaba. '' Akwai mutanen da suka gujewa tsananin cin zarafi na cikin gida ko girman kai da kuma son-kai.
"Ba na saurin yanke hukunci akan abu. Ba na cewa matsalarka ba ta kai ba,'' kowa yana da tasadamuwar daban.''
Ga mutane kamar su Sugimoto, kamfaninta ya taimaka masa shawo kan matsalolinsa.
Amma duk da cewa ya samu ya ɓace, hakan ba yana nufin babu sauran yanayin sa na da a tare da shi ba.









