Yadda za ku samu aiki mai tsoka na harkokin tsaron intanet

Asalin hoton, O Anaya
- Marubuci, Daga John P. Mello Jnr.
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan Kasuwancin Fasaha
- An wallafa
Daya daga cikin kutsen da Oscar Anaya ya yi nasara a kai, shi ne lokacin da ya yi a wata kwamfutarsa da ya bai wa 'yar uwarsa lokacin yana da shekara 11.
'''Yar uwata na son yin wani wasan gem, ba ta son na yi amfani da kwamfutar, don haka sai ta sanya lambobin sirri ta rufe ta,'' in ji Anaya.
Kamar wasa sai ya fara wasa da wasu lambobi a jikin kwamfutar, daga nan sai ya gano wani wuri da ya kurɗa ya gano wasu lambobi.
''Hakan ya ba ni damar shiga wajen da bayanan mutum suke, kawai sai na sauya lambobin sirrin.''
Wannan kutse da Mista Anaya ya fara yi da ƙanƙantar shekaru, shi ya zama dan mabudin shimfida kwarewarsa ta fannin tsaron intanet.
Lamarin ya dauke shi daga mai shirya wakoki zuwa mai tsarawa ko sanya ido kan tsaro ta internet a wasu shirye-shirye na kutsen intanet.
''Daman ni tuntuni ina da sanya ido kan abubuwa, 'Ta yaya mutane ke yin abin da bai dace ba?''
''Wannan kuma ita ce hanyar yin kutse, wato ka gano yadda ake yin abubuwa ta hanayr da ba a saba gani ko binta.''
Duk yadda ya so aiki a fannin harkokin tsaron intanet, lamarin ya yi kama da burinsa bai tabbata ba, sai bayan ya zage damtse wajen neman aiki a fannin bayan matsin lambar matarsa mai juna biyu.
Daga karshe ya samu kansa a wani kamfanin tsaro na intanet da IMB ke jagoranta a shekarar 2019.
Kamfanin na da mazauni a birnin Texas, a yanzu yana matsayin cikakken ma'aikaci karkashin tawagar kamfanin X-Force Red Team, a matsayin mai kutse a shafukan intanet din kamfanoni domin bayyana bayanan da ake boyewa.
Matsayin da Aryana ya samu kansa a kai, misali ne kan hanyoyin da masu fafutuka ke yi a ayyukan da suke gudanarwa domin zama mashahurai.
Aiki ne da ake biyan albashi mai tsoka. Mafi kankantar albashin da ma'aikatan harkokin tsaron intanet ke karba, shi ne Yuro 62,000 (wato dala 74,000), kamar yadda cibiyar da ke sa ido kan bayanan tsaro ta Amurka ta bayyana.

Asalin hoton, Sigmund
Akwai kuma sauran fannonin da ake bukatar daukar ma'aikata domin cike gurbin, duk da cewa an samu ƙaruwar rashin ayyukan yi daga miliyan hudu a shekarar 2019, zuwa miliyan 3 da dubu 100 a shekarar da ta gabata.
''Kasuwar fannin na garawa.'' in ji Ida Byrd-Hill, shugaba kuma wanda ta kirkiri kamfanin tsaro na Automation Workz, mai mazauni a Detroit ta bayyana.
"Duk da yadda ake kai wa bayanai hari ta internet, da satar bayanai ana tsananin bukatar karin ma'aikata a wannan fannin,'' in ji ta.
Wannan buƙatar ta fara yawa da jan hankali. " Abin da masu ɗaukar aiki suke buƙata na son fara sauyawa," in ji Clar Rosso, shugabar (ISC)².
"Kamfanoni na fuskantar matsalar rashin ƙwarewa a ɓangaren tsaron intanet, don haka sun fara tunani na daban kan waɗanda ya kamata su ɗauka," in ji ta.
"Wannan ne ya fara kawo tunanin cewa za a iya fara koyar da tsarin a aikace, amma akwai wasu fannonin tsaron intanet da ke da wahalar koyarwa," a cewarta.
Ross ta ce bincike na baya bayan nan ya gano cewa kusan rabin mutanen da suka shigo hakarar tsaron intanet waɗanda ba su karanci fasahar sadarwa ba ne ko kimiyar kwamfuta.

Labarai masu alaka

Yanzu manyan kamfanoni sun sauya tsarin yadda suke daukar ma'aikata.
"Hanyar zuwa tsaron intanet ta bambanta sosai," in ji Wil Rockall, na Deloitte ɗaya daga cikin masana fasahar intanet a Birtaniya.
"Wasu mutane suna da ilimin da ya shafi fasaha da kwalin digiri da kuma samun horo kan fannin tsaron intanet, amma yawancinsu da muka ɗauka sun fito ne daga ɓangaren da ba na fasaha ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa, wannan fanni ne mai faɗi sosai, tsaro ya shafi abubuwa da dama don haka akwai wurare da dama da mutane suka samu ƙwarewa daban-daban.
Mista Rockall ya ce fannin ya samu sauyi sosai a shekaru 20 da suka gabata. "Ba wai mutane da ke da ƙwarewar dannar keyborads suna wasu ayyukan fasaha ba. Kasuwanci ne da ke buƙatar mutane masu ƙwarewa.
Yayin da za a ci gaba da fuskantar ƙarancin ma'aikata a fannin tsaron intanet, masana sun amince cewa faɗaɗa gasa tsakanin masu neman aiki mataki ne mai mahimmanci wajen magance ƙarancin.
"Abin da hakan ke nufi a yanzu shi ne tafiya da mutane daga fannonin da ke da alaƙa tare da kuma sake horar da su.
"Ko kuma taimaka wa kwalejoji su inganta tsarin horarwa don samun ingantaccen tsari," in ji babban jami'in kamfanin DHI Group, babban kamfanin shafin ɗaukar ma'aikatan fasaha na Dice high-tech job.

Asalin hoton, P Farnsworth
Jim Johnson babban mataimaki a ɓangaren fasaha na Robert Half, babban kamfanin ɗaukar ma'aikata, ya ƙara da cewa kamfanoni ya kamata su ƙara ƙaimi wajen tantance ma'aikatan da suka dace.
"Ya kamata kamfanoni su yi aiki da al'ummarsu tare da makarantun cikin gida da kuma kamfanonn sadarwa don samun goyon baya da kuma taimaka masu wurin ci gaba da tantance waɗanda suka dace," in ji shi.
"Ɗaya daga ciki shi ne tsarin ɗaukar masu son sanin makamar aiki ko kuma bayar da horo ga ɗalibai, zai taimaka wa ɗaliban su samu ci gaba cikin gaggawa."
Heather Ricciuto, ta IBM Security ɗaya daga cikin manyan kamfanonin tsaro na Intanet, ta ce shekaru da dama IBM ta gano cewa ba za ta iya ci gaba da ɗaukar ma'aikata ba daga tsoffin wuraren da aka sani ba.

Asalin hoton, david huff photography
"Ba za mu iya ci gaba da ɗaukar mutane masu digiri na ɗaya da na biyu ba daga manyan jami'o'i.
"Mun fahimci cewa ya kamata mu fara neman waɗanda ba fannin suka karanta ba," in ji ta.
"Muna ɗaukar mutane da suka kammala digiri, da waɗanda suka samu horo na intanet ko suka koyar da kansu."
"Akwai ayyuka da dama na tsaron intanet a duniya, mun kasa cike su da dukkanin masu digirin jami'a. Babu mutane masu yawa da suka yi digiri a fannin domin cike guraben ayyukan."
Bambancin zai kuma taka muhimmiyar rawa wajen faɗaɗa hammayar neman aiki sosai da kuma cike gibi.






