Shin an kusa fara amfani da rigar da ke sa mutane tashi sama?

Asalin hoton, Leigh Coates
- Marubuci, Daga Bernd Debusmann Jr
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan harkokin kasuwanci
- An wallafa
Leigh Coates ya ce a duk lokacin da kake tashi sama kana shawagi a iska sanye da kayan da ke sa mutum tashi sama, ji za ka yi tamkar wani jarumi.
"Wani irin yanayi ne mai dadi marar misaltuwa," a cewar mai ritaya matuƙin jirgin helikwafta a Amurka. "Ji za ka yi kawai za kan iya tashi sama."
"Duk da dai da farkon farawa akwai matuƙar wahala."
A shekarun 1965, riguna masu tashi sama sun yi suna a duniya, lokacin da wasan kwaikwayon James Bond ke tashe,
'Yan bindiga sun biyo ftaccen dan leken asirin da marigayi Sean Connery ya fito akai, a saman kwanon French chateau, wajen da ya sanya rigar tashi sama tare da tserewa daga wajen.
Lamarin da ya karawa shirin armashi da dandano, musamman ma dai ga riguna masu tashi sama, sai kuma aka shigo da Bell-Textron, a matsayin "mutumin makamin roka" ga sojin Amurka a shekarun 1950.
Yayin da sojojin Amurka ke cewa, akwai matukar hadari amfani da shi, sai aka bar jami'an sirri na 007 sukai amfani da ita.

Asalin hoton, Getty Images
Shekaru 56 kenan, an kara inganta fasahar riguna masu tashi sama, da kayan aikin, tare da gwada su ta fannoni da dama, da amfani da su , misali idan za a tura jami'an kartakwana domin aikin ceto ko ga jami'an tsaro.
A watan da ya wuce an nuna wani jirgin ruwa da ke atisaye ta amfani da rigar tashi sama, an yi amfani da igiya ta jirgin helikwafta.
Sai dai ba batu ne da ba a cika tattaunawa akai ba kan amfani da rigar tashi sama. Ma su sa ido na bayyana matsalolin da ka iya tasowa da suka hada da na kariya da muhalli, duk da cewa akwai wani dan inji da ke bayan mutum da ke rike mutum da ba da kariya idan an samu cunkoso a sama.
Sai dai wasu kamfanoni a Amurka da Birtaniya, su na bai wa jama'a damar damar amfani da rigar tashi sama, wadda ke makale da wani karfe da ke hana su tashi can kololuwar sama domin kaucewa matsala.
Shin wannan zai fadada tare da samun karbuwa? ko za a cire igiyar da ke rike mutane?

Asalin hoton, Reddot Media
"Ina ganin za a fara amfani da wannan fasahar a lokuta muhimmai, kafin a fara amfani da shi sosai," inji Benjamin Akih, farfesa a fannin karatun injiniya a jami'ar Syracuse da ke birnin New York.
"Ina tunanin jami'an kahe gobara, da na asibiti da masu aikin ceto, da jami'an tsaro ne suka dace da amfani da rigar nan, saboda yawan amfani da rigar tashi sama a wannan lokacin da muke ciki zai taimaka bunkasa ayyukansu, sannan daga bisani a fadada zuwa masu amfanin kashin kai ko matafiya."
Daniel Levine, kwararre a cibiyar Avant-Guide da ke New York ya maida hankali kan matafiya da 'yan kasuwa, ya ce samar da rigunan tashi sama zai yi matukar tsada, sai dai ba zai zama abin damuwa ba nan gaba idan mutane suka saba amfani da ita, sannan ba za a dinga daure su domin kar su tashi sama kololuwa.
"Nan da shekaru biyar masu zuwa, watakil a samu wadanda za su dinga karbar hayar rigar tashi sama a wasu kasashe, inda kamfanonin inshora ba za su yi musu bukulu ba," inji shi. Ya kara da cewa "Idanu na sun karkata zuwa hadaddiyar daular larabawa."
"Da zarar fasahar ta zama sassauka, za a fara amfani da ita fiye da mota kawai dan jin dadin sufurin wucin gadi."
Sabbain fasahar kasuwanci, sun maida hankali kan bunkasa fannin da saisaita bunkasar tattalin arziki.

Cikin kamfanonin da ke samar da rigar tashi sama akwai, Jetpack Aviation, da ke California da aka samar da shi a shekarar 2015. Kamfanin ya samar da rigunan nau'i daban-daban masu yawa.
A wani bangaren kuma, ana duba yiwuwar amfni da rigar domin bunkasa ayyukan sojoji da jami'an tsaro, kamfanin ya na ba da damar yi wa jama'a atisaye kan yadda za su yi amfani da rigar, wadda injin da ke baya ke amfani da kananzir ko man fetur.
Fannin sufuri da ke kula da JetPackda shugabansa David Mayman ya ce ayyuka sun yi wa kamfanin yawa saboda bukatar rigar da ake nunawa cikin kwanaki biyu da ake yin atasisaye.

Asalin hoton, JetPack Aviation
Mista Mayman ya ce rigar tahi sama da kamfaninsa ke samarwa, ba ta da wuyar amfani. An yi kokarin takaita tashinta sama, wanda ke amfani da ita ya ke danna wani madanni, da kuma ya ke taimakawa mutum yin dama ko hagu.
Sannana kwai dan allon kwamfiyuta da ke dauke da bayanai ciki har da yawan man fetur, da karfin inji, da zafin yanayi da kuma karfin batiri.
Mista Mayman ya ce babu wata matsala da ami amfani da shi zai fuskanta indai ya bi komai daki-daki da bin ka'idoji.
''Ina ganin ba ka bukatar wani atisaye daga fannin sufuri kafin ka fara amfani da rigar tashi sama, ko matuki da zai taimaka maka. abin da ka ke bukata shi ne maida hankali da fahimtar abin da ka ke yi.'' inji Mayman.

Asalin hoton, Gravity Industries
Kamfanin Gravity ya yi nufin shirya wasan tsere na sama na farko, a watan Maris shekarar 2020, amma hakan ba ta samu ba saboda barkewar annobar cutar korona.
Shugaban kamfanin, Richard Browning, tsohon dan kasuwar mai ya ce ya na shirin fara yi wa mutane atisaye musamman wadanda za su shiga gasar tseren.










