Ku San Malamanku tare da Malama Murjanatu Ibrahim Kaita

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malama Murjanatu Ibrahin Kaita
An wallafa

A wannan makon shirin Ku San Malamanku ya tattauna ne da Malama Murjanatu Ibrahin Kaita daga jihar Katsina.

Malama ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha wajen neman ilmi kafin Allah ya kai ta ga samun nasarar kai wa ga matakin karatun da take kai a yanzu.

Ta kuma ce tana da burin yin amfani da karatun da ta yi wajen fadakarwa, da koyar da al'umma, musamman mata a bisa tafarkin addinin Musulunci.

Malamar kuma ta bayyana muhimmancin samar wa da karatun nata takardar shaida wacce ita ce za ta iya ba ta cikakkiyar damar bayyana duk wani abu da za a iya saurarar ta a kuma yi amfani da abubuwan da ta koyar na alkhairi.

Tarihin rayuwarta

An haifi malama Murjanatu Ibrahim Kaita a garin Kuraye da ke jihar Katsina inda nan ne garin mahaifiyarta, a shekara 1963.

Ta kuma fara karatu a makarantar firamare a garuruwa uku, kuma kasancewar mahaifinta manomi ne, an yi mata aure tun tana da shekara 11 bayan da ta kammala karatun firamare,

Malama Murjanatu na da ƴaƴa 12 ciki har da tagwaye.

Daga bisani ta sake komawa karatun sakandare wanda yake hade da karatu na Alkur'ani mai girma da kuma abubuwan da suka shafi addinin mutum tun farko.

Ta kuma yi karatu a makarantar Mai-dabino a wurin wani malami da ta ce ba za ta iya tuna sunansa ba saboda 'karancin shekaru, amma kuma ta karasa karatunta na Alkur'ani mai girma a hannun mahaifinta.

Bayan nan ne kuma a shekarar 1984 ta shiga makarantar horon malamai ta Larabci ATC, kafin nan ta yi makarantar Islamiyya ta farko a garin Katsina lokacin Sheikh Yakubu Musa shi ne shugaban makarantar.

Daga nan ne ta samu aka samu takardar cikewa don samun gurbi karatun a ATC da ya zo da shi, ya kuma zabi wadanda ya hango suna da hazaƙa kuma zasu iyayin karatun ciki har da Malama Mujanatu.

Hakan ne ya ba ta damar fara karatun sakandare a makarantar ta ATC a shekarar 1984, inda ta kammala a shekarar 1990.

A kan haka ne malamar ta dage da sanya ƙwazo wurin neman samun ilimin, ta kuma kammala da kyakkyawan sakamako a shekarar 1990.

Sai dai malamar ta shaida wa BBC cewa a lokacin babu wata makaranta da za ta ci gaba saboda a lokacin ko difloma ta sashen su babu, ba kuma ta waye da ainihin karatu a kwalejin ilimi ta FCE ba kuma a lokacin babu jami'a.

"Don haka sai can wajen shekarar 1997 sai ga Kwalejin Usman Danfodio wacce reshe ce ta Jami'ar Sokoto da suka fara daukar mata bayan sun yi shekara uku suna yaye maza.

"Na zama cikin daliban farko mata da aka dauka mu 21 kuma a nan na yi difloma kan harshen Larabci da ilimin addinin Musulunci na kuma kammala a shekarar 2001,'' in ji malamar.

Wasu na baya da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

Burin malamar

Malama Murja

''Fatana dai in gane in kuma ganar da wasu, wannan shi ne yunƙurina, don yanzu haka karatun da nake wasu na cewa ai sai in je in samu koyarwa a jami'a na ce a'a, ba zan iya wannan aikin ba.

"Abin da nake fata idan karatun ya zamo yana da takarda to inda ya dace mutum ya fadi watarana in ba shi da takarda za a hana shi fadi.

"Don haka ina yin karatu ne don fatan inda duk ya kama aka ce in mutum zai iya fadi a kuma ji a kuma amfana ko da mutum daya ne, don haka takaice shi ne burina a karatu shi ne idan na karanto in karantar,'' ta ce.

"Bayan nan kuma sai muka ci gaba da jiran cewa tun da mutum ya zama matar aure da ƴaƴa da sauransu ina kuma za mu je mu samu yadda za a sake samun wurin kara karatu?

"Allah ya kawo makarantar Jami'ar Alkalam inda muka zamo dalibanta na farko wanda su sun dauki mazan da matan a lokaci guda a daidai shekarar 2005, muka gama a shekarar 2009.

Bayan yin karatu a matakai daban-daban dai Malama har a yanzu tana ci gaba da yi.

Malama ta ce tambayoyin da aka fi yi mata suna yawaita ne a bangaren ibada, da kuma abin da ya shafi mu'amala.