Ku San Malamanku Tare da Sheikh Aminu Abdullahi Yammawa Katsina
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Shirin Ku San Malamanku na wannan mako ya tattauna ne da Sheikh Aminu Abdullahi Yammawa, wani malamin addinin Musulunci a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.
An haifi Malam Aminu a unguwar Yammawa cikin jihar Katsina. Ya tashi gaban iyayensa kuma a gaban iyayensa ya fara karatu.
Ya fara karatu wajen babansa na addini tun daga sanin haruffa. Daga nan ya shiga makarantar boko ta Gobarau Primary School.
Malam ya ce ya fi gane karatun addini, shi ya sa babansa ya ƙi yarda ya ci gaba da karatun boko sai na addini.
"Don kar ya kasance a gaba ba a samu wanda zai gaji malunta ba a gidanmu.
Amma daga baya wani malaminsa na addini ya ƙarfafa masa gwiwar haɗa karatun addinin da na zamanin don samun garaɓasa biyu.
Sai ya tafi makarantar Higher Islamic Studies inda har ya samu takardar shaidar kammala karatu.
"Sannan duk sauran karatuttukana da nake yi ba su yi rauni ba kowane ya tafi yadda ya kamata, har na zo ina koyawa magidanta karatu.
"A hakan kuma har na kan tafi wajen neman abincina."
Daga baya ya samu shaidar NCE a fannin Arabic da Islamic Studies Education a FCE Katsina.
Sai ya tafi Katsina Poloytechnic ya yi difloma a Public Personal Managemet, sannan ya wuce ya yi babbar difloma Public Policy and Admin.
Ya kuma yi digiri na biyu a Jami'ar Karatu Daga Gida, sannan ya je Jami'ar Umaru Musa 'Yar adua ya sake digiri na biyu.
Na so na sake digiri na biyu kan sanin halayyar ɗan adam amma wani malamina ya ce bokon ya isa haka gara na yi a fannin Islamic Studies.
"Daga nan sai na wuce Jami'ar An-Nahda na yi digirin-digirgir," in ji Malam.

Malamansa
- Malam Usman Ɗanƙyado inda na yi karatun littattafai sosai a wajensa
- Malam Babangida Abbas
- Malam Usmatu Abbas
- Malam Halifa na Kofar Kaura
Malam ya ce yana yawan motsa jiki da duba lafiyarsa akai-akai. A fannin abinci kuma ya fi son naman kaji da zabbi da tuwon shinkafa da tuwon masara da miyar kuka.
Me ya sa yake da zafi ga gwamnati?
Ana yi wa malam kallon mai yawan sukar gwamnati da yin zafi a kanta, sai dai ya ce ba don cin mutunci yake ba sai don gyara.
"Ko su su kan bugo min waya wani lokaci, amma sai na tambaye su abin da na fada din an yi ko ba a yi ba? Sai na yi musu bayanin dalilin da ya sa na yi.













