Thandiwe Muriu: Hotunan kayan ƙawa da ke yaudarar idanu

Woman disguised by swirling fabric

Asalin hoton, Thandiwe Muriu

    • Marubuci, Daga Damian Zane
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
1px transparent line

Mai ɗaukar hoto Thandiwe Muriu na so masu yi mata tallar kayan ƙawa su saje amma kuma su fita daban a lokaci guda.

Jerin hotunanta suna yaudarar idanu inda matar da ke cikin hoton take kusan ɓacewa amma kuma ba ka iya ɗauke ido daga kanta.

Hotunan matashiyar mai ɗaukar hoton na kama da hotunan da ake saka wa a manyan mujallun tallar kayan ƙawa, amma suna da wasu ma'anoni daban.

"Ina son ɗaukar hoton kayan ƙawa. Ina iya yin sa kullum, amma sai na fahimci ya kamata ɗaukar hotunan kayan ƙawa ta fito da ainihin ni wace ce," ta shaida wa BBC. "Saboda haka ne na fara ɗaukar jerin hotunan na ɓad-da kama."

Woman disguised by colourful fabric

Asalin hoton, Thandiwe Muriu

1px transparent line

Atamfofin masu haske da gyaran gashin da masu tallar suka yi da tabarau da suka sa sun ja hankali kan yadda matashiyar ke tallata al'adarta.

Amma akwai ƙarin haske.

Muriu ta ce jerin hotunan na "nuna yadda na kan ji kamar na ɓace a bayan fagen al'adata.

"Kuma rayuwata a matsayina na mai ɗaukar hoto na fahimci cewa ina iya ɓacewa ko a yi watsi da ni saboda al'ada."

Woman disguised by sunflower fabric

Asalin hoton, Thandiwe Muriu

1px transparent line

Ita ta koya wa kanta ɗaukar hoto sannan ta koya, a kalamanta, "a jami'ar YouTube", amma mahaifinta ya ba ta ƙwarin gwiwa daga farko-farko.

Ƴaƴansa mata huɗu kuma bai da ɗa namiji ko ɗaya don haka ya jajirce wajen nuna cewa mata na iya yin duk abin da namiji zai yi, in ji Muriu.

Ya koya masu abubuwa na yau da kullum kamar sauya tayar mota da gasa nama da kuma amfani da kyamara.

Kuma ko da lokaci ya zo na zaɓar aikin da za ta yi, ya zaburar da ita ta yi abin da ranta yake so wato ɗaukar hoto.

Woman surrounded by fabric

Asalin hoton, Thandiwe Muriu

1px transparent line

Hotunan da take gani a mujallar Vogue na yayarta sun ɗauki hankalinta, Muriu ta fara ɗaukar hotuna don samun kuɗi wanda a Kenya maza ne suka fi yin wannan sana'ar.

"Ba ni da girman jiki, ina kama da ƙaramar yarinya don haka sau da yawa babban abin da nake fuskanta shi ne mutane suna watsi da ni. Sai in shiga wurin da zan ɗauki hotuna sai mutane su yi wa mai taimaka min namiji magana, kawai suna ganin ai shi ne mai ɗaukar hoton ba ni ba.

"Sai da na koyi jajircewa da zama marar tsoro kuma in ce: 'Ya dai, ni ce mai ɗaukar hoton.'"

Woman with long hair and colourful flower print

Asalin hoton, Thandiwe Muriu

1px transparent line

A lokacin da ta ke ƙara koyon aikinta, wata ƙungiyar masu ɗaukar hoto da suka fara kafa kansu a ƙasar ta taimaka wa Muriu. Ɗaya daga cikin ƴan ƙungiyar, Osborne Macharita ya ƙarfafa wa Muriu wajen lalubo hanyoyin bunƙasa sana'arta.

Wannan ne ya haifar da Hotunan Ɓad-da Kama a shekarar 2015.

Woman with Coke cans as eyewear

Asalin hoton, Thandiwe Muriu

1px transparent line

"Da farko na fi mayar da hankali kan fikirata," a cewarta.

"Ina ga hotuna na farko-farko sun ƙunshi atamfofin nan masu kyau da al'ada mai ƙarfi da nake ciki kuma nake gani kullum."

Ta zaɓi masu tallar kayan ƙawa masu duhun fata musamman don ƙalubalantar abin da ta kira al'adar bilicin a Kenya inda ake ganin fata mai haske a matsayin wadda ta fi kyau.

Mai tallar kayan ƙawa ta farko da ta fara aiki da ita na da wushirya, wanda a al'adarta ta Kikuyu ta ce "alama ce ta kyau". Kuma gashin kanta wanda ba a sa wa man salun ba ne.

Woman licking her lips

Asalin hoton, Thandiwe Muriu

1px transparent line

Muriu ta yi burin yara mata ƙanana a Kenya su ga hotunan su ce: "Ni ce wannan."

Daga kallon hotunan za ka san cewa haɗa su ba ƙaramin aiki ba ne.

Ana farawa ne da zaɓar atamfar, wadda Muriu ta bayyana a matsayin mataki mai wahala amma mai daɗi.

Woman disguised by colourful fabric

Asalin hoton, Thandiwe Muriu

1px transparent line

Tana kwashe tsawon awowi a shagunan atamfofi a Nairobi, tana zaɓar atamfofin da aka shigar da su ƙasar daga faɗin nahiyar.

Tana neman "wani abu mai hasken gaske mai ɗaukar hankali, yadda zanen jikinsu zai nuna kamar atamfar mai rai ce kuma tana motsi sannan ta rikitar da ido". Da an gan ta an san daga Afrika ta fito amma ba lallai irin zanen da aka saba gani ba.

"Muna cikin sabuwar Afrika, sabon ƙarni inda muke da son atamfa amma ba masa ta yadda aka saba gani a gargajiyance."

Woman disguised by colourful fabric

Asalin hoton, Thanidwe Muriu

1px transparent line

Wani mataki mai muhimmanci shi ne gyaran gashi. Yayin da ake ɗaukar hotunan, Muriu ta dage wajen yin gyaran gashi da fahimtar yadda ake kallon kyau a Afrika.

Tana bincike kan gyaran gashi na gargajiya a tarihi. Sannan da taimakon mai gyaran gashin sai a mayar da su "na zamani masu ɗaukar hankali amma ba tare da an watsar da yadda iyaye da kakanninmu su gyara gashinsu ba", a cewarta.

"Sai abin ya zama ya fi ƙarfin kallon abu mai kyau kawai. Sai ya zama ana tambaya ne: "Shin waɗanne ne alamomin kyau da muka rasa?'"

Tabarau ɗin, wanda aka haɗa da gwangwanin lemo da rariyar roba da abin matse shanya da burushi da sauran abubuwa na nuna sabbin hanyoyin da ake amfani da kayan aiki na yau da kullum, in ji Muriu.

Woman disguised by colourful fabric

Asalin hoton, Thandiwe Muriu

1px transparent line

Haka kuma sun ƙara wa hotunan nau'i na barkwanci wanda mai ɗaukar hoton ke so ta ja hankalin mutane da shi, a lokaci guda kuma ta ci gaba jan hankali kan matsalolin da ke faruwa.

Kuma ba ta gama ɗaukar jerin hotunan ba

"Zan ci gaba da yi. Babban ƙalubalen shi ne ƙoƙarin adana duka hotunan kuma in zama wadda ta fara adana gyaran gashinmu da atamfofinmu. Me zai hana?"

Duka hotunan na Thandiwe Muriu ne.