Rikicin Tigray: ‘Na rasa hannuna lokacin da soja ya yi ƙoƙarin yi min fyaɗe’

An wallafa

Gargadi: Ran wasu daga cikin masu karatu zai iya baci idan suka karanta wani bangare na wannan labari.

Wata daliɓa a Habasha ta shaida wa BBC yadda ta rasa hannunta na dama a yayin kare kanta daga wani soja da ya yi ƙoƙarin yi mata fyaɗe - wanda kuma ya yi ƙoƙarin tilasta wa kakanta ya yi lalata da ita.

Matashiyar mai shekara 18, wadda ba mu bayyana sunanta ba, ta shafe sama da wata biyu kwance a asibiti a yankin arewacin Tigray inda take murmurewa daga halin da ta shiga.

Rikicin na Tigray, wanda ya ɓarke a farkon watan Nuwamban shekarar 2020 lokacin da Firaiminista Abiy Ahmed ya ƙaddamar da farmaki don fatattakar jam'iyyar TPLF da ke mulki a yankin bayan da mayaƙanta suka ƙwace ikon wasu sansanonin sojan tarayya, ya tarwatsa rayuwar ɗalibar, da kuma yawancin ƙawayenta da suke karatu tare.

Yawancinsu, da su da ƴan uwansu, sun tsere inda suka fake a tsaunuka - duk da Mr Abiy, wanda ya lashe kyautar Nobel ta Zaman Lafiya, ya ayyana samun galaba bayan ƙwace babban birnin Tigray, Mekelle, da sojojin gwamnati suka yi a ranar 29 ga Nuwamba.

Hakan ya faru ne bayan da jami'an tsaro suka ƙaddamar da yaƙin farautar mambobin TPLF da suka ƙi miƙa wuya, lamarin da ya haifar da zarge-zargen mummunan take haƙƙin bil'adama da aka yi wa mazauna yankin na Tigray. Hukumomin sun musanta zarge-zargen.

Ɗalibar da kakanta sun kasance a cikin gidansu a garin Abiy Addi, kusan kilomita 96 da yammacin Mekelle, saboda zai yi wahala su yi tafiya mai nisa.

A ranar 3 ga Disamba, matashiyar ta ce wani soja, sanye da kakakin sojan Habasha, ya shiga gidansu yana neman ya san inda mayaƙan Tigray suke.

Bayan ya bincike gidan bai ga kowa ba, ya umurce su da su kwanta a kan gado sannan ya fara harbi sama.

"Daga nan ya umarci kakana ya yi lalata da ni. Kakana ya fusata sosai ... suka fara faɗa," in ji ta.

Sojan, a cewarta, ya ɗauki tsohon ya fita da shi waje ya harbe shi a kafaɗa da cinya sannan ya dawo wurinta, yana cewa ya kashe shi.

Ya ce: "Ba wanda zai iya ceton ki yanzu. Ku cire tufafinki. Na roke shi kada ya yi hakan amma ya dinga min naushi."

Sun shafe lokaci suna taƙaddama - duk da cewa ta galabaita daga bugun da yake mata - kuma a karshe ya fusata har ya nuna mata bindiga.

"Ya harbi hannuna na dama har sau uku. Ya harbi kafata sau uku. Ya fice lokacin da ya ji ƙarar harbe-harbe daga waje."

Ya kasance abin godiya kakanta yana raye, duk da cewa ba a sume yake ba, sun shafe kwanaki biyu cikin ruɗani da tashin hankali a cikin gidansu suna matuƙar jin tsoron neman taimako.

'Babu adalci ko kaɗan'

Labarin matashiyar ya haifar da damuwa game da zargin fyaɗe a Tigray kamar yadda Pramila Patten, Jami'ar Majalisar Ɗinkin Duniya kan cin zarafin mata a rikici ta bayyana.

"Wasu matan kuma rahotanni sun ce sojojin sun tilasta musu yin luwadi don ba su abinci, yayin da cibiyoyin kiwon lafiya suka bayyana ƙaruwar buƙatar kwayoyin hana ɗaukar ciki na gaggawa da gwajin cututtukan da ake yaɗawa ta hanyar jima'I, wanda galibi hakan manuniya ce ta matsalar cin zarafin mata."

Jam'iyyun adawa guda uku a Tigray sun ce an yi kashe-kashe kuma fyaɗe ya zama "ruwan dare", suna kuma ba da misali da wani uba da aka tilasta wa ta hanyar amfani da bindiga don ya yi wa 'yarsa fyade.

Wani likita da memba na wata ƙungiyar kare haƙƙin mata - waɗanda dukkansu suka nemi a ɓoye sunansu - sun shaida wa BBC a watan Janairu cewa a tsakaninsu sun yi rajistar aƙalla ƴan mata 200' ƴan kasa da shekaru 18 a asibitoci daban-daban da cibiyoyin kiwon lafiya a Mekelle wadanda suka ce an yi masu fyade.

Yawancinsu sun ce waɗanda suka aikata laifin suna sanye ne da kakin sojin Habasha - kuma daga baya sun masu gargaɗi kan neman taimakon likita.

Likitan ya ce "sun samu rauni a jikinsu. Wasu ma gungun maza suka yi masu fyade. Wata ma an yi mata fyaɗe tsawon mako guda. Ba ta san ma inda take ba. Kuma babu ƴan sanda, saboda haka babu adalci ko kaɗan," in ji likitan.

Mai rajin kare hakkin ɗan Adam ya ce: "Mun kuma ji irin waɗannan labaran na fyaɗe daga wasu yankunan na Tigray. Amma saboda matsalolin sufuri ba za mu iya taimaka musu ba. Abin baƙin ciki ne."

Wani likitan da ke aiki a wani asibiti a Mekelle ya ce ba da daɗe ba kusan a kullum sai mata biyar ko shida sun zo asibiti neman maganin kariya daga HIV da maganin hana haihuwa dangane da zargin fyade.

Weyni Abraha, ƴar rajin kare haƙƙin mata ta ƙungiyar Yikono ta kasance a Mekelle har zuwa ƙarshen Disamba, ta shaida wa BBC cewa ta yi imanin cewa ana amfani da fyaɗe a matsayin makamin yaƙi.

"An yi wa mata da dama fyaɗe a Mekelle. Ana yin hakan ne da gangan domin karya lagon mutane, da yi musu barazana da kuma sa su haƙura da yakin."

Shugaban sojan Habasha Birhanu Jula Gelalcha ya musanta zarge-zargen.

"Sojojinmu ba su yin fyaɗe. Ba ƴan fashi ba ne. Sojojin gwamnati ne. Kuma gwamnati tana da dokoki da sharuɗa," kamar yadda ya shaida BBC.

Magajin garin Mekelle na riƙon ƙwarya Atakilty Hailesilasse, ya ce ƴan rajin kare haƙ kin dan Adam sun zuzuta alƙaluman.

Kwanan nan gwamnatin ta tura wata tawaga zuwa Tigray don ci gaba da binciken zargin, ciki har da mutane daga ma'aikatun mata da na kiwon lafiya da kuma ofishin babban lauyan gwamnati, waɗanda suka ce an yi wa mata fyade, Ko da yake ba fitar da rahoton bincikensu ba.

A makon da ya gabata ne Hukumar Kare Haƙƙin ɗan Adam ta Habasha ta ce an samu rahoton fyade 108 a cikin watanni biyu da suka gabata a duk faɗin Tigray.

'Na so zama injiniya'

Wani likita ya tuntubi BBC game da batun matashiya Abiy Addi bayan ya yanke hannunta.

Ita da kakanta sun gaya masa yadda aka same su kwana biyu bayan harin da sojojin Eritrea da ke bincike a yankin suka kawo musu - duk da cewa Habasha da Eritrea sun musanta hannun Eritrea a rikicin na Tigray.

A yanzu haka kakan ya murmure daga raunin da ya ji, amma har yanzu jikar tasa na bukatar magani sakamakon datse hannunta. Har yanzu ƙafarta ta dama ba ta warke ba.

Ta yi magana da BBC daga gadonta na asibiti, tana kuka game da burinta na rayuwa da ta rasa.

Tana ajin ƙarshe na kammala makaranta kafin yakin ya fara, burinta shi ne ta tafi jami'a domin karatun injiniya sannan ta shiga aikin da zai ba ta damar kula da kakanta, wanda ya raine ta tun bayan rasuwar mahaifiyarta.

Kakanta, a gefen gadonta, cikin tausayai yayin da take kuka: "Ta yaya zai yiwu? Ba zan iya zama kamar yadda nake faɗa ba."