Binciken BBC ya gano ba a da rajistar wadanda suka mutu a yawancin ƙasashen Afirka

Feet in a mortuary

Asalin hoton, AFP

An wallafa

A lokacin da aka yi fama da cutar Ebola da kuma annobar korona, samun sahihan bayanai kan waɗanda suka mutu, da dalili- na da muhimmanci musamman idan aka zo batun ware kuɗaɗe da tallafi.

Masana sun ce rashin tsarin bayarwa da ɗaukar sahihan bayanai kan waɗanda suka fi fuskantar barazana na haifar da aƙuba - akasari mata da yara, bayanansu ba sa isa ga gwamnati da ke yanke shawara idan aka zo kan batun abubuwan da ake buƙata a fnanin lafiyar haihuwa da kariya daga cututtuka.

Wani binciken BBC da ya yi aiki da cibiyar kididdiga ta Afirka da hukumar lura da tattalin arziki da walwala na Majalisar Ɗinkin Duniya,MDD, a Ethiopia, UNECA, ya tattara tare da nazari kan mace-macen da ake samu a ƙasashen Afirka 55 da yankuna - domin gano yadda ake fidda alƙaluman mutuwa da sahihancinsu da kuma rajista a nahiyar.

A cikin ƙasashen 55 da yankuna na BBC tayi nazari, ƙasashe takwas - Masar da Afirka ta Kudu da Tunisia da Algeria da tsibirin Cape Verde da Sao Tome da Seychelles da Mauritius - ke da tsari nagartacce na rajista, da ke tafiya da zamani da tabbatar da cewa ana ɗaukan bayanan kowacce mutuwa.

William Muhwava, wanda shi ne shugaban sashen kididdiga a hukumar UNECA ta MDD a Addis Ababa, ya ce "rajistar mutane haƙƙi ne bisa tsari na kowanne bil adama domin tantance asali."

Dukkanin ƙasashen da muka yi nazari na da nasu irin tsarin rajistan - akasari kan takarda ba a kamfuta ba. Yana aiki a iya yankuna - baya kai matsayin isar da shi har zuwa matakin tarayya.

Akwai yara da aka haifa basu da rajista kuma wataƙil har su gama rayuwa basa kan rajista, saboda tsaikon da ake samu wajen yin rajistar a lokacin haihuwa da mutuwa.

Ƙasancewa cikin wannan rukuni

Tsarin Rajistar da sanin ƙididdiga ya ƙunshi sanin lokacin haihuwa, aure da mutuwa.

Kafin wannan tsarin ya kai matakin aminta da amfani da shi a duniya dole ya cike sharuɗɗan kididdiga da sanin yawan al'umma na MDD da kashi 90 cikin 100 domin gujewa son-kai da ware wani rukuni na mutane daga ƙiyasi.

Nazarin bayanan MDD a Turai ya nuna cewa ƙasashe biyu wato Albania da Monaco ke da tsarin rajistar da aka aminta da shi a duniya, a Asiya kuma, sama da rabin ƙasashen na bin wannan tsarin.

Ba a da rajistar wadanda suka mutu a yawancin ƙasashen Afirka

Asalin hoton, BBC

Yadda Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta tsara inganta tsarinta

Jamhuriyar Afrika ta tsakiya na cikin ƙasashen da kwata-kwata tsarin ta na rajista bai kai wani mataki ba a nahiyar saboda rigingimu, da har yanzu ake gani.

A 2017, kashi 2 cikin 100 na mace-mace da aka samu kawai aka iya yiwa rajista. Adadin ya rubanya mutuwar maza sau biyu sama da mata - a birnin ƙasar kawai da wasu tsirarun garuruwan waje.

Sai dai Elvis Franck Matkoss, na hukumar kididdiga da samun bayanai a ma'aikatar tattalin arziki da tsare-tsare ya shaidawa binciken cewa, " gwamnati na yin duk mai yiwuwa domin inganta wannan tsarin, sannan akwai kuɗaɗen da ake warewa domin raya wadanan ayyuka da ƙarfafa yiwa yara takardar haihuwa kyauta.

Auna girman tasirin Covid-19

Galibin rahotanni na nuna cewa annobar korona ba ta da yawa a Afirka idan aka kwatatan da wasu ƙasashen duniya.

Afirka ta kudu ce ta fi jin jiki sakamakon annobar korona a kasahen Afirka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Afirka ta kudu ce ta fi jin jiki sakamakon annobar korona a kasahen Afirka

Ƙwararu a fanin daƙile annoba, na cewa yanayin al'ummarta da kashi 60 cikin 100 matasa ne ƴan ƙasa da shekara 25 sun taimaka wajen ƙaranci da takaita yaduwar annobar.

Da dama an aminta da cewa Afirka ta dau matakai masu kyau kan annobar, sai dai masana kimiya na cewa iya lissafa wadanda suka mutu a ƙasashen abu ne mai wahala saboda ba ayi amfani da tsari ba wajen tantance hakan.

Tasirin annobar korona a fakaice na iya zarta abin da ake ganin a zahiri

Idan ana maganar yawan mace-mace ana alakanta alkaluman kai tsaye da korona, sai dai akwai wadanda mutuwar tasu na faruwa ne saboda cukowa ko rashin mayar da hankali kan cuttukan da ke damunsu saboda annobar, fargabar zuwa aibiti da kuma rugujewar tattalin arziki.

Wani binciken Lancet a ƙasashen 118 masu ƙarami da matsakacin karfi ya kiyasta cewa matsalolin da fanin lafiya ya fada saboda korona sun yi sanadin rayukan yara 1,157,000 da mace-mace 56,700 da ke da alaƙa da haihuwa.

Rahoton ya kuma ce, a nazarin mace-mace sakamakon Ebola a 2014 a Afirka ta Yamma, tasirin annobar a fakaice ya zarta wanda ake gani kai tsaye ko sakamakon kamuwa ko ɓarkewar cutar.

Labarin Clowé

Clowé Bafouindintsoni da jaririnta sun mutu sakamakon annoba a Congo-Brazzaville. Kasar ba ta da tsarin adana rajistar mutuwa don haka bata da alkaluman mutanen da suka yi irin mutuwar Clowé.

Haɗarin shi ne idan babu irin wadanan bayanai na mace-mace, faruwarsa, garin yaya da sanadi - akwai matukar wahala wajen fidda matakan kariya ko hana cigaban faruwar hakan nan gaba.

2px presentational grey line

Senegal: Mace-macen ban mamaki

A wani misali kan tattara bayanai a Senegal, inda kashi 3 cikin 100 na mamata ake daukan bayanansu, Ma'aikatar lafiya na aiki da wata ƙungiya mai zaman kanta a Amurka domin daidaita bayanan asibitoci.

Wannan kuwa ya nuna cewa yawan mace-mace - da ake samu kai tsaye saboda annobar ko a fakaice - tsakanin Janairu zuwa Yulin 2020 na rubanya sau shida sama da alkaluman da ake fitarwa kan korona.

Sai dai masana kimiya sun ce haƙiƙanin gaskiyar alkaluman na iya ninka hakan, saboda wannan adadi bai shafi na mace-macen da aka rinƙa samu a unguwanni ba.

Kiyasta yawan mace-mace

Afirka ta Kudu da Masar na cikin ƙasashe 8 masu tsari kan rajistan mutuwa, don haka ƙidaya yawan mace-mace a wadanan ƙasashen biyu mai yiwuwa ne, kuma sakamakon masu sahihanci ne.

A Afirka ta Kudu an samu yawan mace-mace dubu 60 a farkon watan Disamba - wanda hakan ya ninka sau uku na alkaluman da aka fitar a hukumance.

Idan aka kacalcala, mutum dubu 23,600 sun mutu a hukumance sakamakon Covid kuma akwai rajistan da ke tabbatar da hakan.

Wannan na nufin akwai mace-mace dubu 37,000 da watakil ba a gano ba ko suka mutu kai tsaye sakamakon tasirin da annoba ya haifar kamar rashin samun maganin sankara ko fargabar zuwa asibiti.

Ana tsaka da batun annoba a karshen watan Yuli, an samu ƙarin mutuwa da kashi 54 cikin 100 wanda ba ayi tsanmanin ba a wannan lokacin, ko da yake lokacin da aka sanya dokar kulle a karon farko alkaluman sun sauya, watakil ko saboda an samu rage-ragen rigingimin da shan barasa ke haifarwa da hadduran ababben hawa.

Mace macen da ake sa rai a Afrika ta Kudu

Wani binciken BBC ya gano cewa akasarin ƙasashen Afirka basu da wadatacce ko tsari mai karfi kan rajista.

Aƙalla ƙasashen 14 na daukan bayanan mutuwa 1 cikin 10 ko ƙasa da hakan.

Aƙalla ƙasashen 14 na daukan bayanan mutuwa 1 cikin 10 ko ƙasa da hakan.

Sama da rabin ƙasashen yankin kudu da hamadar sahara na adana bayanasu ne a littafi maimakon a zamanance ko ta na'ura.

Wasu ƴan kasashen, irinsu Eritrea da Burundi basu da tsarin shari'a na rajista ko tattara alkaluman mutuwa. Eritrea na da tsarin adanan bayanai guda daya kacal wanda ke da akalla da korona, sannan Burundi, na da guda biyu, ko da yake akwai wasu rahotannin da ake yaɗawa cewa mace-mace da ake gani a ƙasar da mutuwar tsohon shugaba Pierre Nkurinziza a bara korona ce.

A Najeriya an samu bayanan mutuwa da kashi 10 cikin 100 a 2017. Annobar ta sake kassara duk wani tsarin harkokin rajista a faɗin ƙasar. Wannan na iya kasancewa dalilin da ya sa adadin mutanen da ke mutuwa sakamakon korona a cikin miliyan ba su taka kara sun karya ba - mutum 7 cikin miliyan 1, idan aka kwatanta da 579 a Afirka ta Kudu da 81 a Masar. A duniya baki daya kuma ana samun mutum 252 cikin miliyan guda.

A Afirka ta kudu da Masar annobar korona ta fi illa a nahiyar Afirka.

Me ake yi a kai?

Ƙasashe da dama na samun ci gaba wajen cike wannan gibi na tattara bayanai.

Yayinda ƙasashe irinsu Senegal da Rwanda ke kokarin bijiro da tsaron inganta rajista, wanda ake iya bada misali da shi kamar yada ake gani a wannan lokaci na annoba. Su ma wasu ƙasashe biyar - Togo da Burkina Faso da Saliyo da Liberia da Ghana - na aiki da hukumar cutuka masu haɗari na Afirka domin inganta nasu tsarin.

Chadi da Liberia na umartar ma'aikatan lafiya a yankuna daban-daban suke daukan bayanai da sanar da mutuwa a gidaje ko asibitoci domin taimaka wajen inganta alkaluman.

Wasu ƙasashen kuma sun bijiro da hanyar amfani da fasahar zamani a wayoyin hannu. A Rwanda da Mozambique mutane na iya amfani da wayoyinsu wajen yin rajista ta intanet, da bada bayanan ƴan uwa ko rahoton mutuwa.

A Uganda, ma akwai irin wannan tsari inda za ake amfani da wayoyin hannu wajen shigar da bayanai da sanar da mutuwa ko haihuwa.

Nan da wasu shekaru kamar 10, masana kimiya na ganin irin wannan kimiya zai taimakawa ƙasashe da kuma cimma muradai na tattare alkaluman a matakin duniya baki daya.

Binciken BBC ya samu goyon baya da tantacewa daga UNECA.

2px presentational grey line