Marieme da Ndeye: Yadda yaran da aka haifa a manne da juna ke rayuwa a makaranta

/
    • Marubuci, Daga Lucy Owen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Jariran da aka yanke kauna za su rayu, kwanaki kadan bayan haihuwarsu a manne da juna wadanda yanzu sun kusa kai wa shekara hudu, na zaune a makarantarsu da ke birnin Cardiff.

A shekarar 2017 ne Ibrahim, mahaifin Marieme da Ndeye Ndiaye ya kai su Birtaniya daga kasar Senegal don a yi musu aikin tiyata a Asibitin Great Ormond Street da ke birnin London.

Yanzu shekarun wadannan 'yaya mata hudu, suna koyon tsayuwa, kuma mahifinsu ya ce ci gaban na su gagarumi ne.

Shugaban makarantarsu ya ce yaran sun samu kawaye kuma suna ''annashuwa sosai''. Yaran wadanda ke amfani da zuciya da gadon baya daban-daban, na amfani ne da hanta da jakar mafitsara da hanji daya, na fama da matsalar da saka su cikin barazanar kamuwa da cutar korona

Amma kuma, Miista Ndiaye ya ce yana son su fara makaranta don ci gaban su.

"Daga yanzu, komai da ke tafe zai kasance riba ce a gare ni. Zuciyata da ruhina da babbar murya na cewa 'Kai! Ku kara kaimi 'yayana,! Ku kara bani mamaki!'.''Idan na tuna baya, lamarin ya kasance wani buri ne da bai cika ba,'' in ji shi.

Mista Ndiaye ya kawo 'yayan nasa mata zuwa Birtaniya ta hanyar wani tallafi daga wata kungiya mai tallafa wa marasa karfi da uwargidan shugaban kasar Senegal Marieme Faye Sall ta kafa, kafin ya nemi takardar izinin samun mafaka.

A cikin watan Maris na shekarar 2018, ofishin lura da harkokin shige da ficen Birtaniya ta mayar da iyalan zuwa Cardiff, saboda za a iya kai masu neman mafaka ko ina a cikin Birtaniya, kuma yanzu suna da izinin zama 'yan kasa.

A shekarar 2019, likitocin fida na Asibitin Great Ormond Street sun yi tunanin raba su amma abu ne da Mr Ndiaye bai amince ba saboda hadarin da ke tattare da yin hakan.

.

Tun bayan wannan lokaci ne, likitoci suka gano cewa hanyoyin zagayawar jini na yaran suna hade fiye da yadda ake tunani a baya, kuma babu wanda zai rayu ba tare da daya ba, da hakan ya sa ba zai taba yiwuwa a yi tiyata a raba su ba.

Shugabar makarantar yaran Helen Borley ta ce, suna koyon karatu sosai tun da aka fara karatu a cikin watan Satumba, kuma sun yi sabbin kawaye.

'Banbancin halayya'

Ta ce: "Yaran kan ce, ni kawar Marieme ce' ko kuma 'ni kawar Ndeye ce ' - ba sa cewa, ' ni ƙawar tagwaye ce'. A kan samu kawaye na kowanne a cikinsu - saboda waɗannan yara na da bambanci a wajen halayya.

''Suna dariya sosai - wanda alama ce mai kyau, ko ba haka ba? Duk yaron da ke dariya sosai lafiyayyen yaro ne."

.

Saboda wadannan tagwaye, makarantar na bukatar kasancewa cikin ziyartar asibiti a koda yaushe.

A cikin watan Oktoba, yaran sun bukaci a yi musu tiyata a Asibitin Great Ormond Stree.

Dakta Gillian Body, wata likitar yara a Asibitin Yara na Wales a Cardiff, ta ce aikin na da matukar muhimmanci, duk kuwa da hadarin da ke tattare da shi.

Ta ce: ''Yaran na da yanayin halaittu masu cike da sarkakiya, da hakan ya saka su cikin barazanar saurin kamuwa da cututtuka.

"Daya daga cikin kalubalen da muka samu shi ne ba su magungunan kashe kwayoyin cuta cikin sauri, kuma wannan bututun da aka dasa musu na nufin za mu iya saka wa ta ciki da sauri kuma ba tare da haifar da damuwa ga yaran ba.''

Twins learning to stand
Bayanan hoto, .

Ta ce zuciyar Marieme na da sarakiya da kuma wasu abubuwa da basu cikasa ba, da hakan ya haifar mata da matsaloli wajen motsa jiki da matsalar numfashi.

'Samun daidaito'

A makarantar kula da lafiyar yaran, Ty Hafan a Sully, da ke 'Vale of Glamorgan', tagwayen na koyon yadda ake tsayuwa.

Wasu karafuna na taimaka musu wajen samu su tsaya sosai, tare da taimaka musu wajen kara kwarin kafafu.

Likitar lura da motsa sassan jiki Sara Wade-West ta ce abin ba mai sauki bane a gare su.

"Abu ne na daban, lokacin da ka riga ka saba da zama a koda yaushe, sannan a ce za a tsayar da kai akwai damuwa,'' ta ce.

"Da farko, musamman Ndeye bata amince da haka ba. Mun yi kokarin mu lallaba mu yi musu wannan aiki a cikin wasa, don karfafa musu su iya dauko kayan wasa, su dan yi aiki kadan, amma idan suka gane abinda muke aniyar yi ba abin wasa bane.''

Ibrahima Ndiaye

Kallon 'ya'yansa a tsaye wani babban ci gaba ne ga mahaifin.

"Suna nuna cewa ba kawai suna son su rayu bane, amma su kasance cikin walwala su kuma yi wasa a cikin al'umma,'' ya ce.

"Duka wadannan ci gaba sun kara ƙarfin gwiwa ga makomarsu. Amma na san yadda rayuwarsu ke cike da wahalhalu da sarkakiya.''

Mr Ndiaye ya ce fatan sa sun yi ''hannun riga da fargaba'' saboda tagwayen na shi '' sun sha cin karo da wahalhalu mafiya muni''.

"Amma takaitaccen abin da ba zan iya yi ga wadannan yara shi ne bayyana duka fatan da nake da su a kan su,'' ya ce.

"Abin da zan iya yi sosai shi ne na kasance a tare da su, na kuma rayu cikin wannan fata, sannan kada in bari wani abu ya dauke min wannan fatan.''

"Jarumai na ne. Sun nuna cewa ba za su taba jajircewa ba tare da fafatawa ba." in ji shi.