Wasika daga ƴan jaridar Afirka: Shiryawar Sudan da Isra'ila ta sa cikin ƴan ci rani ya ɗuri ruwa

Asalin hoton, Getty Images
A jerin wasiƙunmu daga ƴn jaridar Afirka, Zeinab Mohammed Salih duba dambarwar da ke cikin yarjejeniyar shiraywar Sudan da Isra'ila da dalilin da ya sa hakan ya jawo ɓacin rai daga wasu da kuma jin hakan daga wasu.

Babban birnin Sudan, Khartoum, birni ne mai kabilu daban-daban da suka mamaye sassansa, daga gefen birnin akwai mutanen da suka tserewa yaki a yankin Darfur, da tsaunukan Nuba da kuma sauran wasu al'umomi marasa rinjaye.
Su kuwa yankunan bayan gari suna da mashahuran masu magana da harshen Larabci.
Haka nan kuma birnin na da tarihi sosai a kasashen Larabawa, tun bayan da ya karbi bakuncin taron kasashen Larabawa na shekarar 1967, ranar da aka amince da wata sabuwar matsaya ta cewa babu sulhu, babu zaman lafiya, sannan kuma babu maganar amincewa da Isra'ila a matsayin kasa mai zaman kanta.
Sai dai ba dukkanin al'ummar Sudan ne ke da wannan ra'ayi ba, kamar yadda wadanda ke gefen Khartoum za su iya bayar da shaida.
Ruwan sama na lalata daruruwan gidajensu wanda aka gina da laka da itace, a duk sa'ad da damina ta fadi.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarun da suka gabata, ana sake gina wasu ta hanyar amfani da karafa da siminti sakamakon kudin dangin wadanda ke rayuwa a wajen ke tura musu, tun da suna can suna neman kudi a Isra'ila, inda suke rayuwa a matsayin 'yan ci rani.
Yawancinsu sun isa Isra'ila ne bayan sun yi balaguro da kafa, inda suke ketawa ta Hamadar Sinai, bangaren da masu tsaron iyakar Masar ke sintiri.
Wasu da dama ma sun mutu a hanya.

Amma mafaka ta wucin gadi da aka bai wa wadanda suka isa Isra'ila na iya yin barazana ga yarjejeniyar da gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ke jagoranta don daidaita alakar da ke tsakanin Isra'ila da Sudan, abin da galibin kasashen Larabawa suka ce zai faru ne kawai bayan an sasanta rikicin Falasdinu.
Bayan sanarwar, Ministan Leken Asiri na Isra'ila Eli Cohen ya ba da shawara ga masu neman mafaka 'yan Sudan da su koma gida.
Amma duk da haka mafi yawansu sun fito ne daga wuraren da har yanzu ke fuskantar rikici a Sudan.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, akwai bakin haure 'yan Sudan sama da 6,000 a Isra'ila kuma mafi yawansu ba a amince da su a matsayin 'yan gudun hijira a hukumance ba.

Wasu labaran da za ku so:

A zahiri a cikin 'yan shekarun da suka gabata, an kori wasu dubban mutane bayan tilasta musu su zabi tsakanin zama a sansanin ko zuwa wata kasa ta uku kamar Rwanda ko Uganda.
Wani mutum, wanda a karshe ya gwammace ya koma Sudan a 2014, ya yi nadamar wannan hukunci da ya yanke wa kansa, saboda an sanya wadanda suka dawo din a karkashin kula kuma an kwace fasfunansu na tsawon shekaru biyar.

Asalin hoton, Getty Images
'Yaren Hibru kadai 'ya'yana mata suka iya'
Azra el-Nour, wacce ke zaune a garin Arad na Isra'ila, ba ta yarda a tura ta Sudan ba.
Ta gujewa yaki ne a cikin tsaunukan Nuba tare da danginta lokacin da take da shekara bakwai.
Sun tafi Masar, inda suka kwashe shekaru bakwai suna gudun hijira ba tare da tayin sake tsugunar da su zuwa wata kasa ta uku ba.

Ta ce da ni "Don haka mahaifina ya yanke shawarar cewa ya kamata mu je Isra'ila, hakan ba abu ne mai sauki ba, domin mun sha wahala sosai kafin zuwa nan."
A yanzu haka shekarunta 27 kuma uwa ce da ke da 'ya'ya biyu wadanda ke magana da Hibranci kawai, babu dayansu da aka amince da shi a matsayin dan gudun hijira.
Ta damu da cewa idan aka tilasta musu komawa Sudan saboda kowane dalili za su iya fuskantar wariya a yayin zamansu, kamar yadda aka jima ana nunawa a fadin kasar.
"Ya'yana mata biyu ba su san komai game da Sudan ba, ko da ni ban san komai game da kasata ba, ban san yadda zan zauna a can ba idan an kore mu daga nan."
Ba a maraba da su a Isra'ila
Bashir Babikir mai shekaru talatin da daya ya ce yana tsoron komawa Darfur, inda har yanzu danginsa ke zaune a wani sansani bayan an kai wa kauyensu da ke kusa da Khartoum hari.
"Babu wani abu da ya rage a wurin, ko da tsuntsu a kauyena, duk mun gudu, da yawa sun tsaya a sansanin Kassab, wadanda suka yi sa'a suke da dangi a Khartoum sun tafi tare da su."
Daga nan ya tashi zuwa Isra'ila ta Masar yana biyan masu fatauci makiyaya, kuma yana jin tsoron dawowa saboda wasu halaye na 'yan Sudan ga Isra'ila.
Ana iya ganin wannan ta hanyar zanga-zangar baya-bayan nan bayan Sallar Juma'a a Khartoum, tare da dumbin jama'a da suka fusata da yiwuwar yin sulhu da Isra'ila.
Rikici ne har ma tsakanin jami'an gwamnati da mutan gari da janar-janar din Sudan.
Lamarin ya kara kamari biyo bayan kifar da gwamnatin hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir a bara.
Yotam Gidron, wani mai bincike kan alakar Isra'ila da Afirka, ya ce Isra'ila ta dade tana goyon bayan wadanda ke adawa da gwamnati a Khartoum, ciki har da 'yan tawaye a kudanci.
Kuma a dai dai lokacin da rikici ya barke a Darfur, wasu kungiyoyin 'yan tawaye sun bude ofisoshin wakilai a Kudus.
Amma lamarin yana da sarkakiya ga 'yan Sudan din a Isra'ila, wadanda ba a maraba da su.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sabbin dokoki sun bukaci 'yan ci ranin su rike kashi 20% na albashin da ake biyansu har sai sun bar Isra'ila.
"Idan aka mayar da mu zuwa Darfur, za mu iya mutuwa, har yanzu Isra'ila ta kasance abokiyar gaba ga mutane da yawa, amma kuma a nan muna rayuwa cikin mummunan yanayi," in ji Mista Babikir.

Bayani kan wasu kalmomi da muka yi amfani da su:
BBC ta yi amfani da kalmar (bakin haure) wajen bayyana mutanen da hukumomi ba su amince da su a matsayin 'yan gudun hijira ba, da wadanda ke neman takardu a yanzu haka, wadannan mutane sun hada da wadanda suka gujewa yaki a wasu kasashe, wadanda watakila za a iya ba su mafaka a matsayin 'yan gudun hijira, da kuma wadanda ke neman aiki da rayuwa mai kyau, wadanda su kuma gwamnati za ta iya ayyana su a matsayin 'yan ci rani.












