Donald Trump ya sanar da shiryawar Sudan da Isra'ila

Man waves a Sudanese flag in Khartoum (file photo)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sudan ta zamo ƙasar Larabawa ta biyar da ta shirya da Isra'ila
An wallafa

Kasashen Sudan da Isra'ila sun amince su gyara alaƙar da ke tsakaninsu, kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya ce - lamarin da ya zamo na baya-baya cikin jerin ƙasashen Larabawa da suka yi hakan.

Hakan na zuwa ne bayan da Mista Trump ya cire Sudan daga jerin ƙasashen da ke goyon bayan ta'addanci, tare da janye hana ta tallafin tattalin arziki da zuba jari.

Da yake sanar da yarjejeniyar, Mista Trump ya ce ''a ƙalla ƙasashen Larabawa biyar'' suna son cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila.

Hakan na zuwa ne makonni kaɗan bayan da ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE da Bahrain suka cimma irin wannan yarjejeniya da Isra'ila.

Ƙasashen biyu na yankin Gulf sun zamo na farko a Gabas Ta Tsakiya da suka shirya da Isra'ila cikin shekara 26 da suka gabata.

A shekarar 1994 ne Jordan ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila sannan Masar ta yi hakan a shekarar 1979.

Ita ma Mauritania, wata ƙasa da ke cikin ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta shirya da Isra'ila a 2009 amma sai bayan shekara 10 sannan ta ƙulla alaƙa da ita.

Falasɗinawa na ta Allah-wadai da yadda ƙasashen Larabawa ke shirya wa da Isra'ila, abin da suke kallo a matsayin cin amanar fafutukarsu.

A tarihi, ƙasashen Larabawa sun sanya sharuɗɗa kan cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila da cewa sai ta janye daga yankunan da ta mamaye bayan yaƙin shekarar 1967, da kuma kafa ƙasar Falasɗinu da mayar da Birnin Ƙudus babban birninta.

Ta yaya aka sanar da matakin?

Jim kaɗan bayan da Mista Trump ya sanar da matakin cire Sudan daga jerin Amurka na ƙasashen da ke goyon bayan ta'addanci, sai aka shigar da manema labarai a Washington cikin ofishin shugaban ƙasar, inda suka samu yana waya da shugabannin Sudan da na Isra'ila.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yarjejeniyar ''wata babbar abar tarihi ce ta zaman lafiya'' kuma mafarin ''sabon ƙarni.''

Ya ce tawagogin Isra'ila da Sudan za su haɗu don tattauna haɗin kai ta fannin kasuwanci da harkar noma.

Firaministan Sudan Abdalla Hamdok ya gode wa Mr Trump da cire sunan ƙasarsa da ya yi daga jerin ƙasashen da ke goyon bayan ta'addanci, sannan ya ce gwamnatin Sudan na aiki ''kan yadda alaƙar ƙasa da ƙasa za ta yi wa ƴan ƙasar tasa rana.''

Wani mai taimaka wa Mista Trump Judd Deere ya ce shiryawar ''wani babban mataki ne na gina zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya, ta hanyar ƙara samun wata ƙasar da ta shiga jerin Abraham Accords", sunan da ake amfani da shi ga yarjejeniyar da UAE da Bahrain suka cimma.

Haka kuma, wani jami'i daga ƙungiyar ƴantar da Falasɗinawa ta Palestine Liberation Organisation (PLO), Wasel Abu Youssef, ya ce shiryawar Israi'la da Sudan wani ''sabon caka wuƙar ne a gadon bayan Falasɗinawa.''

A hannu guda kuma, Isra'ila ta ce ba za ta yi adawa da sayar wa ƙasar UAE ingantattun kayan yaƙin soja da Amurka za ta yi ba. Sai da Amurka ta yarda da sayar wa UAE jiragen yaƙi samfurin F-35 ne kafin UAE ɗin ta yarda da shirya wa da Isra'ila.

Isra'ila ta ce tana buƙatar samun ƙarfin soji fiye da dukkan ƙasashen da ke Gabas Ta Tsakiya. Amma a farkon makon nan, ta ce Amurka ta amince ta inganta harkar sojin isra'ila.

Ta yaya aka zo nan?

Sudan da Isra'ila a baya maƙiyan juna ne tun bayan kafa Isra'ilar a shekarar 1948.

A wani taron ƙasashen Larabawa da aka yi a Khartoum, babban birnin Sudan a shekarar 1967, Sudan ta sha alwashi cewa: ''babu zaman lafiya da Isra'ila, babu batun shiryawa da Israi'la, babu batun sasantawa da ita.''

Ta yi yaƙi da Isra'ila a shekarun 1948 da 1967, inda ta samar wa ƙananan ƙungiyoyin mayaƙa na Falasɗinawa mafaka, kuma an zarge ta da aika wa mayaƙan sa kai na Falaɗinu makamai a Gaza shekaru da dama da suka wuce - abin da ya jawo aka zargi Israi'la da kai hare-haren sama don nuna adawa da hakan.

Yanayin siyasar ya sauya a bara bayan da aka hamɓarar da gwamnatin Omar al-Bashir da ta daɗe tana mulkin Sudan, aka kuma maye gurbinsa da gwamnatin riƙon ƙwarya ta soji.

Omar al-Bashir (01/04/19)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Omar al-Bashir, wanda ya shahara wajen ƙin Isra'ila an hamarar da gwamnatinsa a 2019

Janar-janar ɗin Sudan sun goyi bayan ƙulla alaƙa da Isra'ila a matsayin wata hanya da za ta taimaka a ɗage takunkuman da Amurka ta sanya wa Sudan, sannan a buɗe ƙofar tallafin tattalin arzikin da ke cikin halin ha'u'la'i.

A wannan makon Trump ya ce za a cire Sudan daga jerin masu goyon bayan ta'addanci da zarar Amurka ta karɓi diyyar dala miliyan 335 na hare-haren da aka kai kan ofisoshin jakadancinta a Afirka.

A shekarar 1998 ne ƙungiyar al-Qaeda ta kai hare-haren a Kenya da Tanzaniya, a lokacin da shugabanta Osama bin Laden ke zaune a Sudan.