Zaɓen Ghana: Ƴan adawa sun yi zargin tafka maguɗi

Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyar adawa ta NDC ta John Dramani Mahama a Ghana ta yi zargin maguɗin zaɓe, yayin da ake dakon fitar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisa. da aka gudanar jiya Litinin.
Duk da cewa an gudanar da zaɓen cikin kwanciyyar hankali a mafi yawan wurare, an samu wasu lamuran tashin hankali da zarge-zargen yin magudi nan da can.
Wani ganau ya shaida wa BBC cewa ya iske yadda ya ga wani ya yi ƙoƙarin yin cushe, sai dai jami'an tsaro sun cafke shi.
Kusan a galibin wurare da aka yi yunƙurin yin cushe ƙuri'u ne da aka dangwala wa jam'iyya mai mulki ta NPP, wanda hakan ya sa ƴan adawa suka farga.
'Maguɗi'
Mai tsawatarwa na marassa rinjaye a majalisar dokokin ƙasar, Honourable Muhammad Mubarak Muntaka , ya bayyana mamakinsa ganin yadda jam'iyyar NPP da hadin kan hukumar zaɓe ke ƙoƙarin yin maguɗi.
A cewarsa, "sun yi mamaki ganin tambarin hukumar zaɓe a bayan katin zaben, ya ce ba za su amince da aringizo da jefa ƙuri'a sama da rajista ba".
Kafin wadannan lamuran da suka faru a mazabar Asewase, jam'iyyar adawar ta kira wani taron 'yan jarida na gaggawa inda ta ce ta gano wani yunkuri na magudin wata mazabar ta daban.
"Akwai wani otel guda uku da aka je ana ta dangwale a katin zaɓen shugaban kasa", in ji Hon Muntaka.
Me hukumar zaɓe ke cewa?
Ofishin hukumar zabe na jihar Ashanti ya tabatar da faruwar wadannan lamuran na yunkurin yin aringizo kuma ya ce ya kaddamar da bincike.
Shi ma jami'in tsare-tsaren jam'iyyar a mazaɓar Menshiya ta Kudu, Abubakar Alhassan, ya shaida cewa sun samu labarin wannan batu amma gaskiya ba da sanin jam'yyarsu ba ne kuma ba shi ne karon farko da ake ganin hakan ba.
Ya ce ko a zaɓukan baya ƴan adawa na iya yin komai domin ƙalubalantarsu ko amfani da wannan siga wajen haifar da tasgaro ga sakamakon zaɓen.
Sai dai yayin da jam'iyyar NDC ke zargin yunƙurin yi mata magudi anan jihar Ashanti ,hukumar zaɓen ƙasar ta fitar da wata sanarwa cewa ta sa an kama wasu malaman zaɓe biyu a garin Boku na jihar arewa.
Ana zarginsu da cire hoton Shugaba Nana Akufo Ado da alamar jam'iyyarsa daga takardar kuri'a kafin su ba masu zaɓe ta yadda sai dai su zaɓi wani ba shi ba ko kuma su fasa zaben.
Wani bidiyo da ke watandari a shafukan zumunta ya nuna yadda kama aka ga ɗaya daga cikinsu tana miƙawa masu zaɓe takardun kuri'un da aka tagayyara.









