Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Amurka: Ruɗanin da Amurka ke fuskanta ya janyo tsoro da fargaba
Cikin sama da makonni, Donald Trump ya ta nanata cewa da an ƙare zaɓen shugabancin ƙasar, zai shigar da abokin takararsa na jam'iyyar Democrat ƙara game da maguɗin zaɓe da kuma yunkurin karɓe nasarar da ya yi.
A safiyar ranar Laraba sai ya yi hakan, lokacin da ya rage miliyoyin kuri'u da ba a ƙirga ba, sai ya yi ikirarin samun nasara a zaben.
"Mun shirya tsaf domin lashe wannan zaɓe, babu ɓoye-ɓoye, mun lashe wannan zaɓe," kamar yadda ya yi ikrari.
Ba tare da gabatar da wata hujja ba, ya ci gaba da yaɗa cewa an yi "magudi" a zaben.
"Wannan shi ne babban maguɗin da aka taɓa yi a tarihin ƙasar mu. Muna so a yi amfani da shari'a ta yadda ya kamata. Dan haka zamu garzaya kotun ƙoli. Muna buƙatar a dakata da ƙirga kuri'un da aka kaɗa."
Abin takaici, 'Abin da ba a yi tsammani ba, abin da ba daidai ba'
Cikin gaggawa wasu 'yan jam'iyyar Democrat sun mayar da martani.
Abokin hamayyar Trump na jam'iyyar Democrat, Joe Biden ya ce zaɓen bai ƙare ba "har sai an kammala kirga ƙuri'un da aka kaɗa".
"Muna kan tafarkin nasara," in ji Biden.
Shugabar yaƙin neman zaɓen Biden, Jen O'Malley Dillion ta ce ikirarin Trump "abin takaici ne, abin da ba a yi tsammani ba ne, kuma ba daidai ba ne".
"Abin takaici ne saboda hakanƙoƙarin take 'yancin mutan Amurka ne a dimokradiyyance," ta ƙara da cewa.
"Abu ne da ba a yi tsammani ba saboda ko a tarihin ƙasarmu ba a taɓa shugaban da ya yi ƙoƙarin danne muryar 'yan Amurka a yayin zaɓen ƙasar."
Wata 'yar jam'iyyar dimokrat Alexandria Ocasio-Cortez, wadda aka sake zaɓa a matsayin 'yar majalisa, ta yi Allah wadai da ikirarin Trump a matsayin "Abin da ya saɓawa shari'a, mai cike da haɗari da ya yi kama da kama-karya".
Ta wallafa a shifinta na Twitter cewa " A ƙirga kuri'u. Sannan a mutunta sakamakon zaɓe,".
Ko 'yan jam'iyyar Republican da Trump ya ke, kamar su tsohon sanata daga jihar Pennsylvania Rick Santorum, ya nuna damuwa kan wannan batu.
Santorum ya ce, kalaman Trump sun matuƙar ɓata masa rai. "Amafani da kalmar maguɗi.... Ina ganin kuskure ne," kamar yadda ya shaida wa CNN.
Haka Ben Shapiro, wani mai sharhi kuma mai yawan sukar Trump ya wallafa a Twitter cewa, wannan "kalaman babu tunani a cikinsu".
Bayan Trump ya gama bayaninsa mataimakinsa Mike Pence ya so ya yi wa zancen kwaskwarima, yana cewa duk halattacciyar kuri'ar da aka kaɗa za a tabbatar da an kirga ta.
'An riga an yi katoɓara'
An riga an gama yin katoɓara, in ji wakilin BBC a arewacin Amurka, Anthony Zurcher.
"Ko Trump ya lashe zaben bisa ka'ida ko kuma ya sha kaye, ya riga ya haifar da shakku kan zaben," in ji Zurcher.
Wannan matsalar annobar korona ya haifar da abin da ba a yi zato ba, saboda 'yan Amurka da dama sun yi zaɓe ta intanet ne, wanda hakan janyo bukatar karin lokaci domin kirga kuri'un.
A wasu jihohin zai ɗauki kwanaki kan kammala ƙirgen.
Anthony Zurcher ya ce "zaben Amurka na cikin wani ruɗani da ya haifar da firgici a zukatan Amurkawa, yayin da shugaban kasar ke ikirarin rashin amincewa da kuri'un da aka kaɗa - daga fadar White House".
Cikin ɗagawa Trump ya ce ba zai karɓi faduwa ba a zaben da ake yi.
A makonnin da suka gabata, wannan ya janyo wata muhawara kan ko za a kira sojoji ne ko kuma 'yan sanda somin fitar da shugaban daga White House idan ya fadi.
Rashin tabbas
Yanzu tseren shugabancin ƙasar na ƙara takaituwa zuwa wasu jihohi da ba su fi a kirga ba, da suka hadar da Arizona da Navada da Pennsylvania da kuma Georgia.
Duk wani ƙalubalen da zai ta so sai an fara garzayawa kotun jiha da farko, in kuma ya yi karfi sai a tsallaka kotun koli. Wanda hakan ke nuna cewa da yi yuwar zai dauki kwanaki kan a sanar da shi.
A gefe daya kuma akwai tsoron cewa za a iya fuskantar tarzoma da sunanan zanga-zanga.
Ko a lokacin da zaben ya matso an ta fuskantar gutsiri tsoma da kuma rikice-rikice a zanga-zangar da aka yi a wasu bangarorin kasar da dama, ciki har da gaban White House.
"Wanne irin rintsi Amurka ke neman faɗawa, lokacin da Biden ke cewa suna kan turbar nasara shi kuma Trump na kukan an yi magudi ana kuma kokarin kwace nasararsa," in ji Zurcher.