Zaben Amurka: Ƴan asalin Najeriya da suka lashe kujerun majalisa a Amurka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar da ke kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta taya wasu ƴan asalin ƙasar da suka yi nasarar lashe kujerun majalisa a zaɓen Amurka.

Oye Owolewa ya kasance ɗan asalin Najeriya na farko da aka zaɓa a majalisar Amurka domin wakilar Washington.

Mista Owolewa ya lashe kujerar majalisar wakilai ƙarkashin jam'iyyar Democrats.

Haka ma Esther Agbaje ƴar Democrats ta samu kujerar majalisa a jihar Minnesota.

Shugaban hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje Abike Dabiri-Erewa, ta wallafa sakon taya murna ga ƴan asalin Najeriyar kan nasarar da suka samu a zaɓen na Amurka.

Ta kuma ce sun kasance wakilai na ƙwarai abin koyi ga matasan Najeriya.

Abubuwa huɗu game da Esther Agbaje

  • An haifi Esther Agbaje a Minnesota.
  • Iyayenta, John da Bunmi ƴan asalin Najeriya ne da suka haɗu a Amurka a makaranta.
  • Ta yi karatun shari'a a makaranta sharia ta Harvard Law school kuma ta ƙware ne a ɓangaren da ya shafi gidaje.
  • Ta yi aiki a gwamnati a ma'aikatar harakokin wajen Amurka.

Abu huɗu game da Oye Owolewa

  • Oye Owolewa ɗan asalin jihar Kwara ne a Najeriya.
  • Ya yi digirinsa na uku a jami'an Northeastern Boston
  • Ba wannan ne karon farko ba da ya shiga siyasa, ya taba zama kwamishina a kudu maso gabashin Washington a 2018.
  • Burinsa a matsayin ɗan majalisa shi ne kawo sauyi a jiharsa.
  • Yana son kawo ƙarshen haramta wa baƙi shiga ƙasar.