Zaɓen Amurka na 2020: Yadda Trump ya hana mutane shiga Amurka tun hawansa mulki

    • Marubuci, Daga Ed Lowther
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Data journalist, BBC News
  • An wallafa

Shugaban Amurka Donald Trump a 2016 ya yi yaƙin neman zaɓensa da shan alwashin kawo ƙarshen kwararar mutane ƙasar ba bisa ƙa'ida ba, inda ya rinƙa ɗora laifin kan 'yan ci-rani da suka shiga ƙasar daga Mexico ba bisa ƙa'ida ba da safarar miyagun ƙwayoyi da aikata laifuka da dama.

A shekara huɗun da shugaban ya kusan kwashewa kan mulki, ta ya hakan ya yi tasiri kan tsare-tsaren shi na shige da fice a ƙasar?

Adadin mutanen da aka haifa waɗanda asalinsu ba 'yan Amurka bane da ke zaune a ƙasar ya ƙaru da kashi 3 cikin 100, daga miliyan 43.7 shekara ɗaya kafin Trump ya zama shugaban ƙasa zuwa kusan miliyan 45 a shekarar bara.

Sai dai wannan ƙaruwar na adadin ya ɓoye wani rukunin mutane mafi girma a adadin - ma'ana waɗanda suka taso daga Mexico suka koma Amurka. Adadin mutanen da ke zama a Amurka waɗanda aka haifa a Mexico na ƙara raguwa tun bayan zaɓen Mista Trump.

Hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta yi ƙiyasin cewa adadin mutanen da ke zama a Amurka waɗanda aka haifa a Mexico ya ragu a hankali tun bayan da Mista Trump ya lashe zaɓe.

Wannan ya samo asali ne sakamakon raguwa a adadin masu shiga ƙasar, amma dai akwai dalilin cewa mutane da dama waɗanda aka haifa a wata ƙasa na komawa ƙasarsu daga Amurka, kamar yadda Anthony Knapp na hukumar ƙidaya ta ƙasar ya bayyana.

Bayan waɗannan sauye-sauyen, akwai wasu tsare-tsare da aka yi wa biza ta ƙasar.

Mista Trump ya bar mutane da dama su shiga Amurka domin su yi aiki na wucin gadi, amma ya sa abin ya yi wuya a ba su takardar zaman Amurka na din-din-din. An samu raguwa a bizar da ake bayarwa ta din-din-din daga adadin mutum miliyan 1.2 a 2016 zuwa kusan miliyan ɗaya a 2019.

Hakan ya jawo matsala ga wasu iyalai na mazauna Amurka da ke da niyyar zuwa Amurka domin zama da 'yan uwansu.

Duk da cewa wannan tsarin ya shafi mutane da dama, babban burin shugaban a tsarinsa na shige da fice shi ne rage adadin 'yan ci-rani da ke shiga Amurka.

Adadin mutanen da ake kai wa Amurka a matsayin 'yan ci-rani a duk shekara, ana bin tsari ne kashi-kashi, inda shugaban ne ke bayyana kaso ko kuma adadin da zai bari su shiga ƙsar.

Dole ne mutanen da ke so su shiga Amurka a matsayin 'yan ci-rani su rubuta takardar neman hakan daga wajen Amurka, da kuma ƙoƙarin shawo kan Amurkan kan cewa za su kasance cikin ƙunci idan suka zauna a ƙasarsu.

A bayyane take cewa Shugaba Trump ya saka matsain lamba ga 'yan ci-rani masu ƙoƙarin shiga ƙasar daga ƙasashen Musulmi - ya taɓa alƙwarin saka dokar cewa zai hana "Musulmai shiga Amurka" - da kuma rage adadin 'yan ci-ranin da ke shiga ƙasar a maimakon hanawa.

Hakan ya sa adadin 'yan ci-ranin da ake bari su shiga ƙasar daga akasari ƙasashen Musulmi irin su Iraƙi da Somalia da Iran da Syria ya zo ya zama ma gaba ɗaya ba a barinsu bayan ya zama shugaban ƙasa.

Rage adadin biza da kuma barin 'yan ci-rani su shiga ƙasar ba ita kaɗai bace hanyar rage mutanen da za su shiga Amurka, haka kuma Mista Trump ya sa komawa ko zama a Amurka ba tare da takardar zama ba ya yi wahala.

Sai dai hakan yana da wuya ba kamar yadda ake ɗaukarsa ba. Domin fahimtar abin da ya faru a lokacin mulkin Shugaba Trump, yana da muhimmanci a san ƙididdigar adadin mutanen da aka fitar daga ƙasar aka mayar da su ƙasashensu ba tare da umarnin kotu ba.

Shugaba Trump bai kawo wani sauyi ba kan adadin mutanen da ake mayar wa ƙasashensu idan aka kwatanta shi da shugaban da ya gabace shi.

Hukumar kula da shige da fice ta Amurka da hukumar kwastam waɗanda su ne ke kula da akasari batun mayar da mutane ƙasashensu, sun bayyana adadin yadda ake korar mutane daga ƙasar a matsayin ba wani mai yawa ba inda suka ɗora laifin ga ƙarancin albarkatu, da kuma tsaiko a "ɓangaren dokoki da shari'a", da sauransu.

Hukumar na fuskantar matsin lamba a iyakarta da Mexico, inda sauyin da ƙasar ta yi na bayar da mafaka ya jawo lamura da dama, inda a wani lokacin ake samun rabuwar iyali da kuma ajiye yara a wurin tsare mutane, inda kuma masu neman mafaka ake mayar da su Mexico.

Duk da cewa kafafen yaɗa labarai sun mayar da hankali matuƙa kan rikice-rikice na kan iyaka, wani rahoto a 2019 ya nuna cewa da ba a kori wasu 'yan ci-rani ba- da adadin da za a samu na waɗanda ake tsarewa kan iyaka zai ninka adadin na shekarar bara, inda hakan ke ƙara yawan adadin mutanen da ke ƙoƙarin tsallakawa zuwa ƙasar.