Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa Donald Trump ya fasa shirinsa na daina bai wa ɗaliban ƙasashen waje biza
Shugaban Amurka Donald Trump ya janye shirinsa na mayar da daliban kasashen waje kasashensu tare da hana su biza idan aka mayar da azuzuwansu ta intanet saboda annobar korona.
Wannan mataki na zuwa ne mako daya bayan an sanar da shirin mayar da daliban kasashensu.
Jami'ar fasaha ta Massachusetts da kuma jami'ar Harvard ne suka shigar da gwamnatin Amurka kara kan wannan shirin nata.
Alkalin lardin mai shari'a Allison Burroughs da ke Massachusetts ya ce bangarorin biyu sun shawo kan matsalar da ta taso tsakaninsu.
Yarjejeniyar ta kara jaddada aiki da wannan tsarin da aka fara tun a watan Maris, yayin da ake tsaka da fama da annobar korona, wanda zai bai wa daliban kasashen waje damar shiga azuzuwansuta intanet idan har ya zamar musu dole, kuma an yarjewa dalibai a kasar yin hakan, kamar yadda jaridar New York Tims ta wallafa.
Daliban kasashen waje da dama ne ke zuwa Amurka karatu ko wacce shekara, kuma suna samar da kaso mai yawa na kudaden shiga ga ga jami'o'i.
Me wannan sabuwar dokar ke nufi?
An shida wa daliban kasashen waje a makon jiya cewa ba za a barsu su zauna a Amurka ba a wannan kakar, har sai dai idan sun koma daukar darussan da za su rika biyawa kansu kudaden makaranta.
Wadanda suka koma kasashensu lokacin da aka ta fi hutu a watan Maris - sakamakon yaduwar korona - an gaya musu ba za a kyalesu su koma ba matukar an mayar da karatunsu ta intanet.
Ma'ikatar da ke lura da shige da fice da ta hana fasakauri sun ce za a rika mayar da mutane kasashen da suka fito matukar ba su cika ka'idojin zama a Amurka ba.
Me jami'o'i suka yi akai ?
Kwana biyu bayan hakan, jami'ar Harvard da MIT suka shigar da karar neman a janye wannan hukunci.
Gwamman jami'o'i ne suka nuna goyon bayansu ta hanyar sanya hannu nuna goyan baya kan korafin a kotu.
Wannan ya mutukar samar da kwarin gwiwa ta yadda jami'o'i sama da 59 suka nuna goyan bayansu, wanda suka ce babu ruwan dokar da zuwa ajin da dalibai suke yi.
Antoni janar na jihohi 18 ne akalla ciki har da na Massachusetts da na California ne suka shigar da karar.
Trump ya ta kokarin ganin jami'o'i da sauran makarantu sun koma ajujuwansu, yana ganin sake bude makarantun wata alama ce ta warwarewar al'amura bayan dakatar da su da aka yi 'yan watannin baya, wanda kuma hakan zai iya amfanar shi a kokarinsa na ganin an sake zabarsa a zaben watan Nuwamba.
Da yawa daga cikin ma'abota ilimi na nuna damuwa kan halin da daliban za su tsinci kansu ciki, tare da tabbatar da ba da tazara yayin da annobar ke ci gaba da yauwa.
Suwa wannan doka za ta shafa?
Wannan doka za ta yi aiki ne ga wadanda ke neman bizar karatu da kuma dalibai masu zuwa koyan sana'o'i. Ma'aikatar tsaron Amurka ta ba da biza ga wadannan mutane har 388,839 a 2019, kamar yadda bayanan hukumar suka zayyana.
A cewar ma'aikatar kasuwanci ta Amurka daliban kasashen waje sun samar da kudin shiga da suka kai dala biliyan 45 a 2018.