Tristan da Cunha: Mutanen da ke rayuwa a garin da ke kan tsauni a tsakiyar teku

Asalin hoton, Getty Images
"Ba zan iya rayuwa a ko ina ba" Harold Green ya shaida wa BBC a 'yan shekarun baya.
Amma Tristan da Cunha, ko kuma TDC ba wajen zaman matsorata ba ne.
Za a iya cewa duk abin da ake cewa a kansa ana rage darajarsa ne.
Idan kana son ganin wajen da ake rayuwa kamar a duniya kamar a ƙarnin baya to ga shi:


Asalin hoton, Alasdair Wyllie
- Ka fara hawa jirgi zuwa Cape Town da ke Afrika Ta Kudu
- Sai a hau kwale-kwale
- Tafiyar kwanaki 18 cikin teku mara daɗin tafiya a duniya, babu fatan samun hutu a wajen da yayyafin ruwa ke neman haɗewa da samaniya, kuma ido ya fara hango wani ƙaton tudu abin birgewa
- Ka fara shirye-shiryenka, ka kuma yi addu'a kada iska mai ƙarfi ta taso ta kifar da kwale-kwalenka.
- Ka gyara kwale-kwale kafin iska ta gwara shi da duwatsu ya kakkarye - ko kuma ka yi ban kwana da shi - kai kuma wani ya tsintoka a wani wajen wata rana
- Ka yi sallama da Edinburgh da ke tsakiyar teku mai hawa bakwai, babban birnin Tristan da Cunha wanda shi ne kuma mazauninsu tilo

Ba shakka za ka iya amfani da kwale-kwale masu sauri: ka mayar da tafiyar ta kwana shida a jirgin ruwan da ake kira SA Agulhas - sai dai shi kuma matsalarsa tafiyar kilomita 2,810 yake yi sau daya a shekara, kuma taƙaitattcen filin ajiye kaya ne da shi. Ko kuma za ka iya samun ragin hanya a jiragen kamun kifi da suke zuwa suna komawa.
Haka yake da wahala zuwa yakin Tristan de Cunha ko kuma zama a can.
"Rayuwar abokai"

Asalin hoton, penguins-and-potatoes.co.uk
Duk mutanen yankin su 245 mata 133 sai kuma maza 112 a lokacin da aka yi ƙidayar karshe. Kuma dukkansu sana zama a Edinburgh ne.
Garin na da wajen shan shayi, da dakin zamantakewa, da wajen aika wasika da kuma mashaya.
Akwai wani ɗan karamin asibiti na zama da kuma wata makaranta ƙarama.
"Sai dai idan ka bar tsibirin, amma mutanen da ka yi makaranta da su, su ne mutanen da za ka ƙare sauran rayuwarka da su," in ji Alasdair Wyllie wadda ta rike matsayin mai ba da shawara a ɓangaren noma, amma ta bar yankin a bayan nan.

Asalin hoton, Google
Anan ne za ka iya haduwa da wadda za ka aura, tun kafin ka fara tunanin aure.
Watakila kuma wani abin mamaki shi ne, in dai kai dan asalin tsibirin ne, da yiwuwar ka riƙa amsa daya daga cikin sunayen yankin shida: Lavarello da Repetto da Rogers da Swain da Green da kuma Glass.
Akwai kuma mazauna yankin biyu da ba a haifesu ba a yankin: wani mutum da matarsa da suka yi aure suka yanke shawarar zama da iyalansu a yankin.
Akwai kuma likita da malami da suke zuwa na wani lokaci daga Burtaniya, saboda yankin a ƙarkashin kulawar Burtaniya yake.
Nishaɗi

Asalin hoton, Getty Images
"Wajen ba hayaniya, za ka rika jin motsin ciyayi" in ji Harold, wadda ta ce tana son zaman lafiya da kuma shirun da mahaifarta ke da shi.

Asalin hoton, Getty Images
Amma intanet "ba shi da ƙarfi a wurin koma in ce ba shi da kyau."
Wani lokacin ma kiran da ake na waya kyauta ne ba a ɗaukar kuɗi.
Akwai wani titi guda da za ka iya tafiyar kilomita uku a jikinsa da ke gefen ruwa, wasu jerin duwatsu ne da aka yi katanga da su saboda kare iska.

Asalin hoton, Alasdair Wyllie
Akwai kuma yiwuwar yin tafiyar ƙasa a tsibirin mai cike da korayen ganye - wanda bai fi ɗakin kilomita 10 ba - zai kuma dauke ka mita 2,062 na hawa da saukar da za ka yi kan tudu kafin ka je bakin teku.
A takaice dai babu wani waje da yake lebur, kuma wannan katangar duwatsun da aka yi ta mamaye kaso biyu cikin uku na yankin.
Duka dai kasar wajen ruwa ne

Asalin hoton, Brian Gratwicke
Tristan da Cunha, ko kuma kawai yankin Tristan kamar yadda wasu suka fi sani, shi ne ainihin inda duwatsu masu aman wuta suke.
Tsibirin Nightingale nan ne inda ƴan yankin Tristan suke zuwa hutu wani lokacin kuma wuri ne da ba a fiye ninƙaya a cikinsa ba saboda wajen rayuwar manyan kifaye ne.

Asalin hoton, Getty Images
Babu 'ya'yan itace babu kayan miya

Asalin hoton, penguins-and-potatoes.co.uk
Zama a wannan yankin da ake irin rayuwar baya a duniya na nufin babu wata magana ta killace kai - yanayin nisa zai maka wannan aiki.
''Amma don babu mai ɗauke da Covid-19 ba ya nufin cutar ba ta shafe mu ba,'' in ji wata mazauniyar yankin Fiona Kilpatrick.
Dokar kullen na nufin jiragen ruwan Afrika Ta Kudu da suke kawo kaya tsibirun ba za su bar Cape Town ba.

Asalin hoton, penguins-and-potatoes.co.uk
Farin cikin haihuwa

Asalin hoton, penguins-and-potatoes.co.uk
Amma wani abun mamaki, shi ne wata yarinya da aka haifa da cutar a farkon wannan shekarar.
"Domin gudun matsala mata da yawa na tafiya Afrika Ta Kudu gab da za su haihu. Amma saboda dokar kullen ta katse duk wata hanyar sadarwa, don haka aka haifi yarinyar a nan a Trintan," in ji Alasdair.
Amma duk da uwar da 'yar suna lafiya, kuma duka jama'a sun yi farin ciki da haihuwar.
Mutanan farko da suka fara zama a yankin a farkon 1800 suna da yawa, amma tun daga nan yawan jama'ar yake yin gaba ya yi baya, cikin gwamman shekaru dai raguwa yake yi.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai wani kyakkyawan labari na cewa an kai wasu 'yan mata uku Burtaniya su yi sakandire, kuma ɗaya daga cikinsu za ta ci gaba da karatu mai zurfi, in ji Alsdair.
A karon farko an samu macen da za ta je jami'a a wannan ɗan ƙaramin yanki.
"Shugabannin yankin na cewa ga duk mai sha'awar komawa yankin har abada ƙofa a buɗe take" in ji Alasdair.











