Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Damar da Najeriya ke da ita ta karbo kayan tarihinta daga Turai
Yayin dawo da gidajen tarihin Turai bayan zanga-zangar adawa da wariyar launin fata da masu fafutikar Black Lives Matter, ƴan siyasar Najeriya na da damar tsara makomar kayayyakin tarihi na Benin, kamar yadda Barnaby Phillips masani kan batun ya rubuta.
Muhawarar da aka shafe shekaru ana yi yanzu ta ƙara zafafa. Da dama a Afrika, da sauran wurare suna cewa yanzu lokaci ya yi da za a dawo da dukiyar kayayyakin tarihi da al'adu da aka wawushe lokacin mulkin mallaka.
Tagullan Benin - da dubban kayan ƙere-ƙere na al'adu da mutum-mutumi da hauren giwa - sun kasance alamu da ake zargi na rashin adalci. Asalinsu daga yankin da ake kira jihar Edo ne a yanzu a kudancin Najeriya.
Kayayyakin da sojojin Birtaniya suka sace a 1897, yawancinsu suna gidajen tarihin ƙasashen yammaci da kuma wasu gidajen tarihin masu zaman kansu.
Gidan tarihin Birtaniya, da ke da kayan tarihin Benin 950, ya sha suka musamman saboda ƙin amincewa ya dawo da su, amma yana ɗaya daga cikin gidajen tarihin da ke ƙoƙarin tabbatar kayayyakinsa a bisa doka.
Sarakunan Edo - Obas - fafutikarsu ta shekaru kan neman dawo da kayayyakin ta kasance a banza.
Amma ƙalilan ne da ke gidajen tarihin ƙasashen yammaci suka ɗauki buƙatun ƴan Afirka da muhimmanci. Masu kula da gidajen tarihi na ƙasashen yammaci sun yi iƙirarin cewa ƙasashen Afrika ba su da ƙarfin da za su iya kula da ƙadarorin nasu.
Amma kuma ƙasashen tarihi na yammaci ba su da wani ƴanci na yin gyara ga ɓarnar da aka yi a shekaru da dama na mulkin mallaka.
Yanzu wannan ya sauya, kuma a bayan fage abubuwa na tafiya.
Tun 2017, ƙungiyar tattaunawa da Benin da ake kira Benin Dialogue Group da ta ƙunshi Oba da gwamnan Edo da gwamnatin Najeriya da gidajen tarihin Jamus da Netherlands daSweden da kuma na Birtaniya - suna diba hanyoyin yadda za a dawo da wasu kayayyakin tarihin a Najeriya.
Sun amince Benin babban birnin jihar Edo a nan za a yi sabon gidan tarihi na Benin Royal Museum.
Gidajen tarihi na ƙasashen Turai za su tallafa da wasu ɗaruruwan tagullan Benin.
Tasirin ya nuna fadar Oba zata kasance cibiyar tattara kayayyakin a birnin Benin.
Daga ƙarshe, mutanen Edo za su yi tozali da wasu kayayyakin al'adunsu na gargajiya.
Gwamna Godwin Obaseki ya taka rawa sosai wajen tattaunawar.
Ya ɗauko hayar wani ƙwararren mai zane daga ɗan asalin Ghana, Sir David Adjaye, wanda ya tsara gidan tarihin Afirka a Amurka da ke birnin Washington DC.
Sai dai akwai ƙalubale idan har ba a sake zaɓen Mr Obaseki, wanda ke neman wa'adi na biyu a zaben gwamnan Edo da za a yi 19 ga Satumba.
Idan har ba a sake zaben Godwin ba, zai yi wahala a ci gaba da aikin," a cewar Phillip Iheanacho.
Tabbas, babu ɗaya daga cikin gidajen tarihin Turai da zai yi hasashen wanda zai yi nasara a zaɓen jihar Edo, ko kuma ya ce ga wanda ya fi dacewa mutanen jihar su zaba.
Amma kuma sun damu da makomar tattaunawar da kuma yiyuwar sake sabuwar tattaunawa da wani sabon gwamna.
Daraktan wani gidan tarihi daga cikin masu tattaunawar Benin ya ce: wannan aikin Obaseki ne - Idan har wani ne daban, abin damuwa ne, zai kare muna ƙwarin guiwa.
Daya daga cikinsu kuma ya ce: "Wannan aikin na buƙatar kuɗi. Idan har aka samu sauyin gwamnati za a samu tsaiko.
Ya ce gidan tarihin "mataki ne mai kyau."
"Muna son haɗa guiwa da Oba domin samar da gidan tarihi da zai nuna kyawawan al'adun mutanenmu."
An sace kayayyakin tarihin Benin. Cin fuska ne, kamar yadda suka ce, dawo da su bisa sharadin gidan gidan tarihi ko kuma yaudarar ƴan siyasar Najeriya, kamar yadda bai dace a yi maganar bashi ba ko kuma wani ƙawance.
Amma akwai wata hanyar ta duba al'amarin.
Gidajen tarihin Turai, na tabbata suna son kawar da sukar shekaru da aka shafe ana yi.
Suna buƙatar sabon gidan tarihi don cin nasara.
Wani mai shiga tsakani ya shaida cewa yadda wasu da ke cikin ƙungiyar tattaunawar Benin suke ganin kayayyakin nasu na Benin " sun kasance abn kunya."
"A zahiri, idan har Obaseki ya kafa rumfa a bayan gidansa, za su iya miƙa masa. don kawar da su."
Buɗe gidan tarihi a garin Benin mai cike da kayayyakin tarihi na mutanen garin da aka mayar daga Turai, zai kasance babban muhimmin lokaci na tarihi a Afirka tun samun 'yancin kai.
Barnaby Phillips tsohon wakilin BBC ne a Najeriya. Littafinsa mai taken "Loot; Britain and the Benin Bronzes" za a wallafa shi a farkon 2021