Mazaunan Amurka da suka koma Ghana sun bayyana wariyar launin fatar da suka sha

Amurkawa baƙaƙen fata da ke zaune a Ghana sun bayyana irin yadda suka fuskanci wariyar launin fata a Amurka
Ghana ta bayyana shekarar 2019 a matsayin shekarar da baƙaƙen fata mazauna Amurka suka fi ziyartar ƙasar ta Ghana.
A shekarar, an samu ƙaruwar baƙaƙen fata mazauna Amurka da suka dawo ƙasarsu ta gado domin ci gaba da zama sakamakon wariyar launin fatar da ake nunawa a Amurka.
A halin yanzu, akwai kusan mutum 5,000 da suka koma zama a Ghana.
Ga waɗanda suka koma Ghana da zama, kisan da aka yi wa George Floyd da kuma zanga-zangar da aka yi ta nuna muhimmancin baƙar fata ya dawo musu da tunanin irin abubuwan da suka fuskanta marasa daɗi.
Na yi tafiyar sa'a biyu daga Accra babban birnin ƙasar Ghana domin na haɗu da wasu tagwaye masu shekaru 37 wato Titus da Tyree Busbee waɗanda suka baro jihar Alabama ta Amurka shekaru kaɗan da suka gabata sakamakon wariyar launin fata.

Mun haɗu a Elmina Castle - wata tsohuwar ganuwa da ke a tashar ruwa da ake jigilar bayi lokacin mulkin mallaka wadda kuma aka fara ginawa a 1482 a gaɓar teku da ke kudancin Ghana.
An yi jigilar dubban 'yan Afirka zuwa Amurka daga Elmina Castle domin zuwa aikin bauta.
Ko da muke tafiya cikin ganuwar, wadda ita ce mafi girma da ake tara bayi a Ghana, sun bani labarin yadda suke zuwa nan domin tuna yadda wannan wuri ya yi tasiri ga rayuwar Amurkawa a yanzu.
Sun bayyana mani cewa su mawaƙa ne a Alabama, kuma a nan suka girma suka yi karatu. Sun bayyana cewa suna gani ana nuna musu wariya lokacin da suka fara yin waƙa.
"Ba za mu iya aiki a wurare da yawa ba," in ji Titus "An saka dokar irin nau'in kayan da za a saka domin kada mu yi waƙa a wurin wasa."
Har ma an haramta musu yin waƙa idan sun je wurin wasa sakamakon suna saka kayan 'yan Afirka maimakon na Turawa. Suna tunanin da gan-gan ake nuna musu wariya. "Akwai jan layi da aka ja mai yawa, dole sai mun biya kafin mu yi wasa," in ji su.
Sun bayyana cewa asalin mazauna Amurka ba su cika son yanayin irin waƙoƙin da suke yi ba, musamman Turawan da suke zaune a garin da suke, inda suke caccakar su da zarginsu da cewa suna tallata waƙoƙin hip-hop a maimakon waƙoƙin asali na ƙasar.

Sun bayyana cewa sun ɗauki shekaru da dama suna tunanin barin ƙasar wanda hakan ya ja suka fara tara kuɗi.
Na tambaye su kan irin abin da suka yi kan abin da ya faru a Amurka a 'yan kwanakin nan, da kuma kukan da duniya ke yi. Sun bayyana cewa lamarin ya daɗe yana tafe, "ba za ku iya ajiye mutane a ƙasa ba na lokaci mai tsawo ba tare da sun tashi ba, in ji Titus.
Muhammida El Muhajir, wata mace mai shekaru 30 da ɗoriya kuma darakta a wani kamfanin tallata hajoji na zamani, ta koma Ghana daga Brooklyn, New York a 2014 inda ta ce ta fuskanci wariya shi ya sa ta koma.
Ina aiki a matsayina na Manaja kuma ni kaɗai ce baƙar fata a kamfanin da ke New York, wata farar fata mai zama a zauren kamfanin na son muƙamin da aka bani, kuma ta ji haushi sakamakon an bani aikin, in ji Muhammida. "Domin ta mayar da martani, sai ta sanar da cewa an sace katin kuɗinta kuma ni take zargi da satar.
An kira 'yan sanda kuma sun tambaye ni ko zan iya zuwa ofishinsu domin amsa tambayoyi," in ji ta.
Ta bayyana mani cewa an riƙe ta na sa'o'i da dama kuma an sake ta ne bayan 'yan sandan sun gane cewa babu wata hujja da za a iya kama ta da sata. "Na fuskanci tashin hankali," in ji ta. "Lamarin shi ne, sakamakon ni baƙar fata ce shi ya sa aka ɗauka kawai ina da laifi," in ji ta.

Ta bayyana cewa zamanta a Ghana ya ba ta dama domin ta huce. "Zai yiwu akwai wasu matsaloli ko kuma nuna bambanci da mutane ke fama da su," a irin halin da take ciki in ji ta. "Amma yanke wa mutum hukunci don launin fatar jiki ba ya cikinsu.

Abin da kisan George Floyd ya jawo a Afrika
Mutuwar George Floyd a hannun 'yan sanda ta jawo zanga-zanga a faɗin nahiyar Afirka, domin nuna goyon bayansu ga ɗan uwansu ɗan Afirka.
Na ziyarci ƙungiyar 'yan Afirka masu zama a ƙasashen waje a cibiyar W.E. B. Du Bois da ke Accra babban birnin Ghana.
An rubuta sunan George Floyd da launin baƙi a jikin farin bango domin girmama shi kan abin da ya faru da shi. An sadaukar da bangon kuma ga wasu sauran 'yan Afrika mazauna Amurka waɗanda suka mutu sakamakon irin wannan lamari.
Ƙungiyar 'yan Afrika masu zama a wasu ƙasashe, wadda ke aiki tare da Ƙungiyar Tarayyar Afrika, na bayar da tallafi ga baƙaƙen fata mazauna Amurka masu komawa gida.
Ta bayyana mani cewa akwai baƙaƙen fata mazauna Amurka da dama da suka nuna sha'awar komawa Ghana sakamakon nuna wariyar launin fata da suke fuskanta.
"Mutanen da ke Amurka na cewa suna so su dawo gida, ka san muna jiran su. Idan za ka tambaye ni ko zan koma Amurka yanzu, zan ce a'a," in ji ta.
Ita ma daga Amurka ta dawo. Ghana ce ƙasa ɗaya tilo a Afirka da ke da doka da ke bayar da dama ga 'yan Afirka daga wasu ƙasashe su yi aiki a ƙasar ba tare da an sabunta takardar bizar su ba ko kuma ta aiki.
Yayin da baƙaƙen fatan Amurka da ke zaune a Ghana ke fuskantar sabuwar rayuwa a wata ƙasa daban, suna da yaƙinin cewa zanga-zangar da ake yi a Amurka da kuma faɗin duniya zai zama wani mataki na sauyi ga rayuwar baƙar fata a Amurka.












