Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Amurka: Abubuwan da Amurka ta yi daidai da kura-kuranta kan cutar korona
Amurka na ci gaba da samun ƙaruwa a yawan masu kamuwa da cutar korona a ƙasar.
A wannan makon, Amurka ta samu mutum 60,000 da suka kamu da cutar ta korona a rana guda.
Ƙasashe da dama da suka ci gaba da ke nahiyar Turai da Asia sun ɗauki tsauraran matakai da suka haɗa da yawan gwaje-gwaje da neman waɗanda suka kamu, inda kuma suka sassauta dokar kulle a hankali ba tare da sauri ba.
Ƙasashe da dama ba su samu irin wannan matsalar da Amurka ta fuskanta ko kuma take fuskanta ba.
An gudanar da bincike da kuma bitar abubuwan da Amurka ta yi na daidai da kuma waɗanda ta yi ba daidai ba, a daidai lokacin da Amurka ta shiga wani sabon babi na annobar wadda ba alamun ƙarshenta.
INA AMURKA TA YI KUSKURE?
An buɗe jihohi cikin gaggawa
A watan da ya gabata, yawan masu kamuwa da cutar bai fito da wani yawa ba. Cutar ta yaɗu a hanakali, har ake ganin yawan masu cutar ba ya ƙaruwa.
Wannan ne ya ja aka sassauta dokoki a jihohin ƙasar da suka haɗa da Texas da California da Florida da Arizona.
Akasarin waɗannan jihohin sun yi gaban kansu ba tare da bin ƙa'idojin hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a ƙasar ba, da ya haɗa da ko wace jiha ta jira ta ga ta samu raguwa na masu kamuwa da cutar na makonni biyu, da kuma samun kashi biyar cikin 100 na waɗanda aka yi wa gwajin cutar ba su ɗauke da cutar.
Sai hakan ya sa adadin yawan masu kamuwa da cutar ya saka mutane cikin ruɗani, sakamakon jihohin da cutar ta yi ƙamari kamar New York da New Jersey suna samun raguwa, sai kuma jihohin da babu cutar sosai suna samun ƙaruwa.
A halin yanzu, an kulle kasuwanni da sauran wuraren kasuwanci a Texas da California da Arizona da wasu jihohin tare da saka dokar saka takunkumi dole domin rage yaduwar cutar.
"Mun buɗe Arizona cikin sauri," in ji magajiyar garin Arizona Kate Gallego, a wata tattaunawa da ta yi a talabajin. "Muna cikin jihohin ƙarshe da muka saka dokar kulle kuma muna cikin na farko da muka fara buɗewa".
Mutane 8,181 da suka kamu da cutar a Texas a ranar Lahadi na cikin adadi mafi yawa da aka samu. A Arizona, kashi 14 cikin 100 na waɗanda ake yi wa gwaji ana samun su ɗauke da cutar.
California wadda ita ce jiha da ta yi nasara da farko a wurin daƙile yaɗuwar cutar ta samu ƙaruwar cutar da kusan kashi 90 cikin 100 a makonni biyu da suka gabata, bayn jihar ta bayar da damar buɗe kasuwanci a watan Mayu.
Rabuwar kai wurin saka takunkumi
Bayan jihohi da dama sun yanke shawarar sassauta dokokin kullen da suka saka duk da gargaɗin da masana kiwon lafiya suka bayar, ɗaya daga cikin hanyoyin da ya kamata a ce an kare kai daga yaɗuwar cutar ita ce hanyar saka takunkumi.
Wani bincike da aka gudanar a watan Yuni ya nuna cewa kashi 49 cikin 100 na 'yan jam'iyyar Republican ke saka takunkumi awatan da ya gabata, inda kuma kashi 83 cikin 100 na 'yan Democrats ke sakawa.
'Yan jami'iyyar Republican suna gnin tamkar wani mataki ne mai tsauri na saka takunkumin.
Shi kansa shugaban Amurka Donald Trump wanda ɗan jam'iyyar Republican ne ya taimaka wajen samun rabuwar kai wajen saka takunkumin inda akwai lokacin da ya taɓa zaulayar wani ɗan jarida wanda ya ƙi cire takunkuminsa a yayin wani taro.
Su kansu ma'aikatan lafiya ba za a cire su daga zargin kawo rabuwar kai ba a wurin saka Takunkumi domin tun a farko su suka ce ba lallai bane saka takunkumin yana kare kai daga ɗaukar cutar ba.
Sai daga baya kuma suka sauya matsayarsu kan batun saka takunkumin.
INA AMURKA TA YI DAIDAI?
Samun Sauƙi a NewYork
Duk da cewa ana samun yawan ƙaruwar masu ɗauke da cutar ta korona a jihohi da dama da ke kudanci da kuma yammacin Amurka, New York ta taɓa zama matattarar wannan cuta ta korona kuma a halin yanzu an samu raguwar yaɗuwar cutar matuƙa.
Yawan mace-mace a jihar ya kai maƙura inda mutum 799 suka mutu a jihar. A halin yanzu, kashi 1.38 cikin 100 na waɗanda aka yi wa gwajin gwajin a ranar Juma'a ne suka kamu da cutar.
A daidai lokacin da sauran jihohi ke ƙara saka dokar kulle, New York ta fara buɗe wurare na gwamnati da masu zaman kansu da suka haɗa da wuraren motsa jiki da wuran aski da gyaran jiki. Sai dai har yanzu wuraren cin abinci akasari a kulle suke.
A daidai lokacin da jihar ke ƙoƙarin sassauta dokar kulle, akwai yiwuwar cutar ta sake ɓulla.
Tattalin arziƙi ya fara daidaita
Wani abin mamaki ya faru da tattalin arziƙin ƙasar. Tattalin arziƙin Amurka da masu masana suka yi hasashen zai sha wuya sai ga shi ya fara farfaɗowa tare da kuma daidaita.
An yi kiyasin cewa za a samu raguwar rashin aikin yi da kusan kashi 20 cikin 100 sai kuma gashi an samu kashi 13.3 kacal. Sai kuma a watan Yuni, ya ragu zuwa kashi 11.4 .
Haka zalika farashin hannayen jari sun fara komawa yadda suke a lokacin hunturu.
Samun ci gaba a kimiyyance
Yayin da cutar ke ci gaba da ƙamari a jihohi da dama na ƙasar, masana kimiyya musaman likitoci na ƙoƙarin nemo magani da kuma riga-kafin cutar korona.
Remdesivir, wanda magani ne na kashe ƙwayoyin cuta ya nuna alamu wajen rage zafin cutar a asibitoci waɗanda ke ɗauke da masu cutar.
Wani sabon bincike ya nuna cewa maganin dexamethasone na kawo sauki matuka ga masu ɗauke da cutar da ke ƙarƙashin kulawar na’urar tamikama wa numfashi ta ventilaor.
Akwai kuma wasu alamomi da ke nuna cewa amfani da wani na'ui na jinin waɗanda suka warke daga cutar ta korona kan taimaka wa waɗanda ke fama da ita, sai dai har yanzu ba a gama tabbatar da wannan batu ba.