Kullen Coronavirus: Ko yanayi na iya sa mu farin ciki?

    • Marubuci, Daga Emily Kasriel
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

"Halin da muke ciki yanzu ya sauya rayuwarmu zuwa halin rai kwakwai mutu kwakwai," in ji Dakta Anna Jorgensen, wadda take bincike kan alaka tsakanin muhalli da ingancin lafiya a Jami'ar Sheffield.

"Mun daina tunanin cewa ba za mu mutu ba," a cewarta.

A lokacin da mutane da yawa ba sa iya aiki, ko kuma suke aiki daga gida, da yawa daga ciki suna duba yanayi a unguwanninsu a wani yunkuri na mayar da hankalinsu ga muhallinsu.

Kamar yadda wani mai amfani da shafin Instagram y ace: "Kulle na sa mutane su gano sabbin hanyoyin komawa gida. Na gudo daga 'ofis' na bi ta hanyar Rafin Trent wanda ke gefen hanyar gidanmu, na wuce tosffin kutturen itatuwa da aka sare da tsuntsaye masu ban sha'awa."

Gurbatacciyar iskar da masana'antu da motoci ke fitarwa ta ragu, don haka an fi saurin ganin sararin samaniya a yanzu da taurarin da ke sama. Haka kuma, tunda karar da a kan ji a birni yanzu ta ragu, an fi saurin jiyo kukan tsuntsaye.

Haka kuma, mutane na nuna zakuwarsu na son yin noima. Abubuwan da aka fi dubawa a shafin Google, wato Google Trends sun nuna cewa a fadin duniya, mutanen da ke duba kalamai kamar 'taki' da 'iri' sun rubanya idan aka hada da bara.

Ko yanayi na iya taimaka mana wajen tafi da damuwarmu?

Yayin da ba a fiya adana bayanai kan yadda yanayi ke tasiri a kan lafiyarmu ba, bincike da dama sun nuna cewa yanayi na da kyakkyawan tasiri kan lafiyar kwakwalwarmu.

Ko yaya idan mutum ya ribaci wani bangare na yanayi - misali ya yi minti goma a waje iska na kadawa, ko kuma ya sha hasken rana - hakan na iya rage gajiya, a cewar Dakta Mathew White na jami'ar Exeter.

Idan muka mayar da hankalinmu ga kallon filaye masu kyau kamar gabar teki ko daji mai cike da itatuwa, mu kan ji dadi mai karfi a zukatanmu, a cewarsa.

Mayar da hankali ga yanayi na iya taimaka mana wajen samun farin ciki da karfi, tare da sanin abin da muke so da inda muka sag aba, sannan sai mu ga ayyukan da ke gabanmu sun yi mana sauki.

Dakta Gretchen C Daily na Jami'ar Stanford da ke Amurka ya yi amfani da wannan shaidar wajen taimakawa Babban Bankin Duniya da gwamnatocin wasu birane a fadin duniya samar da manufofi don shigar da yanayi da muhalli cikin gineiginemu na birane.

Ayyukan da suka danganci muhalli da yanayi kamar aikin lambu ko noma, na daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen magance cutukan kwakwalwa a fadin duniya tsawon shekaru.

Likitoci a Landan da Liverpool da Dorset na bai wa masu fama da cutar tsananin damuwa shawarar mayar da hankali ga yanayi. Kamar yin tattaki na dan wani lokaci ko shuka na'a-na'a har ta girma.

Wani bincike da aka sa manyan talabijin dauke da hotunan yanayi mai kyau a wajen wani ofishi ya nuna cewa alakar da mutane ke da shi da sauran mutanen na karuwa.

Sauti na da tasiri a kan lafiyar kwakwalwa, a cewar mai bincike Alex Smalley.

Don haka kana iya kara farin cikinka ta hanyar sauraren sautukan abubuwan da suka danganci yanayi kamar karan ruwa a teki ko sautin tsuntsaye.

Dakta Jorgensen na ganin cewa kallon wasu abubuwa da suka danganci yanayi kamar yadda tsirrai da dabbobi suka rayu duk da wasu wahalhalu na rayuwa na iya taimaka mana wajen samun kwarin gwiwa a rayuwarmu.

Ko me ya sa yanayi ke yin tasiri mai kyau?

Daga cikin abubuwan da yanayi ke iya yi shi ne har da wanke duk wani abu da ke jawo mana damuwa in ji Dakta Daily.

Daga cikin abubuwan da yanayi ke iya yi shi ne har da wanke duk wani abu da ke jawo mana damuwa in ji Dakta Daily.

'Yan kananan motsi kamar na ruwa ko tafiyar giza-gizai a sama na matukar yin tasiri a yadda muke tunani ta hanyar dauke mana hankali daga damuwarmu.

Kula da shuka na taimaka mana wajen fahimtar ikon da muke da shi wajen raino, kuma mu ji gamsuwa idan shukar ta girma, wanda Dakta Jorgensen ya ce yana da muhimmanci musamman ga masu fama da cutar tsananin damuwa

Hanyoyin da za a bi don a mori yanayi

A cewar Dakta White, ana iya morar yanayi sosai idan aka ware sa'o'I biyu a mako aka mayar da hankali kan yanayi. Sannan mu yi amfani da bangarorin jikinmu kamar ji da gani da dandano da kamshi don samun ribar haka.

Shawarwari daga kwararrun da suka bayar da gugunmuwa:

  • Ku kai ziyarar a-kai-a-kai kan wata bishiya kusa da gindaku don ganin yadda ganyayyakin ke sauyawa. Tsuntsaye na kai ziyara kan bishiyar? Bawon bishiyar na da kwari ko gamsa kuka a kansa?
  • Ku bude taga don sauraron sautin ganyayyaki ko kamshin kasa bayan an yi ruwa.
  • Ku yi tattaki da zarar gari yaw aye ko kafin rana ta fadi, lokacin da launukan sama suka sauya kuma yanayi ya yi kyau.
  • Shuka iri, ta hanyar amfani da na kayan marmari ko wata bishi a kusa da ku.
  • Ku yi tunanin yanayi mai kyau idan kuna girki, ku mayar da hankali kan kaloli masu haske da dandanon kayan marmari musamman masu tsami. Idan kuka ji kamshin gahawa da safe, ku yi tunanin tsuntsayen da suke taimakawa itatuwan gahawa wajen yin 'ya'ya.
  • Ku sa zanen abubuwan da suka shafi yanayi a gidajenku kamar rassan bishiya a jikin bangonku.

Karin Bincike daga Kate Provornaya