Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Ko yaya rayuwa da addini za su kasance bayan annobar?
- Marubuci, Daga Fernando Duarte
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
Yayin da kasashe da dama suka fara shawo kan annobar, gwamnatoci sun fara rage tsaurin dokokin da suka sa don hana yaduwar cutar.
Ba za mu ci gaba da rayuwa kamar yadda muka saba a baya ba , amma babu shakka janye dokokin kulle sun kwantar da hankalin mutane da masana'antu bayan makonni da dama ana kulle a gida.
Cutar korona ta bulla a sassan duniya daban-daban ta hanyoyi da dama, don haka dage dokokin kullen ma za su bambanta tsakanin birane.
Amma kuma kasashe da daman a da kusan kalubale iri daya. A nan, mun duba wasu bangarori masu muhimmanci a lokacin da muke tunkarar karshen kullen.
A guji annoba a karo na biyu
Masana kimiyya sun gargadi hukumomi kan hadarin gaggauta dage dokar kulle, saboda hakan na iya janyo barkewar annobar a karo na biyu.
"kasashe da daman a ganin raguwar mutane masu dauke da cutar da masu mutuwa dalilin cutar bayan makonni biyu ko uku suna kulle," in ji Pushan Dutt, Farfesa a bangaren tattalin arziki a Makarantar Kasuwanci ta Insead.
"Amma wannan na iya zama kamanceceniya da rayuwar da aka saba a baya. Kasar Singapore na iya zama misali."
Singapore ta ga karuwar masu dauke da cutar bayan da ta sassauta tsauraran matakan da ta sa lokacin da ta zama kasar da cutar korona ta fi yi wa barna bayan China a watan Fabrairu.
Mutum 3,000 ne suka kamu da cutar a cikin kwanaki 3 kacal a tsakiyar watan Afrilu - kuma dalilin haka ta kara kakaba dokar har zuwa 1 ga watan Yuni.
Japan ma ta sake fuskantar barkewar annobar a karo na biyu a arewacin kasar.
An sake sa dokar hana fita a birnin Hokkaido a karo na biyu, bayan da aka dage na farkon a lokacin da aka kai mataki da babu mai dauke da cutar ko daya ran 17 ga watan Maris.
Don haka, hikimar gujewa barkewar annobar a karo na biyu na taimakawa kasashe da dama da ke shirin dage dokar kullen.
Italiya misali, na saukaka dokarta ta kulle ta tsawon mako 7 ta hanyar bude gidajen cin abinci da shagunan sayar da barasa amma mutane ba za su shiga ciki su ci su sha ba sai dais u saya su wuce.
Yayin da filiyaen shakatawa suka sake budewa, dokar barin tazara na aiki a wuraren.
"Dole ne mu guje wa daukar matakai cikin gaggawa," in ji kwamishinan harkokin cutar korona na Italiya, Domenico Arcuri a makon jiya.
"Har yanzu cutar na nan a cikin mu - ba kamar da ba, amma tana nan."
Yin gwaji sosai, da lalubo mutanen da suka yi mu'amala da masu dauke da cutar, sun yi amfani sosai a kasashen nahiyar Asiya da annobar da fara barkewa.
Don haka, ana kaddamar da su a wasu kasashen daki-daki, a wani bangare na kokarin sa ido kan yiwuwar sake barkewar annobar.
Yadda za a tayar da tattalin arziki
Daya daga cikin manyan dalilan da suka sa aka sassauta dokokin kulle, shi ne tsananin bukatar rage tasirin da annobar ta yi kan tattalin arziki.
Daga kananan sana'o'I zuwa manyan masana'antu, duk sun fuskanci faduwa.
Asusun Lamuni na Duniya, IMF na hasahsen tattalin arzikin duniya zai ragu da kasha 3 cikin 100 a 2020, a kiyasin da aka yi a watan Afrilu. Watanni uku kafin annobar korona ta barke, an yi has ashen tattalin arzikin zai karu da kasha 6 cikin 100.
Hukumar Kwadago ta Duniya, ILO ta yi kiyasin cewa ma'aikata biliyan 1.6 ne ke fuskantar rashin tabbas, yayin da sana'o'I miliyan 430 ke "cikin hadarin durkushewa".
Ba abin mamaki bane kenan da gwamnatoci a fadin duniya suka samar da tsare-tsaren rage radadi ga ma'aikata da kamfanoni.
A kasashen G-20, kudaden da aka bayar na rage radadin matsin tattalin arziki sun kama daga kasha 0.7 cikin dari nag aba daya kudin da kasar ta samar a Mexico zuwa kasha 21 cikin 100 a Japan.
Kuma gwamnatoci sun sanya dokokin kan yadda za a gudanar da aiki kulli yaumin bayan an bude kasashen. Jamus, misali, ta bayar da shawara ta musamman ga ko wace sana'a, kama daga manyan masana'antu zuwa shagunan gyaran gashi.
Hakan zai yi aiki? Da kamar wuya.
Shugabar bangaren bincike ta IMF, Gita Gopinath na ganin cewa tattalin arzikin duniya na daf da fuskantar koma bayan dala tiriliyan 9.
"Girma da saurin yadda ayyuka suka tsaya cik ba abu ne da aka taba gani ba a rayuwar nan," kamar yadda Gopinath ta rubuta a shafin IMF na intanet.
The IMF's director of Research Gita Gopinath, believes that the global economy is set to take a USD9 trillion hit - and that's a best-case scenario.
"The magnitude and speed of collapse in activity that has followed is unlike anything experienced in our lifetimes," Gopinath wrote in the IMF blog.
Komawa aiki
Saboda mafi yawan ma'aikata ba za su iya aiki daga gida ba, an matsa wa gwamnatoci lamba su dage dokokin kulle.
Bangladesh na daya daga cikin irin wadannan kasashe da aka yi lallaba gwamnati ta dage dokar, kuma an dage dokokin yanzu.
Daruruwan masana'antu a bangaren kayan sawa, bangaren da tattalin arzikin kasar ta fi dogara da shi, sun bude a karshen watan Afrilu duk da gwmnati ta tsawaita dokar kullen har zuwa tsakiyar watan Mayu.
A matsayinta na kasa ta biyu da ta fi fitar da kayan sawa, masana'ntun Bangladesh 4,500 ne suka shiga matsi bayan da Turai da Latin Amurka suka soke odar kayan da suka yi daga wajenta.
"Sama da ma'aikatan masana'antun dinka kayan saw a miliyan biyu ne za su iya rasa ayyukansu," Rubana Hug , shugaban kungiyar masu dinkawa da fitar da kayan sawa ya yi gargadi.
Kuma akwai fargabar cewa masana'ntu a fadin duniya ba za su iya tabbatar da dokar nan ta barin tazara ba ko kuma su samar wa ma'aikatansu kayan kariya yadda ya kamata.
Belgium na daya daga cikin kasashen da da suka dauki matakai don tabbatar da barin tazara: ma'aikata a tashar jirgin ruwa ta Antwerp, za su yi gwaji da wani awarwaro da ke yin 'yar kara idan mutum ya matso kusa kai fiye da mita biyu.
Za a iya amfani da bayanan awarwaron wajen gano mutanen da aka yi mu'amala da su.
Ana gwada irin wadannan tsare-tsaren a Amurka.
Sai dai dakatra da ayyuka cik ba durkusar da sana'o'I kawai ya yi ba: bangaren noma na fuskantar koma baya saboda rashin ma'aikata wanda ya shafi samar da abinci.
A Indiya, manoman ganyen shayi sun fuskanci asara a karon farko kan ganyen Darjeeling kuma ana fargabar za a sake fuskantar irin haka. Kuma ba ganyen shayi ba kawai - an yi asarar kayan abinci da dama a fadin duniya saboda annobar ta hana a yi girbi.
Kasashen da suka dogara da noma na neman hanyoyin da za su saukaka dokar yadda manoma za su takaita asara.
Yadda za a bude makarantu
Rufe makarantu na daya daga cikin matakan da aka dauka a duka kasashe don takaita yaduwar annobar.
170 cikin 193 na kasashen Majalisar Dinkin Duniya sun rufe dukka makarantunsu zuwa karshen Afrilu, a cewar Unesco, hukumar MDD ta bangaren ilimi.
An yi kiyasin cewa dalibai biliyan 1.3 a fadin duniya ne rufe makarantun ya shafa.
Wasu kasashen sun fara bude makarantunsu a yanzu kuma sun kaddamar da matakan da za su tabbatar yara da sauran ma'aikata sun tsare kansu.
Wannan ya hada da rage yawan dalibai a aji guda na wucin gadi zuwa takaita daliban da za su je makaranta (A Burtaniya, dalibai 'yan shekaru 10 zuwa 12 ne za su fara komawa) da kuma dokar barin tazara.
A wata makarantar firamare a birnin Hangzhou na China, an sanya wa yara wata hula ta musamman don taimaka masu wajen barin tazara.
Ana gwajin zafin jiki a Vietnam, yayin da a Norway an rarraba lokacin da za a kai kuma a dauki wasu yaran daga makaranta.
A Denmark, an sa doka kan lokacin tara: yara na iya taruwa amma kar su wuce mutum shidda a lokaci guda.
Wasu masana kimiyya sun nuna damuwarsu kan sake bude makarantun bayan wani bincike ya nuna cewa yara na iya yada cutar kamar manya.
Amma kwararru a bangaren ilimi sun ce komawa makaranta na da alfanu ga ilimin yara da lafiyar kwakwalwarsu.
"Karuwar rashin daidaito da cutuka da rikici da mayar da yara 'yan kwadago da auren wuri na daga cikin wasu hadurran da yaran da suka dade bas a zuwa makaranta ke fuskanta", in ji Henrietta Fore, darektar Asusun Kananan yara na Majalisar dinkin Duniya (Unicef).
Mutanen da ke rayuwa a birane, inda mutane suka fi yawa sun fi shiga hadarin kamuwa da cutar.
Don haka, yayin da ake cire dokar kulle, wasu daga cikin abubuwan da matakan za su fi mayar da hankali a kai su ne sa ido kan yadda rayuwa za ta koma yadda aka saba a manyan biranen duniya.
Kasashe da yawa na dar-dar wajen sassauta dokokin taruwa a wuri guda kamar gidajen cin abinci da shagunan sayar da barasa da wuraren kallo.
A Thailand, an umarci wuraren cin abincin da ba su da damar sa kwastomominsu su bar tazara, sus a shingaye a tsakanin tebura.
Don rage cinkoso a motocin haya, inda barin tazara zai iya zama kalubale, wasu biranen na duba wasu hanyoyin.
A birnin Milan da cutar ta yi wa mummunar illa, an samar da titunan Babura na wucin gadi yayin da magina da ma'aikatan kamfanoni ke shirin komawa aiki.
Magajin garin ya sa an rubuta wani sako a kan titin: "Idan gidanka na da nisan kilomita daya daga wurin aikinka, ka taka da kafa ko ka hau keke. Wannan zai amfane mu, kai ma zai amfane ka."
Haka kuma, wasu biranen na duba yiwuwar ci gaba da amfani da matakin da aka dauka lokacin da aka sa dokar kulle na takaita miotocin da ke yawo.
Wani misali shi ne Bogota. Babban birnin Colombia birni ne da masu keke ke walwala tun kafin annobar Covid-19 ta barke, inda yake da titunan tuka keke masu nisan kilomita 550 - kuma shi ne birnin da ya fi ko wanne yawn titunan keke a biranen Latin amurka.
Amma yaduwar cutar ya sa an same gina wasu titunan keke, don rage cunkosa a motocin haya.
Gwamnatin kasar ta ce ba za a bari motoci su hau wadannan titunan ba, inda aka kara wasu titunan masu nisan kilomita 45 zuwa karshen Afrilu.
Zirga-Zirga
"A shekaru ashirin da suka gabata, mun yi kokarin hana ,mutane sayen motocin kansu," Nicolas Estupinan, babban jami'I a hukumar zirga-zirga ta Bogota, ya shaida wa jaridar El Tiempo.
"Dole ne mu nemi wasu hanyoyin. Hawa Keke wata dama ce."
A Paris, magajin gari Anne Hidalgo ta ce za a koma yadda ake kafin zuwan annobar da zarar faransa ta sassauta dokar kullenta ran 11 ga watan Mayu.
"Ina mai tabbatar da cewa ba za mu taba bari motoci da gurbacewar muhalli su kutso da mana ba, a cewarta.
Tanaso ta fito da wani shiri inda birnin Paris zai zama "birni na miniti 15": a takaice mazaunin birnin ya samu duk wani abu da yake bukata cikin tafiyar minti 15 daga gidansa.
An fito da wasu tsare-tsare masu kama da wannan a wasu sassan duniya kafin annobar Covid-19. Yanzu akwai yiwuwar wadannan tsare-tsaren za su samu karbuwa.
"Watakil a manyan birane sai an sake kirkirar wasu kananan biranen a cikinsu,£ in ji Elvis Garcia, kwararre a bangaren lafiyar al'umma kuma malami a Jami'ar Harvard.
Sabbin hanyoyin Ibada?
Dokar kulle ta shafi tarukan addini sosai. Yaduwar cutar ta dakatar da wasu idabun.
Ta shafi addinin Kirista da Yahudanci a lokacin Easter da Passover, wasu daga cikin manyan ibadunsu na shekara-shekara.
An soke bukukuwan sabuwar shekara na addinin Buddha a Kudu maso gabashin asiya.
Akwai yiwuwar cutar korona za ta janyo a dakatar da ayyukan Hajji, taron kusan mutum miliyan biyu a kasar Saudiyya.
Amma wasu kasashen na kokarin ci gaba da halartar tarukan ibada.
Iran ta sanar da sake bude masallatanta a kusan bangare daya cikin uku na kasar, a wuraren da hukumomin lafiya ke ganin cutar ta bace.
Amma a lokacin da ayke Magana a talabijin, Shugaba Hassan Houssani ya yi jan-kunne kan yadda mutane za su tafi da ayyukansu na ibada.
"Barin tazara ya fi sallar jam'I muhimmanci," a cewarsa.
Suna kulle a gida, kungiyoyin addini da yawa sun koma shafyukan intanet wajen gudanar da ibadunsu.
Kwararru na ganin cewa ba lallai ne wannan ya sauya ba ko bayan an cire dokar kullen.
A Italiya, misali, gwamnati ba ta amince da bude majami'u ba a wannan matakin - abin da ya bata wa malaman addini a kasar rai.
"Malaman coci a Italiya ba za su amince da wannan tauye hakkin addini ba," a cewar gamayyar kungiyoyin majami'un Italiya.
Wannan batu y ace-ce-ku-ce har Fafaroma Francis ya nemi "a bi lamarin a sannu".
"A yayin da muka fara sassauta dokokin kulle, mu yi addu'a Allah Y aba mu, dukanmu, hakuri da juriya ga dokokin yadda annobar ba za ata dawo ba," in ji Fafaroman.