Coronavirus: Taswirar da ke nuna yawan wadanda suka kamu a duniya

An wallafa

An fara wallafawa ranar 22 ga watan Afrilu. Za a dinga sabunta shi kullum.

Zuwa yanzu akwai mutum miliyan da dubu 500 da aka tabbatar sun kamu da cutar korona a kasashe 185 a duniya. A kalla 178,000 ne kuma suka mutu.

Yawan masu cutar a Amurka ya nunka sau hudu fiye da sauran kasashe.

Wannan taswirar ta kasa na nuna yadda annobar ta yadu a duniya tun farkon barkewarta a China a watan Disambar 2019.

Mutum nawa ne suka mutu?

A karshen shekarar 2019 ce cutar mai alaka da numfashi ta fara barkewa a birnin Wuhan na China.

A hankali take yaduwa a kasahsen duniya da dama sannan yawan wadanda suke mutuwa na ta karuwa.

Duba wannan teburin na kasa don ganin bayanan alkaluman cutar a fadin duniya.

Kwayoyin cuta na 'virus' na sauya fasali ko yaushe, amma sauye-sauyen da ke faruwa ga asalin kwayoyin halittarsu ba shi da yawa.

Ana sa rai kwayoyin cuta su sauya su rage karfi nan gaba, amma babu tabbacin haka.

Fargabar ita ce idan coronavirus ta sauya, garkuwar jiki ba za ta gane ta ba kuma riga-kafinta ba zai kare mutane daga kamuwa da ita ba.