Coronavirus: Ko cutar za ta fantsama kasashen da ba su san ta ba?

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Owen Amos
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
A ranar 12 ga watan Janairu kasa da watanni uku da suka gabata annobar coronavirus ta fara fita a kasar China. A lokacin ba a samu ko da mutum daya da ya kamu da cutar a wata kasa da ba Chinar ba.
A ranar 13 ga watan na Janairu ne katsam sai annobar ta karade duniya. An samu mai dauke da cutar a Thailand da Japan da Koriya ta Kudu da kuma Amurka.
Daga nan ne kuma sai cutar ta fantsama a sauran kasashen duniya.
Yanzu haka dai akwai masu dauke da cutar ta cornavirus fiye da milyan daya a fadin duniya. Abun tambaya yanzu shi ne a dai-dai lokacin da jama'a ke ci gaba da mutuwa sakamon cutar kuma asibitoci ke kara cika da masu cutar, ko akwai kasashen da har yanzu ba su san wannan cutar ba? Amsar ita ce e, akwai su.

Asalin hoton, EPA
Kasashe 193 ne dai mambobin Majalisar Dinkin Duniya.
A ranar 2 ga watan Afrilun 2020, akwai kasashe 18 da ba su da masu dauke da cutar ta Covid-19 kamar yadda bayanan BBC suka dace da alkaluman jami'ar Johns Hopkins University.

Kasashe 18 da ba su da coronavirus:
- Comoros
- Kiribati
- Lesotho
- Marshall Islands
- Micronesia
- Nauru
- North Korea
- Palau
- Samoa
- Sao Tome and Principe
- Solomon Islands
- South Sudan
- Tajikistan
- Tonga
- Turkmenistan
- Tuvalu
- Vanuatu
- Yemen

Wasu kwararru sun amince cewa kasashen da ba su da cutar ka iya yiwuwa suna da ita amma saboda masu ita ba su yi korafi a kanta ba. Misali kasar Koriya ta Arewa kwata-kwata ba ta da ko da mutum daya da ya kamu da cutar kamar kasar Yemen mai fama da yaki.
To sai dai akwia kasashen da kwayar cutar ta cornavirus ba ta isa ba. Yawancin wadannan kasashe tsibiri ne da ke da karancin masu ziyartar su - 7 daga cikin kasashe 10 da aka fi ziyarta a duniya kamar yadda alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka nuna, ba su san cutar cornavirus ba.
Kasancewarsu masu nisa na nufin wani abu guda wato sun kasance kasashen da su ne ma suka amsa sunan tazara fiye da yekuwar da ake yi ta jama'a su bayar da tazara a tsakaninsu.
To sai dai Lionel Aingimea, shugaban Nauru daya daga cikin kasashen 18 ya ce shi kam yana cikin ko-ta-kwana inda ya shaida wa BBC cewa cutar cornavirus al'amari ne mai bukatar kulawar gaggawa daga gwamnati.

Kasar ta Nauru ta dauki wasu matakai na ko-ta-kwana tun bayan barkewar cutar coronavirus a wasu kasashen duniya:
- A ranar 2 ga watan Maris an hana matafiya shiga kasar daga China, Koriya ta Kudu da Italiya. Sannan kwanaki biyar bayan nan an hana 'yan Iran shiga kasar.
- A tsakiyar watan na Maris din dai jiragen kasar ta Nauru ta dakatar da jiragenta zuwa tsibirin Fiji da Kiribati da kuma Marshall Islands.
- Har wa yau fasinjoji masu shiga kasar daga Italiya an tilasta musu killace kai na kwanaki 14 a otal din kasar.
Wannan tsarin da Nauru ta dauka in ji shugaba Lionel Aingimea ana kiran sa da 'kama ka kunshe'.

Asalin hoton, Getty Images
Nauru dai ba ita kadai ba ce karamar kasar da ayyana batun yaki da cornavirus a matsayin ta-baci ba, akwai sauran kananan kasashe irin su Kiribati da Tonga da Vanuatu da dai sauran irin su.
Dr Colin Tukuitonga, na kasar Niuea Kudancin Pacific ya ce tabbas matakin na kasashen ke dauka ya dace.

Har wa yau, wasu kanana kasashen da ba na tsibiri ba ma ba su da cutar ta coronavirus.
Misali har sai a ranar Alhamis ne kasar Malawi da ke yankin Afirka ta Gabas mai yawan jama'a milyan 18 ta fara samun mutum na farko da ya kamu da cutar.
To amma dama tun kafin hakan kasar ta shirya da zarar annobar ta shige ta.
Malwai ta ayyana ta-baci inda ta kulle makarantu da soke bizar shiga kasar, inda yanzu take kokarin fara yi wa jama'arta gwaji domin gano ko suna dauke da coronavirus.
An gano cewa coronavirus za ta ratsa duk wata kasa a duniya. Yanzu abin tambaya a nan shi ne idan ban da Malawi wace kasa ce za ta zama ta karshe da coronavirus za ta kutsa kai?
" Za ta iya yiwuwa wadannan kasashen na tsibiri ne, zan iya yin caca a kan hakan", in ji Andy Tatem, farfesa a fannin yankunan duniya na jami'ar Southampton.
"A zamanin dinkewar duniya wuri guda, ba ni da tabbas cewa akwai wani wuri da cutar ba za ta kutsa ba."
Rufe iyakoki kamar yadda Nauru ta yi - "bai zama lallai hakan ya yi tasiri ba kuma da wuya ya dore."









