An kai wadanda ake zargi da fyade a Indiya kotu

An wallafa
An fitar da mutanen nan biyar da ake zargi da yi wa daliba fyade, tare da hallakata a watan jiya a birnin Delhi na India, daga kotu, bayan sun saurari tuhumar da ake ma su.
Tun farko dai, sai da jami'ai suka maida zaman sauraren shariar daga na bainar jama'a zuwa na bayan fage, bayan da aka fuskanci rudani a kotun.
Rahotanni sun ce biyu daga cikin wadanda ake tuhumar, sun amince su bada shaida a kan sauran , a wani yunkuri na kaucewa hukuncin kisa.
Akwai yiwuwar dai a maida sauraren shari'ar zuwa wata babbar kotu da za ta gaggauta sauraren karar.
Harin da aka kai wa dalibar dai, ya haddasa jerin tarzoma a kasar ta India inda galibi ba a hukunta masu cin zarafin mata.







