Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda Aljeriya ta lashe kofin AFCON

Labarai da bayanai kai-tsaye game da wasan karshe a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka AFCON 2019.

Rahoto kai-tsaye

Umar Rayyan and Umar Mikail

  1. Senegal 0-1 Aljeriya

    Aljeriya ta yi laifi a wannan wasa sau tara sama da Senegal da ta yi biyar.

    Yanzu haka Lamine Gassama ne a kwance bayan Ismael Bannacer ya kai shi kasa.

  2. Senegal 0-1 Aljeriya

    Bugun tazara ne Senegal ta samu bayan an buge Mane a kusa da yadi na 27.

    Kuma an buga M'Bolhi ya kama

  3. Senegal 0-1 Aljeriya

    Zuwa yanzu Senegal ce kan gaba wajen yawan rike kwallo da kashi 53%, inda Aljeriya ke da kashi 46%

  4. Senegal ta samu bugun tazara, Senegal 0-1 Aljeriya

    Senegal ta samu bugun tazara amma Aljeriya ta cire kwallon.

  5. Wasa yana ci gaba da daukar zafi, Seneal 0-1 Aljeriya

    Wasa yana ci gaba da daukar zafi kowa yana kai wa kowa hari akai-akai.

  6. Aljeriya ta samu bugun tazara, Senegal 0-1 Aljeriya

    Aljeriya ta samu bugun tazara amma Senegal ta cire kwallon.

  7. GO, Senegal 0-1 Aljeriya

    Aljeriya ta jefa kwallo a ragar Senegal ta hannun Baghdad Bounedjah ana cikin minti biyu da fara wasa.

  8. Senegal, Senegal 0-0 Aljeriya

    Senegal ta fara kai wa Aljeriya hari

  9. An fara wasa

    An fara wasa tsakanin Senegal da Aljeriya.

  10. Ana shirye-shiryen fara wasa

  11. Mane da Mahrez

  12. Gololin kasashen biyu

    Kokarin gololin kasashen biyu...

  13. Kocin Senegal da Aljeriya duka 'yan Afirka ne

    Duka kocin Senegal da na Aljeriya suna horar da tawagar kasashensu ne. Kuma duk kasar da ta yi nasara ta kafa tarihi ke nan.

  14. Dakin kayan 'yan wasa

  15. Everton ta yi wa Gueye fatan samun nasara

    Ita ma kungiyar Everton ta yi wa dan wasanta Idrissa Gana Gueye wanda dan Senegal ne fatan lashe wannan kofin.

  16. City ta yi wa Mahrez fatan samun nasara

    Haka zalika kungiyar Manchester City Riyad Mahrez ta yi wa Mahrez fatan samun nasara a wasan a shafinta na Twitter.

  17. Liverpool ta yi wa Mane fatan alheri

    Kungiyar da dan wasan Senegal Sadio Mane ke yi wa wasa a Turai, Liverpool, ta yi wa shahararren dan wasan fatan nasara a karawar yau a shafinta na Twitter.

  18. Super Eagles sun koma gida

    'Yan wasan Najeriya sun koma gida a ranar Juma'a.

  19. Najeriya ce ta zo ta uku

    Najeriya ce ta zo ta uku a gasar bayan doke Tunisiya da ci 1-0 a ranar Laraba.

    A karshen makon jiya ne Aljeriya ta doke Najeriya da ci 2-1 a wasan kusa da na karshe.

  20. 'Yan wasan Aljeriya suna tsinka jini