Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda Aljeriya ta lashe kofin AFCON

Labarai da bayanai kai-tsaye game da wasan karshe a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka AFCON 2019.

Rahoto kai-tsaye

Umar Rayyan and Umar Mikail

  1. , Senegal 0-1 Aljeriya

    Mahrez ya bugo bugun tazara zuwa cikin ragar Senegal amma 'yan baya sun cire ta kwana

  2. Sabaly ya kai hari, Senegal 0-1 Aljeriya

    Sabaly ya zabga wa Rais golan Aljeriya kwallo kuma da kyar ya tura ta kwana

  3. Niang ya kai mumunan hari, Senegal 0-1 Aljeriya

    Sai da ya yanke gola ta bangaren dama a cikin yadi na 18 amma saboda ya yi gefe bai iya samun buga ta da kyau ba. Waje ya buga ta

  4. An soke finareti, Senegal 0-1 Aljeriya

    Alkalin wasa ya soke finareti ne bayan da ya duba na'urar VAR.

  5. Finareti, Senegal 0-1 Aljeriya

    Senegal ta samu bugun finareti, amma yanzu lafari ya tafi duba abin da ya faru ta na'uurar VAR

  6. An yi wa Sabaly keta, Senegal 0-1 Aljeriya

    An yi wa Sabaly na Senegal keta kuma an ba Senegal bugun tazara.

  7. 54, Senegal 0-1 Aljeriya

    An bai wa Belali na Aljeriya katin gargadi bayan ya kayar da Gassama na Senegal a gefen dama na gidan Senegal din.

  8. An shigo da kofin gasar filin wasa, Senegal 0-1 Aljeriya

    Tsohon dan Kamaru Samuel Eto ya kawo kofin gasar cikin filin wasan.

  9. Mane ya taba kwallo da hannu, Senegal 0-1 Aljeriya

    Mane ya taba kwallo da hannu alkalin wasa ya hura.

  10. , Senegal 0-1 Aljeriya

  11. An dawo hutun rabin lokaci, Senegal 0-1 Aljeriya

    An ci gaba da wasa. Aljeriya za ta so a tashi a haka ko da ba ta kara kwallo ba domin ta kafa sabon tarihi a harkar kwallonta. Shi kuwa Riyad Mehrez murnarsa ba za ta musaltu ba

  12. Senegal 0-1 Aljeriya, Senegal 0-1 Aljeriya

    Minti 45 kawai ya rage wa Aljeriya kafin su daga kofin Afirka na farko a tarihi.

    Ba su taka wata rawar a zo a gani ba a fallen farko na wannan wasa, amma kwallon da Bounedjah ya ci ita ce ta yanke hukunci.

  13. An tafi hutun rabin lokaci, Senegal 0-1 Aljeriya

  14. Senegal ta kai hari, Senegal 0-1 Aljeriya

    Ismaila Sarr ya kusa cilla kwallo cikin ragar Aljeriya kafin dan bayan Aljeriya ya saka masa matsi.

    'Yan Senegal suna ta kai kuka ga lafari cewa keta aka yi masa saboda haka bugun finareti ne.

  15. An kara minti biyu, Senegal 0-1 Aljeriya

    Alkalin wasa ya kara minti biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

  16. Yadda kasashen biyu suke wasa, Senegal 0-1 Aljeriya

  17. Bugun tazara, Senegal 0-1 Aljeriya

    Henry Saivet na Senegal ne ya bugo kwallo cikin yadi na 18 amma 'yan bayan Aljeriya sun yi namijin kokari sun tsige ta

  18. Senegal ta kai wawan hari, Senegal 0-1 Aljeriya

    M'Baye Niang ne ya dada kwallo daga yadi na 23 da kafarsa ta hagu, kuma saura kadan ta shiga raga. Amma sai dai ta haye ta saman raga

  19. Wasa yana ci gaba da yin zafi, Senegal 0-1 Aljeriya

    Wasa yana ci gaba da yin zafi yayin da Senegal take ci gaba da dannawa don gannin ta farke kwallon da Aljeriya ta jefa mata.

  20. An ba Amir katin gargadi, Senegal 0-1 Aljeriya

    An ba Amir na Aljeriya katin gargadi