Saura minti 15 a tafi hutun rabin lokaci, Liverpool 1-0 Barcelona
Liverpool na ci gaba da kokari amma kwallayen da suke kai wa bakin ragar Barcelona ba wasu masu hadari ba ne.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labarai da sharhi game da yadda Liverpool da Barcelona ke karawa a wasan kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai a filin wasa na Anfield.
Liverpool na ci gaba da kokari amma kwallayen da suke kai wa bakin ragar Barcelona ba wasu masu hadari ba ne.
Robertson ya tsige kwallo mai hadarin gaske zuwa bugun kwana.
Barcelona sun bugo kwana amma babu hadari ga Liverpool
Robertson ya dada kwallon mai zafin gaske. Da kyar da yarfe gumin goshi Stegen ya buge ta.
Liverpool na ci gaba da matsawa kuma da alama suna kokarin samun wani abu a farkon wasan nan
Wasa ya sake daukar zafi, inda Barcelona ta kai wa Liverpool hari amma babu ci.
Messi ya kusa jefa kwallo a ragar Liverpool. Ya yi kokarin yanke Van Dijk amma inaaaa. Van Dijk ya sakace kwallon
Yadda wasan ke gudana bayan minti 15 da farawa.
Messi ya kai harinsa na farko a wasan, kuma da kyar Alisson ya yi wa kwalloin gada zuwa bugun kwana.
An bugo kwanar amma babu wani hadari ga Liverpool
Liverpool sun kama da wuta sosai, inda suke aiki tukuru a 'yan mintunan da aka yi zuwa yanzu.
Liverpool ta zura kwallo a ragar Barcelona a minti na bakwai da fara wasa.
Henderson ne ya shigo da kwallon shi kadai cikin tsakiyar yadi na 18 din Barcelona, inda ya yanke mutum biyu kuma ya buga ta raga. Da kyar Stegen ya kare ta. Nan take kuma Origi ya kara buga ta kuma ta kwanta cikin ragar Barcelona.
Wasa ya fara daukar zafi duka bangarorin sun fara kai wa juna hare-hare, sai dai har yanzu babu ci.
Mane ya jawo kwallo cikin yadi na 18, inda Henderson ya kusa jefa ta cikin ragar Barcelona. da kyar 'yan bayan Barcelona suka fitar da ita bugun kwana.
Wannan shi ne yunkuri na farko a wasan
Wajibi ne Liverpool ta ci 4 a wannan wasa kafin ta samu damar wucewa.
Sau biyar kowanne daga cikin kungiyoyin biyu suka taba lashe kofin gasar.
Ana shirye-shiryen fara wasa a filin wasa na Anfield duka 'yan wasan kungiyoyin biyu suna tsinka jini.
Yau sarki daya ne a cikin fili, kuma ba wata tantama shi ne Messi.
Sai dai daya sarkin na Liverpool Mo Salah yana shawartar abokan wasansa da magoya baya da kada su karaya.
Abin da aka rubuta a rigarsa: "Kada ku sake ku karaya"
Wadannan su ne 'yan wasan da ake sa ran za su fara yi wa Barcelona wasa
Wadannan su ne 'yan wasan da ake sa ran Liverpool za ta fara wasa da su