Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Liverpool ta yi kaca-kaca da Barcelona

Labarai da sharhi game da yadda Liverpool da Barcelona ke karawa a wasan kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai a filin wasa na Anfield.

Rahoto kai-tsaye

  1. Messi ya kai mummunan hari, Liverpool 3-0 Barcelona

    Messi ya kai mummunan hari, amma golan ya cire kwallon.

  2. Messi ya samu bugun tazara, Liverpool 3-0 Barcelona

    Messi ya buga kwallon amma ta daki bango kuma ta tafi kwana

  3. Yanzu ana kunen doki, Liverpool 3-0 Barcelona

    Yanzu haka ana kunen doki tsakanin kungiyoyin biyu 3-3.

  4. Katin gargadi, Liverpool 3-0 Barcelona

    An bai wa Matip katingargadi bayan ya bige Messi a bakin ragarsu

  5. Kan-kan-kan, Liverpool 3-0 Barcelona

    Liverpool sun tasa Barcelona a gaba kuma komai yana taffiya a yadda suke sonsa.

    Ana kan-kan-kan a yanzu

  6. Wasa ya sake daukar sabon salo, Liverpool 3-0 Barcelona

    Wasa ya sake daukar sabon salo, inda Liverpool take ci gaba da danna Barcelona.

  7. An ba Rakitic katin gargadi, Liverpool 3-0 Barcelona

  8. GO Liverpool ta sake jefa kwallo a ragar Barcelona, Liverpool 3-0 Barcelona

    Wijnaldum ne ya yi tsallen gaske a tsakiyar yadi na 18 din Barcelona kuma kunduma ta cikin ragarsu.

    Ya sake jefa kwallon ne a minti na 56.

  9. GO! Liverpool ta sake jefa kwallo a ragar Barcelona, Liverpool 2-0 Barcelona

    Liverpool ta sake jefa kwallo a ragar Barcelona a minti na 54.

    Wijnaldum ne ya shauda ta ga Stegen, inda shi kuma ya kasa tare ta kuma afka cikin raga.

  10. Van Dijk, Liverpool 1-0 Barcelona

    Van Dijk ya kai mumunan hari inda Stegen ya kama ta da kyar.

    Sadio Mane ne ya take kwallon bayan an bugo masa ita. Sagio Roberto ne ya cilla kwallon bugun kwana

  11. Liverpool ta samu kwana, Liverpool 1-0 Barcelona

    Liverpool ta samu bugun kwana, amma 'yan wasan bayan Barcelona sun cire kwallon.

  12. An dawo wasa, Liverpool 1-0 Barcelona

  13. Rawar da kowacce kungiya ta taka a minti 45 na farko, Liverpool 1-0 Barcelona

  14. An tafi hutun rabin lokaci, Liverpool 1-0 Barcelona

  15. Alba, Liverpool 1-0 Barcelona

    Jordi Alba ya buga kwallo ga Alisson kuma ta tsallake shi, amma ya rarrafa ya kamo ta. Mummunan hari ne domin kuwa daga shi sai gola. Allah ya kare Liverpool kawai

  16. Messi, Liverpool 1-0 Barcelona

    Messi ya kusa cilla kwallo ragar Liverpool amma ta yi fadi ta kuma fita bugun gida ga Liverpool

  17. Karin lokaci, Liverpool 1-0 Barcelona

    An kara minti 4 a kan minti 45 na farkon wasa. Nan gaba kadsan kuma za tafi hutun rabin lokaci

  18. Wasa ya dau zafi, Liverpool 1-0 Barcelona

    Yadda wasan ke gudana cikin hotuna.

  19. , Liverpool 1-0 Barcelona

    Shaqiri ya nemi Mane a cikin yadi na 18 din Barcelona amma mai same shi ba

  20. , Liverpool 1-0 Barcelona

    Wannan yakin fa ba na wasa ba ne😲💪