Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai

Real Madrid ta yi nasarar lashe kofin Zakarun Turai karo na uku a jere bayan ta doke Liverpool ci 3-1 a wasan karshe da suka fafata a birnin Kiev na Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau

  1. Real Madrid na harin lashe kofi karo na uku a jere, Liverpool 0-0 Real Madrid

    Real Madrid da ta lashe kofin Zakarun Turai sau 12, a yanzu tana harin lashe kofin gasar ne a karo na uku a jere.

    Bayern Munich ce kungiyar da ta taba lashe kofin sau uku a jere a tsakanin 1974 zuwa 1979 tun kafin a fara kiran gasar Zakarun Turai.

    Kocin Madrid ya ce sun fi Liverpool yunwar kofin duk da nasarorin da suka samu a shekaru biyu a jere.

  2. An fito fili, Real Madrid 0-0 Liverpool

  3. 'Yan wasa na shirin fitowa fili, Real Madrid 0-0 Liverpool

  4. Yadda Mawakiya Dua Lipa ta cashe a filin Kiev, Real Madrid 0-0 Liverpool

  5. An fara bikin kammala gasar

    An fara bikin kammala gasar zakarun Turai ta 2018 kafin soma fafatawa tsakanin Real Madrid da Liverpool a Kiev

  6. Ronaldo ya ci kwallo 105 a wasa 100 a gasar zakarun Turai a Real Madrid

  7. Salah ya ci kwallo 41 a wasa 51 da ya buga wa Liverpool a bana

  8. Yadda Liverpool ta fito atisaye, Real Madrid 0-0 Liverpool

  9. Salah bai dauki Azumi ba, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Liverpool ta tabbatar da cewa Mohamed Salah bai dauki Azumi ba a yau saboda wasansu da Real Madrid.

    Tun da farko an ruwaito dan wasan na Masar zai ci gaba da Azuminsa na Ramadan.

    Amma Likitan Liverpool ya ce Salah ya ajiye azumi a ranar Alhamis da Juma’a da kuma Asabar domin fafatawa da Real Madrid.

    Salah zai ci gaba da Azumi idan an kammala wasan.

  10. 'Yan wasan Real Madrid 11

  11. 'Yan wasan Liverpool 11

  12. 'Yan wasa 11 da za su buga wa Real Madrid

  13. 'Yan wasa 11 da za su buga wa Liverpool, Real Madrid 0-0 Liverpool

  14. Atisayen Real Madrid a Kiev, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Bidiyon yadda Real Madrid ke atisaye, shirin fafatawa da Liverpool

  15. Yadda Real Madrid ta isa filin Olympic na Kiev, Real Madrid 0-0 Liverpool

  16. Barkarmu da wannan lokacin, Real Madrid 0-0 Liverpool

    Jama'a barkanmu da kasance wa da ku a wannan fili inda za mu kawo muku sharhi kan wasan karshe na gasar cin kofin Zakarun Turai.

    Real Madrid da Liverpool za su gwabza inda za a fitar da zakara tsakaninsu.

    A birnin Kiev na Ukraine ake fafatawar.