Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai
Real Madrid ta yi nasarar lashe kofin Zakarun Turai karo na uku a jere bayan ta doke Liverpool ci 3-1 a wasan karshe da suka fafata a birnin Kiev na Ukraine.
Rahoto kai-tsaye
Awwal Ahmad Janyau
An sako Lallana, Real Madrid 0-0 Liverpool
Lallana ya canji Salah
Salah ya ji rauni an fitar da shi, Real Madrid 0-0 Liverpool
Ya fita fili yana kuka
Sau biyar Klopp na shan kashi a wasannin karshe
Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya sha kashi a wasannin karshe na muhimman gasa shida ciki har da wasan karshe na zakarun Turai biyu.
A karon farko dai Klopp yana tare ne da Borussia Dortmund, a lokacin da suka sha kaye a hannun Bayern Munich a wasan karshe na gasar zakarun Turai ta shekarar 2013 da aka buga a filin wasa na Wembley, yayin da na biyun ya zo a lokacin da Liverpool ta sha kaye a hannun Sevilla a wasan karshe na gasar Europa.
Idan Liverpool ta sha kaye a yau, Klopp zai zama koci na hudu - bayan Max Allegri (a shekarar 2015 da 2017), Diego Simeone (shekarar 2014 da 2016) da kuma Hector Cuper (shekarar 2000 da 2001) - da suka fuskanci irin wannan rashin nasarar a wasanni karshe na gasar zakarun Turai.
Sai dai kuma kungiysar ba ta da irin wannan mummunar tarihin. Babu wani dan wasan da ya buga wa Liverpool a wannan kakar da ya taba buga wasan karshe a gasar zakarun Turai, sabanin 'yan kungiyar Real Madrid, inda takwas daga cikinsu ke fatan cin kofin a karo na hudu.
Ramos ya yi wa Salah keta, Real Madrid 0-0 Liverpool
Salah ya fadi ana duba lafiyarsa bayan Ramos ya ma sa mugunyar keta
Liverpool na taba Madrid, Real Madrid 0-0 Liverpool
Liverpool sun fara da karfinsu. Ko za su daure a haka?
Liverpool ta kai hari amma golan Madrid ya kame kwallon, Real Madrid 0-0 Liverpool
Kofin Zakarun Turai na biyar Ronaldo ke hari, Real Madrid 0-0 Liverpool
Ronaldo na harin lashe kofin zakarun Turai na biyar, tarihin da ‘yan wasa hudu kawai suka taba kafawa
Dan wasan ne kuma ya fi yawan cin kallaye a gasar a bana inda ya ci 15.
Sau shida a jere ke nan Ronaldo ya fi kowa cin kwallo a raga a gasar Zakarun Turai.
Ronaldo ya sauya wuri, Real Madrid 0-0 Liverpool
Ronaldo ya koma gefen dama bayan ya fara a gefen hagu
Ronaldo ya kai hari, Real Madrid 0-0 Liverpool
Amma ya dirka kwallon saman ragar Liverpool
Haduwa ta biyu tun 1981, Real Madrid 0-0 Liverpool
Karo na biyu ke nan da Real Madrid ta hadu da Liverpool tun 1981 a Paris da Madrid ta yi nasara da ci 1-0
Real Madrid ta koma tsaron gida, Real Madrid 0-0 Liverpool
‘Kwarewar Madrid a gasar ba komi ba ne’, Real Madrid 0-0 Liverpool
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce lashe kofin zakarun Turai abu ne da ke jinin Liverpool. A cewarsa, duk da Madrid ta goge a gasar, hakan ba zai razana ‘yan wasan shi ba.
Klopp ya taba jagorantar Borussia Dortmund wasan karshe a gasar zakarun Turai a 2013 amma ya sha kashi a hannun Bayern Munich.
Liverpool ta matsawa Real Madrid, Real Madrid 0-0 Liverpool
Liverpool na son ta yi gaggawar zura kwallo
Modric ya tare kwallon da Salah ya buga a gidan Madrid
Ramos ya yi wa Salah keta, Real Madrid 0-0 Liverpool
An fara wasa da zafi, Real Madrid 0-0 Liverpool
Liverpool ta kai kora biyu a gidan Madrid.
Real ta kai hari, Real Madrid 0-0 Liverpool
Ronaldo ya kai kora amma Isco ya yi satar gida
Andriy Shevchenko ne ya gabatar da kofi a fili kafin soma wasan
An fara wasa, Real Madrid 0-0 Liverpool