Sai wani lokacin, Real Madrid 3-1 Liverpool
A nan muka kawo karshe sharhin da muke kawo mu ku kai-tsaye.
Za mu sake haduwa a gasar cin kofin duniya.
Muna taya magoya bayan Real Madrid murna kamar yadda muke taya magoya bayan Liverpool bakin ciki.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta yi nasarar lashe kofin Zakarun Turai karo na uku a jere bayan ta doke Liverpool ci 3-1 a wasan karshe da suka fafata a birnin Kiev na Ukraine.
Awwal Ahmad Janyau
A nan muka kawo karshe sharhin da muke kawo mu ku kai-tsaye.
Za mu sake haduwa a gasar cin kofin duniya.
Muna taya magoya bayan Real Madrid murna kamar yadda muke taya magoya bayan Liverpool bakin ciki.
Jerin shekarun da Real Madrid ta lashe kofin gasar Zakarun Turai
Sergio Ramos ya daga kofin da Real Madrid da ta lashe karo na 13 a gasar Zakarun Turai. Kofi na uku a jere.
Jurgen Klopp ya fi kowa bakin ciki bayan buga wasannin karshe sau 6 ana doke shi
Sau biyu a gasar Zakarun Turai, sannan a 2016 ya sha kashi hannun Sevilla a Europa League
Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai karo na uku a jere
Saura kiris ta kai kafar Ronaldo ya jefa ta raga amma Dijk ya kabe
Asensio ya canji Benzema
Shigowar Gareth Bale bayan dawo wa hutun rabin lokaci ya yi tasiri ga samun nasarar Real Madrid
Daga nesa Bale ya dirko kwallon sai a ragar Liverpool