Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Sarki Charles lll ya gana da shugabannin Commonwealth a Fadar Buckingham

Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Ingila.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Halima Umar Saleh, Abdullahi Bello Diginza and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Masu Alhini na ci gaba ajiye furanni a wurare daban-daban a fadin duniya

    Mutane da dama a fadin duniya na ci gaba da bayyana jimamin rasuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta hanyar ajiye furanni tare mika sakonnin jaje a ofisoshin jakadancin Burtaniya.

  2. Ƙasashe rainon Ingila na Commonwealth sun bayyana godiyarsu ga Sarauniya

    Sarauniya dai ta kasance mai nuna sha'awarta ga Commonwealth - ƙungiyar da ke ƙunshe da ƙasashe 50 da suka fito daga Daular Burtaniya.

    Shugabannin ƙasashen ƙungiyar sun bayyana godiyarsu ga jajircewarta da ƙoƙarinta.

    Firaministan Indiya, Narendra Modi ya ce ana matuƙar girmamata saboda nutsuwarta.

    Gwamnatin Jamaica ta sanar da yin ƙasa-ƙasa da tutocinta a duk gine-ginen gwamnati tsawon kwana 12.

    Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya ce ƙwazonta abu ne na koyi ga duniya baki ɗaya.

    Shi kuwa Firaministan Australia Anthony Albanese ya yaba wa Sarauniyar saboda yadda ta shafe rayuwarta bisa hidimtawa al'umma da iyalinta da kuma addinta.

    Ya ce wannan babban rashi ne da ya taba zukatanmu a Australiya, marigayiya Elizabeth ita kadai ce Sarauniyar da akasarinmu muka sani, kuma sarauniyar da ita kadai ta taba zuwa Australiya.

  3. Babban ɗan Sarauniya, Charles ya ce mutuwar mahaifiyarsa abin baƙin ciki ne gare shi

    A yau ne babban ɗan Sarauniya, Charles zai koma birnin London daga Balmoral inda za a ayyana shi a matsayin Sarki a hukumance a Fadar Saint James.

    An tabbatar za a riƙa kiran shi a matsayin Sarki Charles na uku wato King Charles the Third.

    Cikin wata sanarwa, magajin Sarauniyar ya ce mutuwar mahaifiyarsa abin baƙin ciki ne gare shi da kuma iyalin masarautar.

  4. Shugaba Buhari ya ji baƙin cikin rasuwar Sarauniyar Ingila

    A saƙonsa na jimami da alhinin rasuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya ji baƙin ciki matuka da samun labarin mutuwar Sarauniyar.

    Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar jiya Alhamis.

    "Ni da iyalaina da al'ummar Najeriya sama da miliyan 200 duk mun ji takaici sosai na rasuwar Sarauniya Elizabeth, wanda hakan ya kawo ƙarshen mulkinta na tsawon shekara 70 mai cike da ban sha'awa da babu irin sa.

    “Mulkin marigayiyar shi ne kadai masarauta mai girma a Turai da kashi 90 cikin 100 na al'ummar duniya a yau da suka sani.”

    Ya ƙara da cewa “a daidai wannan lokaci na jimami mun bi sahun sauran ƙasashen duniya wajen alhinin rashin Sarauniya Elizabeth.

    "Muna miƙa ta’aziyyarmu ga illahirin iyalan masarautar da mutanen ƙasar Birtaniya da ma ɗaukacin ƙasashe Rainon Ingila na (Commonwealth).”

    Shugaba Buhari ya ce tarihin Najeriya a matsayin ƙasa ba zai taɓa kammaluwa ba, ba tare da an taɓo babin Sarauniya Elizabeth ta biyu ba, shugabar da zamto tamkar wata bango ga ƙasashen duniya ta kuma yi fice da shahara.

    “Ta sadaukar da rayuwarta wajen gina ƙasarta da ƙasashe rainon Ingila da ma ƙoƙarin tabbatar da duniya ta zama waje mai kyau", sanarwar ta ƙara da cewa.

    Shugaba Buhari ya yi maraba da Mai Girma Yarima Charles bisa gadon mulkin da ya yi, ya kuma yi addu'ar ganin ci gaba da samun ƙarin ingantuwar dangantaka da alaƙa tsakanin ƙasashen biyu a yayin mulkin Yarima Charles na III.

  5. Ƙasashen duniya na ci gaba da alhinin rasuwar Saruniyar Ingila

    Ƙasashen duniya da dama na ci gaba da bayyana alhini da jimami na rasuwar Sarauniya Elizabeth da ta fi daɗewa kan karaga a Burtaniya.

    Ta rasu ne jiya Alhamis tana da shekara 96. An yi ƙasa-ƙasa da tutoci a Amurka yayin da Shugaba Joe Biden ya bayyana marigayiyar a matsayin mai kishin ƙasa da tsayuwar daka.

    Cikin dare kuma, an kashe fitilu a Hasumiyar Eiffel da ke Paris. Shugaba Macron ya ce zai tuna da ita a matsayin ƙawar Faransa.

    Shi ma Shugaban Jamus yana bayyana Sarauniyar a matsayin wadda ta ba da gudummowa a wannan ƙarni.

    Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya ce ta kasance mai mutunta al'ummarta.

    Shi kuwa Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce mutuwar Sarauniya Elizabeth gagarumin rashi ne ga duniya baki ɗaya.

  6. Buɗewa

    Masu bin wannan shafi na BBC Hausa assalamu alaikum, barkanmu da safiyar Juma'a.

    Kamar yadda kuka sani dai a jiya Alhamis ne Fadar Buckingham ta Birtaniya ta sanar da rasuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth II, tana mai cewa Sarauniyar ta rasu ne salin-alin a gidanta da ke Balmoral.

    A yau wannan shafi da zai mayar da hankali ne kacokan wajen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniyar.

    Sai ku kasance da mu.