An buɗe ƙofar shiga Fadar Balmoral
An buɗe ƙofar shiga Fadar Balmoral inda ake jira a fito da gawar Sarauniya.
Ta rasu ne salin alin a cikin Fadar ta Balmoral a ranar Alhamis.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Ingila.
Mustapha Musa Kaita, Halima Umar Saleh, Abdullahi Bello Diginza and Nasidi Adamu Yahaya
An buɗe ƙofar shiga Fadar Balmoral inda ake jira a fito da gawar Sarauniya.
Ta rasu ne salin alin a cikin Fadar ta Balmoral a ranar Alhamis.
Dubban mutane ne ake sa ran za su kafa layi a hanyar da za a bi da akwatin gawar Sarauniya Elizabeth a yau Lahadi.
Za a tafi da gawar tun daga Fadar Balmoral zuwa Edinburgh babban birnin Scotland.
Da misalin ƙarfe 10:00 na safe ne za a soma tafiya da gawar.
Coci-coci a Birtaniya za su gudanar da addu'o'i a yau Lahadi ga Sarauniya Elizabeth II.
Babbar Cocin Ingila ta ba Ikklesiyi shawarwari na musamman kan yadda za a gudanar da addu'o'in a tsawon lokacin makokin.
Cocin Ingila ta buƙaci sauran coci-coci da su kaɗa ƙaraurawa da kuma gudanar da addu'o'i na musamman bayan rasuwar sarauniyar a ranar Alhamis.
Sarauniya Elizabeth ta kasance garkuwa ga Cocin Ingila kuma ko a lokacin da taka raye ta bayyana cewa addininta wani babban sashe ne na rayuwarta, haka shi ma Sarki Charles III ya bayyana yadda addini ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarsa.
Tun bayan rasuwar Sarauniyar Ingila, ana ta makoki a ƙasashe da dama na duniya kuma daga ciki har da Indiya.
A ƙasar ta India, an sassauto da tutoci ƙasa-ƙasa sa'annan an soke gudanar da duk wani taro na nishaɗi a hukumance inda za a shafe kwana guda ana zaman makoki.
Sai dai an samu mabanbanta ra'ayi game da matakin inda wasu Indiyawa ke neman sanin dalilin da ya sa ake karramar sarauniyar da ƙasarta ta yi mulkin mallaka.
Amma jagororin siyasa sun furta kalaman yabo kan marigayiyar. Firaiministan India Narendra Modi ya bayyana ta a matsayin mace mai jajircewa.
Shugabar Jam'iyyar Congress, mai hamayya Sonia Gandhi ta bayyana marigayiyar a matsayin mace ce mai kwarjini.
Nan da ƴan sa'oi kaɗan ne gawar Sarauniya Elizabeth za ta bar Fadar Balmoral inda ta rasu.
Ana sa ran za a soma farko bi da akwatin gawar ta ƙauyukan da ke yankin Royal Deeside sai Aberdeen zuwa Dundee sa'annan Edinburgh inda akwatin zai kasance a Fadar Holyroodhouse.
Ƴar marigayiyar Gimbiya Anne za ta yi wa akwatin gawar rakiya daga Balmoral zuwa Edinburgh ɗin.
Dubban mutane ake sa ran za su yi dafifi kan hanyar. Akwatin wanda aka yi wa ado bisa tsarin masarautar Scotland zai ci gaba da zama a Edinburgh har zuwa ranar Talata kafin a tafi da shi birnin London.
Za kuma a yi jana'izar sarauniya Elizabeth ne ranar 19 ga watan Satumba.
Jama'a barkanmu da safiyar Lahadi, 11 ga watan Satumbar 2022. A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni musamman kan abubuwan da ke faruwa game da shirye-shiryen jana'izar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II wadda ta rasu a ranar Alhamis.
Haka kuma za mu ɗan rinƙa tsakuro maku wasu labaran da ke faruwa a wasu sassan duniya.
Masu bibiyarmu a wannan shafi nan muka kawo karshen labarai da rahotanni kan rasuwa da makokin da ake ciki na rasuwar Sarauniya Elizabeth ta II.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa da wasu sabbin rahotannin, da halin da ake ciki a Birtaniya, da sauran kasashe.
Abdullahi Bello Diginza ke muku fatan alkhairi.
Mun gode.
A yanzu haka gawar Sarauniyar na fadarta da ke Balmoral a yankin Scotland inda a nan ne ta rasu.
Nan gaba ne kuma za a dauko gawar zuwa birnin Landan gabanin jana'izar kasa da za a yi mata ranar Litinin 19 ga watan Satumba.
A daidai wannan lokaci da kasar ke cikin jimami, za a bai wa mutanen kasar damar nuna girmamawa ga Sarauniyar a yayin da za a ajiye gawarta a fadarta da ke Edinburgh, kafin a wuce da ita zuwa birnin Landan.
A gobe ne dai za a dauko gawar Sarauniyar daga fadar Balmoral, inda za a yi tafiyar sa'a shida da ita cikin tsanaki zuwa Edinburgh.
Za a kai gawar Sarauniyar fadar Holyroodhouse, wato gidan sarautar Birtaniya wanda ke Edinburgh, babban birnin yankin Scotland.
Sannan kuma a ranar Litinin za a kai gawar zuwa majami'ar St Giles' inda sabon Sarki tare da sauran danginta za su kasance tare da ita
Sarki Charles ya koma gidansa na 'Clarence House' bayan shafe wunin yau yana gabatar da al'amura daban-daban.
Tun da farko dai da safiyar yau ne majalisar da ke nadin sarki ta ayyana shi a matsayin sabon sarki a hukumance, sannan kuma ya gabatar da jawabi tare da ganawa da jama'a da dama a fadar Buckingham.
Sabon Sarkin ya tsaya a wajen gidan nasa, domin gaisawa da dimbin jama'ar da ke dakon isowarsa.
Sarki charles lll ya fice daga fadar Buckingham, yayin da cincirindon jama'a ke tseye a kofar fadar domin yi masa fatan alkairi
Tuni dai sarkin tare da matarsa suka gana da Firaminista Liz Truss tare da wasu ministocin kasar.
Haka kuma sun gana da shugabannin jam'iyyun hamayya, wadanda suka hadar da shugaban jam'iyyar Labour Sir Keir Starmer
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa a ranakun Lahadi da Litinin za a sauko da tutoci a fadin kasar, da kuma a ofisoshin jakadancin kasashen waje domin nuna girmamawa ga Sarauniyar Ingila Elizabeth II wacce ta rasu a ranar Alhamis.
A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar ta fitar, ta ce Sarauniyar ta ''Nuna kwazo a tsawon lokacin da ta shafe a kan karagar mulkin Birtaniya, kuma shugabar Kungiyar Kasashe Rainon Ingila''
''Haka kuma ta nuna jajircewa wajen wanzuwar zaman lafiya da hadin kai tsakanin kasashe'' in ji sanarwar.
Tuni dai gwamnatin Najeriya ta mika sakon ta'aziyyarta tana mai cewa Birtaniya da Najeriya sun kasance cikin kyakkyawar dangantaka karkashin mulkin Sarauniyar.
Najeriya ce dai kasa mafi girma a Afirka da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka.
Kwanaki kafin jana'izar mahaifiyarsa, Sarki Charles III tare da matarsa Camilla, za su kai ziyara zuwa yankunan Scotland da Ireland ta arewa da kuma Wales
Wuri na farko da za su fara ziyarta shi ne Scotland, inda za su halarci bikin tunawa da Sarauniyar da za a yi a majalisar dokokin kasar.
Ranar Talata kuma Sarkin tare da matarsa za su je Ireland ta arewa domin ziyartar fadar Hillsborough.
Za su kuma halarci taron addu'o'in da za a yi wa Sarauniya tare da karbar sakonnin ta'aziyya da shugaban majalisar dokokin Ireland ta arewa zai jagoranta.
Bayan sun dawo Landan domin tarbar gawar Sarauniya, ranar Juma'a kuma ma'auratan za su tafi zuwa Wales a ci gaba da ran-gadin da suke yi
Fadar Buckingham ta tsayar da ranar Litinin 19 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a yi wa Sarauniya jana'iza.
Sanarwar ta ci gaba da cewa za a yi jana'izar ne a Westminster Abbey da ke birnin Landan.
A wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram Yarima William ya ce a yayin da duniya ta yi rashin shugaba, ''Ni kuma na rasa kaka''
''Dama na sani dole wannan rana za ta zo'' yana mai ishara ga mutuwar Sarauniya
''Hakika zan dauki lokaci kafin na saba da rayuwa ba tare da kakata ba''
''Zan martaba ta, ta hanyar bai wa mahaifina duk wani taimako da yake bukata ta kowanne fanni a matsayinsa na Sarki''
Wata tsohuwa mai suna Shirley Boehly ta halarci fadar Buckingham domin nuna alhininta game da rasuwar Saruniya.
Tsohuwar mai shekara 88, ta san tsawon shekaru 70 da Sarauniyar ta dauka tana mulki
Ta bayyana cewa Sarauniya ta yi mata komai, kuma ba za a taba samun irinta ba.
Ta ci gaba da cewa ''Na san ta tsawon mulkinta, wannan dama ce a gareni na kasancewa a nan, domin bayyana irin radadin da mutanen kasarmu ke ji''
Shirley ta kara da cewa Sarki Charles lll, zai kasance sarki mai farin jini, tana mai cewa jawabin da ya yi jiya ya sanya ta kuka.
Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya shaida wa BBC cewa marigayiya Sarauniya Elizabeth ta bayar da gagarumar gudunmuwa ga Ƙungiyar Ƙasashe Rainon Ingila, wato Commonwealth.
Jama'a da dama na ci gaba da taruwa a wajen Fadar Balmoral domin ta'aziyya.
A fadar ne Sarauniya Elizabeth II ta rasu salin alin, a lokacin da take tare da iyalanta a ranar Alhamis.
A wurin ne kuma ta shafe hutun da ta yi da dama a tsawon rayuwarta.
Akwatin gawar sarauniyar zai bar Fadar Balmoral nan da kwanaki kaɗan zuwa Edinburgh.
Masu zuwa ta'aziyya kuma na ci gaba da ajiye furanni a gaban kofar shiga fadar.
Manyan Ƴan Majalisar Birtaniya ciki har da Firaiminista Liz Truss sun yi mubaya'a ga Sabon Sarki Charles III a wani zama na musamman da majalisar ƙasar ta yi.
Kakakin Majalisar Wakilan Birtaniya Lindsay Hoyle shi ne ya buɗe zaman bayan yin mubaya'a, bayan nan sai kuma Sir Peter Bottomley, wanda shi ne ɗan majalisa da ya fi daɗewa a majalisar.
Hoyle ya bayyana cewa sakamakon ƙarancin lokaci, ƴan majalisa ƙalilan ne kawai za su iya yin mubaya'ar.
Truss na daga cikin waɗanda suka yi mubaya'ar inda suka rantse cewa za su yi biyayya ga sabon sarki Charles III da magadansa kamar yadda doka ta tanada.
A yayin da aka naɗa Sarki Charles III a matsayin Sabon Sarkin Ingila, akwai tsofaffin Firaiministocin Birtaniya shida da suka halarci naɗin.
Sun haɗa da Sir John Major da Theresa May da David Cameron da Boris Johnson da Gordon Brown da Sir Tony Blair.