Abin da ya faru yau - da kuma abin da ake sa ran zai faru
Idan yanzu kuka shigo wannan shafin, ga takaitaccen bayani game da abubuwan da suka faru a yau zuwa wannan lokaci.
- Kararrawa ta kada a cocin St Paul's, da Windsor, da Westminster Abbey, an kuma harba bindigar ban-girma a daukacin kasar ga Sarauniya Elizabeth ta II
- Sarki Charles na III ya koma birnin Landan daga Aberdeen, inda ya gaisa da dubban mutane a wajen Fadar Buckingham
- Ya kuma gana da Firaiminista Liz Truss a Fadar Buckingham, kuma ita ce ta farko da ya fara ganawa da ita
Abubuwan da za su faru nan gaba a yau:
- Sabon Sarki zai yi wa al'ummar Birtaniya jawabi da karfe shida na yamma agogon kasar
- A daidai lokacin, za a gudanar da addu'o'i na musamman ga marigayi Sarauniya Elizabeth ta II a cocin St Paul a Landan
- Mahalarta zaman addu'o'in za su rera wakar ''Allah ya ja zamanin Sarki'' a hukumance. Za kuma a rera taken Birtaniya a kuma sauya kalamar ''Sarauniya'', zuwa kalamar ''Sarki'', a kuma sauya kalmar ''Nasara sarauniya'', zuwa kalmar ''nasara ga Sarki''.
Ranar Asabar
- Charles zai zama Sarki a hukumance
- Za a dawo da tutocin Birtaniya kamar yadda suke a baya, na kwana guda. Karfe 1 na rana kuma za a yi wani biki, kuma daga bisani a mayar da su rabi.