Sarki Charles III ya ce dansa Yarima William zai gaji sarautarsa ta Yariman Wales.
A jawabin da ya gabatar ga 'yan kasa a karon farko bayan rasuwar Sarauniya Elizabeth.
"A matsayinsa na magajina, a yanzu William zai gaji sarautar da na bari ta Scotland, wadda nake alfahari da ita," in ji shi.
"Zai gaji sarautata ta Duke din Cornwall, zai fara aiki karkashin sarautar da nake kanta sama da shekaru 50.
"A yau, Ina alfahari da zan mika wa dana sarautar Yariman Wales, wadda ta kasance daya daga cikin abubuwan da nake alfahari da su.
"Na tabbatar kasancewar mai dakinsa Catherine tare da shi, Sabon Yarima da Gimbiyar Wales za su ci gaba da gudanar da ayyukan bai wa matasa gwiwa da tattauna batutuwan da suka shafi kasa."
Mai dakinsa Catherineza ta zama Gimbiyar Wales ta farko tun bayan rasuwar mahaifiyar William Gimbiya Diana a shekarar 1997.
Bisa al’adar Yariman yankin Wales ne kadai ke sarautar, amma bayan Sarki Edward I ya mamaye Wales a karni na 13, babban dansa ya fara sarautar Yariman Wales a wani biki da da aka yi Fadar Caernarfon.
Tun daga lokacin yawancin Sarakunan Birtaniya, suka fara bai wa manyan 'ya'yansu da za su gaji wannan sarauta ta Wales. Hakan ta kasance ga Sarauniya Elizabeth ta II, tana da danta Yarima Charles, matarsa kuma ta zama Gimbiyar Wales a shekarar 1969, wadda aka haskawa miliyoyin mutane ta gidan talbijin.