Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Atiku ya fi karfin Tinubu, in ji PDP

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Umar Mikail, Umaymah Sani Abdulmumin, Halima Umar Saleh and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Jami'an EFCC sun halara a Eagles Square

    Jami'an EFCC sun yi balaguro zuwa dandalin Eagles Square domin ganin cewa ba a a 'sayi' daliget ba.

    Sun hallara a wurin ne domin ganin cewa komai ya tafi daidai a zaɓen fitar da gwani na Shugaban ƙasa a Jam'iyyar APC

  2. Sojojin Kamaru sun kashe jaririya da wasu farar-hula takwas

    Rundunar sojin Kamaru ta tabbatar da cewa dakarunta sun kashe wata jaririya 'yar wata 18 a yankin arewa maso yammacin kasar.

    Kakakin rundunar sojin, Cyrille Atonfack, ya bayyana haka a wani sako da ya aike wa manema labarai.

    Ya ce baya ga jaririyar, sojojin sun kashe farar-hula takwas a wani yanayi da ya bayyana a matsayin "abin takaici."

    Rundunar sojin ta kara da cewa an jikkata wata jaririya 'yar wata 12 tana mai cewa ta kaddamar da bincike kan lamarin.

    Lamarin ya faru ne ranar 1 ga watan Yuni yayin da sojoji suke neman wani abokin aikinsu da ya bata a yankin.

    Kyaftin Cyrille Atonfack ya kara da cewa sojojin bakwai sun fuskanci turjiya daga wurin mutanen garin don haka ne suka yi amfani da makamansu ta hanyar da "ba ta dace ba."

  3. Daliget sun soma hallara a filin taron fitar da gwani na APC

  4. Bidiyon shirye-shiryen zaɓen fitar da gwani na APC

  5. Mu ba mu ga amfanin tallafin mai ba - CAJA

    Ƙarancin man fetur na cikin manyan matsalolin da suke addabar al`umma a sassa Najeriya.

    Mahukunta dai na ikirarin kashe makudan kudade da sunan ba da tallafi.

    Amma `yan kasar na cewa ba su ga man ba, kuma ba su san inda tallafin yake shiga ba, sakamakon yadda ake sayar da man a farashi mai tsadar gaske, sabanin naira 165 da gwamnati ta kayyade.

    Masu abin hawa da dama na rayuwa cikin fargaba saboda karancin man fetur, ya na nema ya gagari al`umma, duk kuwa da dimbin kudaden da gwamnati ke ikirarin kashewa a kan tallafin mai wanda tun ana maganar miliyoyin naira, yanzu ya kai matakin tiriliyon.

    A saurari rahoton da Ibrahim Isa ya hada.

  6. Muhimman abubuwa huɗu da za su faru a wajen taron fitar da gwani na APC

    A yayin da APC ta ɗau harama a zaɓen fitar da gwaninta na mutumin da zai tsaya takara a inuwar jam'iyyarta, ga wasu muhimman abubuwa da ake saran su faru a wajen taron.

    Tantace Daliget

    Da misalin karfe 10 na safe har zuwa 1 na rana ake soma tantace masu jefa kuri'a a wannan zaɓe da suka fito daga sassa daban-daban na Najeriya. Wadannan daliget su za su yanke hukunci da zaɓo mutumin da zai tsaya da tikitin APC a zaɓen 2023.

    Jawaban 'yan takara

    Da misalin karfe 4:45 na yamma zuwa 5:45 ake sa ran 'yan takarar da za su fafata a zaɓen su gabatar da jawabai a wajen taron. Jawaban nasu ana saran ya kasancewa kunshe da batutuwan da za su iya jan hankali masu zaɓe da kuma al'ummar kasa.

    Kaɗa ƙuri'a

    Za a shafe kusan sa'a uku ana kaɗa kuri'a tsakanin daliget sama da dubu biyu. Da misalin 6:00 na yamma zuwa 9:00 na dare.

    Sannan za a shafe sa'a 1 wajen kidaya kuri'a. Da misalin 9 zuwa 10 na dare.

    Jawabin wanda ya yi nasara

    Wannan kusan shi ne abu na ƙarshe da ake saran duk mutumin da ya yi nasara zai gabatar da zaran an kammala kidaya kuri'a da sanar da sunnan wanda ya yi nasara.

    Ana dai sa ran duk wanda ya yi nasara ya gabatar da wannan jawabi da misalin karfe 10 na dare.

    Zuwa 11 na dare dai ake saran karkare taro. Sannan 'yan kasa su kuma jiran babban zaɓe a 2023.

  7. Amurka ta gargadi Koriya ta Arewa kan gwajin makamin nukiliya

    Wani babban jami'in diflomasiyyar Amurka ya ce za a mayar da martani cikin gaggawa da karfin gaske, idan Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamin nukiliya.

    Mataimakiyar sakataren harkokin wajen kasar, Wendy Sherman, ta ce tana sa ran duniya baki daya za ta mayar da martani a matsayin tsnitsiya madaurinki daya.

    Tana magana ne bayan wata ganawa da takwararta ta Koriya ta Kudu a birnin Seoul.

    Bayanai sun nuna Koriya Ta Arewa na take-taken yin gwajin makamin nukiliya na farko tun bayan wanda ta yi shekaru biyar da suka gabata.

    A jiya litinin, shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ya yi gargadin cewa Pyanyong din na kara fadada cibiyoyinta na Nukiliya.

  8. An soma tantace daliget a zaben fitar da gwanin APC

    An soma tantace daliget-daliget da za su kaɗa kuri'a a zaɓen fitar da gwani na neman tikitin takara a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

    Sama da daliget dubu biyu ne za a tantace domin zabo mutumin da zai fafata da ɗan takarar jam'iyyar adawa ta PDP a zaben 2023 da ke tafe.

    Za a gudanar da zaɓen ne a dandalin Eagles square kuma kusan an kammala duk wasu shirye-shirye.

    An tsaurara matakan tsaro, sannan an sauya fasalin wajen taron.

    Mutum 23 ne suka nuna sha'awarsu ta takara a karkashin inuwar APC.

    Fitattu a cikinsu akwai, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan.

  9. Ana ta ce-ce-ku-ce kan makomar Firaiministan Burtaniya Boris Johnson

    Ana ta ce-ce-ku-ce a kan makomar firaiministan Buritaniya, Boris Johnson duk da tsallake rijiya da baya a kuri'ar yanke kauna da gwamnatinsa.

    Mista Johnson ya ce ko ba komai a yanzu abubuwa za su ci gaba da tafiya, yana mai bayyana sakamakon kuri'ar a matsayin mai gamsarwa.

    Shugaban 'yan adawa Keir Starmer ya ce al'ummar Buritaniya sun gaji da firaministan da ko kusa bai cancanci hawa mukamin da ya ke kai ba.

    Boris Johnson bai taba amincewa da shan kayi ba, amma gaskiyar ita ce kashi 40 na 'yan majalisar jam'iyyyarsa na da ra'ayin cewa komai zai fi tafiya dai-dai ba tare da shi a matsayin firaiminista ba.

    Wajen jama'a ma goyon bayan da Mista Johnson na ci gaba da raguwa tun bayan fara aiwatar da bincike a kan zargin da ake yi masa na saba dokar hana yaduwar korona.

  10. Gwamnonin Arewa sun gabatarwa Buhari sunayen mutum biyar daga kudu domin ba su takara

    Gwamonin Arewa na jam'iyyar APC sun gabatarwa shugaba Buhari sunayen mutane biyar da suke son a yi maslaha domin bai wa ɗaya daga cikinsu takara, a cewar jaridar Punch ta Najeriya.

    Jaridar ta ce mutum biyar da gwamnonin suka gabatar da sunayensu duk 'yan kudu ne da suka hada da tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Kayode Fayemi na Ekiti da Rotimi Amaechi sai gwamnan Ebonyi, Dave Umahi.

    Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan Filato, Simon Lalong, wanda ya tabbatar da wannan mataki nasu, ya ce sun gabatar da sunayen ne bayan dogon nazari da kuma tsallake tantacewa.

    Sai dai gwamnan ya ce, wannan ba yana nufin za yi tasiri ko hana sauran masu nemana takara su shiga a fafata da su ba.

    Ko a Jiya Litinin sai da gwamnonin suka yi ta ganawa da Shugaba Buhari domin cimma matsayar maslaha domin bai wa kudu takara.

  11. Rahoto kan rarrabuwar kawuna a APC gabanin soma zaɓen fitar da ɗan takararta

  12. Sojojin da ke mulki a Mali sun ce ba za su miƙa mulki ba a yanzu

    Shugabannin sojojin da ke rike da mulki a Mali, sun tabbatar da cewa ba za su mika mulki ga farar hula ba har nan da shekaru biyu.

    Shugaban rikon kwaryar kasar, Kanar Assimi Goita, ya rattaba hannu kan gyaran da aka yi wa wata doka da ke kayyade tsawon lokacin mika mulkin da aka dauka tun da fari.

    Da farko dai sojojin da suka kwace mulki a 2020, sun yi alkawarin mayar da mulki hannun farar hula amma daga bisani suka ci gaba da kankane madafun iko.

    Sai dai suna fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan su gudanar da zabe nan ba da dadewa ba.

  13. Rufe manyan tituna a birnin Abuja saboda zaɓen fitar da gwanin APC ya haifar da cunkoso

    Rufe manyan tituna a birnin Abuja saboda zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC ya haifar da cunkoson ababen hawa da jefa mutane cikin yanayi na wahala kafin isa wuraren aikinsu da kasuwanci.

    Duk da cewa a dandalin Eagle Square za a gudanar da zaɓen, 'yan sanda sun rufe wasu tituna tun a jiya Litinin.

    Tituna da aka rufe sun hada da titin Goodluck Ebele Jonathan ta wajen Court of Appeal, sai titin da ya kasance mahaɗa daga ginin Ecowas zuwa Ma'aikatar Mata zuwa Ma'aikatar Kuɗi da Harkokin Waje.

    Akwai kuma titin Kur Mohammed da ta wajen Babban Masallaci birnin da Benue Plaza.

    Sauran sun hada da Nitel Junction da Phase 3 da NNPC Towers da gadar Ceddi Plaza, titin Gana ta wajen Transcorp.

    Sai kuma titin Hedikwatar DSS Phase 1 da aka rufe da titin ginin majalisa, Bullet da Bayelsa House.

  14. Masu neman takara a APC na zaryar masaukin daliget gabanin zaɓen fitar da gwani

    Rahotanni daga jaridun Najeriya na cewa masu neman takara a jam'iyyar APC na zarya a otel-otel din da aka sauke daliget domin ganawa da su gabannin soma jefa kuri'a a wannan Talatar a Abuja.

    Cikin 'yan takarar da aka ambato na tuntuɓar daliget har a masaukinsu, sun hada da Bola Tinubu, da Yemi Osinbajo da Rotimi Amaechi da Kayode Fayemi da kuma Ahmed Lawan.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta rawaito cewa yayinda gwamononin jihohi suka bai wa daliget din jihohinsu masauki, sauran jihohin da ba APC ke mulki ba, 'yan takara ne suka rinka daukar nauyinsu har da makwanci a otel.

    Wani ɗan majalisa da ke kula da baƙin ya ce an basu abinci da 'yan kuɗaɗe da wajen kwana.

    Sannan ana ta kai komo domin farantawa daliget da kuma shawo kan su gabanni jefa kuri'a

    Mutane 23 ne dai suka shiga wannan fafatawa ta nemen tikitin takara, kuma kawo yanzu babu wani sahihin batu kan maslaha.

  15. Sabbin bayanai na fitowa game da harin Owo

    Ana kara samun sabbin bayanai game da harin nan da 'yan bindiga suka kai a wata coci da ke jihar Ondo a Najeriya a ranar Lahadi, lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama.

    Sabbin bayanan 'yan sanda sun ce maharan sun yi ɓad-da-kama a matsayin masu ibada, da suka halarci cocin kamar kowa.

    Sannan daga bisani suka fara tashin abubuwan fashewar da suke tare da su, yayin da wadanda ke waje suka buɗe wuta.

    Har yanzu dai ba a san dalilin da ya sa suka kai harin a garin Owo da ke kudu maso yammacin ƙasar ba.

    Haka kuma 'yan sanda ba su bayyana adadin wadanda suka mutu a hukumance ba.

  16. APC na shirin zaɓen ɗan takararta na shugaban ƙasa

    A wannan Talatar jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya za ta fitar da gwani da zai kasance ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

    Sai dai, za ta shiga fagen zaɓen fid da gwanin ne, daidai lokacin da ta shiga ruɗani da rarrabuwar kai game da batun ɗan takarar masalaha da goyon bayan mafi rinjayen APC.

    Manyan turakun jam'iyyar sun kasa jituwa kan batun, abin da kuma ya yi matuƙar yamutsa hazo sa'o'i kafin babban taron na yau.

    Shugaba Muhammadu Buhari dai ba shi da damar sake tsayawa takara bisa kudin tsarin mulki, kasancewa wannan ce wa'adinsa ta biyu kan karaga.

    Sama da delagates 700 ake sa ran su jefa kuri'unsu a yau.

    Taron na zuwa na zuwa ne kwanaki biyu bayan kazamin harin bindiga da aka kai kan masu ibada a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    Matsalar tsaro da rashin aikinyi da tsadar rayuwa na daga cikin manyan kalubale da ke gaban sabon shugaban Najeriya a 2023.

  17. Maraba lale

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa barkanmu da safiyar Talata.

    Da fatan za ku kasance da mu a wannan shafin a yau don ku dinga samun labarai da ɗumi-ɗuminsu kan wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya.

    Amma ayau za mu fi mayar da hankali ne kan labaran da suka shafi zaɓen fitar da gwani na jam'iyya mai mulki ta APC a Najeriya.

    Sunana Umaymah Sani Abdulmumin ni ce kuma zan ja ragamar shafin har zuwa lokacin da abokin aikina Mustapha Kaita zai karbe ni.