Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Atiku ya fi karfin Tinubu, in ji PDP

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Umar Mikail, Umaymah Sani Abdulmumin, Halima Umar Saleh and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Daliget na aikinsu

    Zuwa yanzu ban da karakainar daliget babu abin da ake gani a dandalin Eagle Square da ke Abuja, inda jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ke zaɓar ɗan takararta na zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

    Ga hotunan yadda abubuwan ke tafiya:

  2. Daliget ɗin da aka tantance don kaɗa ƙuri'a

    Ga jerin wakilai ko kuma daliget ɗin da aka tantance da za su zaɓi ɗaya daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa guda 14 a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

    • Abiya 50
    • Adamawa 50
    • Anambra 63
    • Bayelsa 24
    • Bauchi 55
    • Benue 64
    • Borno 81
    • Cross River 54
    • Delta 73
    • Enugu 51
    • Ekiti 48
    • Edo 52
    • Ebonyi 38
    • FCT (Abuja) 18
    • Gombe 33
    • Imo 81
    • Jigawa 81
    • Legas 60
    • Filato 81
    • Katsina 102
    • Kebbi 63
    • Kwara 48
    • Kogi 63
    • Kaduna 61
    • Kano 126
    • Nasarawa 39
    • Neja 75
    • Ondo 54
    • Ogun 60
    • Oyo 99
    • Osun 90
    • Rivers 69
    • Sokoto 69
    • Taraba 48
    • Yobe 51
    • Zamfara 42
  3. EFCC ta dira a filin zaɓe

    Kamar yadda ta yi yayin zaɓen fid da gwani na jam'iyyar adawa ta PDP, hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta tura jami'anta dandalin Eagle Square don sa ido kan gilmawar kuɗaɗe.

    Wakilin BBC Hausa Abdulbaki Jari ya ga zuwan jami'an hukumar tun da tsakar ranar Talata.

    Ana ganin zuwan nasu ba zai rasa nasaba ba da zargin da ake yi cewa masu neman takara na raba wa daliget maƙudan kuɗaɗe don su zaɓe su.

    Sai dai jam'iyyun kan musanta zargin kuma ya zuwa yanzu ba mu ji ko EFCC ta kama wani ba bisa zargin raba kuɗi a wurin zaɓen.

    Ana yawan zargin 'yan takara da ba wa daliget dubban dalolin Amurka da zimmar sayen su, abin da daliget ɗin da 'yan takarar ba sa magana a kai balle ma su musanta ko su gaskata.

    Sai dai wani daliget da ya samu kuɗaɗe bayan zaɓen fid da gwani na PDP ya raba wa 'yan mazaɓarsa wasu daga cikin miliyoyin da ya samo:

    • Yadda wani daliget ya raba wa 'yan garinsu kuɗin da ya samo a zaɓen fitar da gwani na PDP
  4. Yawan daliget na kowace jiha

    Jihar Kano ce kan gaba a yawan wakilan da ke kaɗa ƙuri'a na jam'iyyar APC - waɗanda ake kira daliget a turance - inda take da 132.

    Sauran su ne:

    Arewa maso yamma: 558

    Kano - 132

    Katsina - 102

    Jigawa - 81

    Kaduna - 69

    Sokoto - 69

    Kebbi - 63

    Zamfara - 42.

    Kudu maso yamma: 411

    Oyo - 99

    Osun - 90

    Ogun - 60

    Legas - 60

    Ondo - 54

    Ekiti - 48

    Kudu maso kudu : 372

    Akwa Ibom - 93

    Delta - 75

    Rivers - 69

    Edo - 57

    Cross River - 54

    Bayelsa - 24

    Arewa ta tsakiya: 360

    Neja - 75

    Benue - 66

    Kogi - 63

    Filato - 51

    Kwara - 48

    Nasarawa - 39

    Abuja - 18

    Arewa maso gabas: 336

    Borno - 81

    Adamawa - 63

    Bauchi - 60

    Yobe - 51

    Taraba - 48

    Gombe - 33

    Kudu maso gabas: 285

    Imo - 81

    Anambra - 63

    Abia - 51

    Enugu - 51

    Ebonyi - 39

  5. Kalli jawabin Shugaba Buhari

    Kuna iya kallon jawabin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya yi kafin a fara kaɗa ƙuri'a.

    A ciikin jawabin ne ya nemi 'yan Najeriya su tabbata ba su bar jam'iyyar adawa ta PDP "ta mayar da ƙasa baya ba".

  6. Daliget na Abiya ne za su fara jefa ƙuri'a

    Mai gabatarwa ta kira masu kaɗa ƙuri'a daga Jihar Abiya a kudu maso gabashin Najeriya don su fara jefa ƙuri'unsu ga 'yan takarar da suke so.

  7. Ana wayar da kan daliget kan sunan 'Ahmed' uku da ke takara

    Masu gabatarwa na wayar da kan masu jefa ƙuri'a wato daliget cewa su tabbatar sun rubuta sunayen 'yan takarar da suke son zaɓa da kyau a kan takaradar saboda akwai sunayen 'yan takarar da ya zo ɗaya.

    Misali, akawai masu suna Ahmed har mutum uku da suka haɗa da Bola Ahmed Tinubu, da Ahmed Sani, da Ahmed Rufai Sani.

    "Duk wanda ya rubuta ' Ahmed' kawai za a jefar da ƙuri'arsa, wajibi ne ya rubuta cikakken sunan wanda yake so," a cewar APC.

    Kazalika, akwai farfesa biyu da ke takarar. Su ne Farfesa Ben Ayade da Farfesa Yemi Osinbajo. "Duk wanda ya rubuta farfesa kawai ƙuri'arsa ba ta yi ba."

  8. Kaɗa ƙuri'a ne ya rage yanzu

    Bayan Shugaba Muhammadu Buhari, shugaban kwamatin zaɓe na wannan taro Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu ya sanar cewa za a fara kiran daliget don kaɗa ƙuri'unsu.

    Tuni masu neman takara takwas suka janye, inda bakwai ke goyon bayan Bola Tinubu ɗaya kuma ke mara wa Yemi Osinbajo baya.

    'Yan takarar da za a jefa wa ƙuri'a yanzu su ne:

    • Yemi Osinbajo (Jihar Ogun)
    • Ahmad Lawan (Jihar Yobe)
    • Bola Tinubu (Jihar Lagos)
    • Tein Jack-Rich (Jihar Rivers)
    • Rochas Okorocha (Jihar Imo)
    • Tunde Bakare (Jihar Ogun)
    • Rotimi Amaechi (Jihar Rivers)
    • Emeka Nwajiuba (Jihar Imo)
    • David Umahi (Jihar Ebonyi)
    • Ogbonnaya Onu (Jihar Ebonyi)
    • Ben Ayade (Jihar Cross River)
    • Yahaya Bello (Jihar Kogi)
    • Ikeobasi Mokelu (Jihar Anambra)
    • Ahmed Rufai Sani
    • Ahmed Yerima
  9. Labarai da dumi-dumi, Buhari ya roƙi 'yan Najeriya 'kada ku ƙyale PDP ta mayar da Najeriya baya'

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya su tabbata ba su bar jam'iyyar adawa ta PDP "ta mayar da ƙasa baya ba".

    Da yake jawabi a wurin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyarsu ta APC, Buhari ya ce APC ta sauya Najeriya ta hanyar gudanar da ayyukan raya ƙasa.

    "Wajibi ne mu zaɓi masu adalci 'yan kishin ƙasa da ke da aƙidar haɗa kan ƙasarmu...don ciyar da ita gaba.

    "Bai kamata mu ƙyale PDP ta mayar da Najeriya baya ba."

    Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton PDP ba ta mayar da martani ba, wadda tuni ta zaɓi Atiku Abubakar a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a babban zaɓe na 2023.

  10. Ku zaɓe ni na ɗora a kan halin Buhari - Ike Obasi

    Mai neman takarar sugaban ƙasa a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Ike Obasi, ya ce Shugaban Ƙasa Buhari "ba ɓarawo ba ne", yana mai neman daliget su zaɓe shi don ya ɗora kan irin halin shugban.

    "Kun taɓa jin Buhari ya saci wani abu?" kamar yadda ya tambayi masu sauraro.

    "Ba shi da gidan mai ko ɗaya, ko famfon mai ba shi da da shi. Ku zaɓe ni na ɗora kan halin Buhari."

  11. Ku zaɓe ni don na samar da ayyukan yi - Osinbajo

    Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya nemi wakilai wato deliget su zaɓe shi don ya yi wa jam'iyyar APC takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

    Kafin jawabin nasa, hayaniyar da wasu magoya baya ke yi ta kawo masa tsaiko, inda suka hana shi gudanar da jawabi a wajen taron na APC.

    "Na gode, na gode sosai," abin da Osinbajo ya dinga faɗa musu ke nan amma da kyar suka bar shi ya yi jawabin.

  12. Labarai da dumi-dumi, Mutane sun hana Osinbajo yin jawabi

    Hayaniyar da wasu magoya baya ke yi ta hana Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo gudanar da jawabi a waje taron APC.

    "Na gode, na gode sosai," abin da Osinbajo ke ta faɗa musu ke nan amma har yanzu suna ci gaba da ɗaɗɗaga hannu tare da yin sowa.

  13. Labarai da dumi-dumi, Uju Ohanenye ta janye wa Bola Tinubu

    Mace ɗa tilo da ke neman takara a APC, Uju Ohanenye, ta ce ta janye kuma ta mara wa Bola Ahmed Tinubu baya.

    Ita ce 'yar takara ta bakwai da ta janye wa Tinubu a wanna dare yayin da ake ƙara kusantar jefa ƙuri'a tsakanin waɗanda suka rage.

    Ta nemi daliget su zaɓi tsohon gwamnan na Legas, wanda ya zuwa 'yan takara bakwai suka janye takararsu saboda shi.

  14. Ni ne gwamna Musulmi na farko a Arewa da ya gina wa Kiristoci coci a gidan gwamnati - Yahaya Bello

    Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello kuma mai neman APC ta ba shi takarar shugaban ƙasa a Najeriya ya ce daga cikin abubuwan da ya cimma har da zama gwamna Musulmi na farko a yankin Arewa da ya gina wa mabiya addinin Kirista coci a gidan gwamnatin jihar.

    Bello ya ƙara da cewa a loƙacin da yake gwamna ba a taɓa yajin aiki a jiharsa ba - BBC ba ta tabbatar da wannan ikƙirarin nasa ba.

    Kazalika, ya nemi daliget su zaɓe shi a matsayin ɗan takarar shugban ƙasa a babban zaɓe na 2023.

  15. Janye wa Bola Tinubu da 'yan takara ke yi alamun nasara ce - Gwamna Ganduje

    Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya faɗa wa BBC Hausa cewa janyewar da suke don mara wa Bola Ahmed Tinubu baya alamu ne cewa ɗan takarar tasu zai yi nasara.

    Ganduje ya faɗi hakan ne yayin da yake tattaunawa da Buhari Fagge a dandalin Eagle Sqaure, inda taron jam'iyyaer APC ke gudana yanzu haka.

    "Wannan alamar nasara ce kuma ka ga yadda kowa yake murna saboda ɗan takararmu Bola Tinubu ya fi sauran 'yan takara cancanta," in ji shi.

    Ku garzaya shafinmu na Facebook don kallon taron kai-tsaye.

  16. Ni Rochas ɗan jikan Sokoto, ni na san matsalar Arewa - Rochas Okorocha

    Tsohon Gwamnan Jihar Imo Sanata Rochas Okorocha ya soki sauran masu neman takara a jam'iyyar APC cewa ba su san matsalar arewacin ƙasar ba.

    Da ya sauya harshe daga Ingilishi zuwa Hausa sai ya ce: "Ku tambaye su me suka yi muku...ni Rochas ɗan jikan Sokoto, ni ne na san matsalar Arewa."

    Ya ƙara da cewa ni ne kwamandan bai wa yara ilimi kyauta a Najeriya.

    "Wallahi billahillazi babu wanda ya kai ni son Najeriya da arewa a cikinsu" in ji Rochas kamar yadda ya fada cikin harshen Hausa.

    Kazalika Rochas ya ce ya sha so ya bar siyasa, amma idan "na tuna da tsofaffi da yara da wadanda mazajensu suka mutu suka bar su da talakawa, sai na fasa."

  17. Labarai da dumi-dumi, Nicholas Felix ya janye wa Yemi Osinbajo

    Nicholas Felix ya janye wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo takararsa.

    Shi ne ɗan takara na farko da ya janye wa Osinbajo ya zuwa yanzu.

    Msta Felix ya ce ba zai yarda da ɗan takara Musulmi sannan mataimakinsa ma Musulmi ba, kalaman da suka zama na gugar zana ga ɗan takara ga Bola Tinubu.

    Tuni mutum shida suka janye wa Bola Ahmed Tinubu.

  18. Ba a yi wa 'yan ƙabilar Igbo adalci a siyasar Najeriya - Ogbonnaya Onu

    Dan takarar shugaban kasa a zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC Ogbonnaya Onu ya ce ba a yi wa 'yan kabilar Igbo adalci a tsarin siyasar Najeriya.

    Mista Onu wanda tsohon ministan kimiyya da fasaha ne ya ce tun daga shekarar 1999 da aka koma mulkin dimokuradiyya yankin Yarabawa da Arewa ne suke karba-karba.

    "Ba a yi wa yankin kudu maso gabas adalci. Ina adalcin ya ke? Ana nuna mana wariya," in ji shi.

    A karshe dan takarar ya ce ba zai janye wa kowa ba kuma za a ci gaba da fafatawa da shi.

  19. Amaechi zuwa ga daliget: 'Kar ku zaɓe ni idan ba ku ga cancantata ba'

    Tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya roƙi daliget da kada su zaɓe shi idan har ba su ga cancantarsa ba.

    Sai dai kuma ya ce shi ne ya fi sauran dukkan 'yan takara ƙwarewa saboda muƙaman da ya riƙe a siyasance.

    "Na yi gwamna shekara takwas...na yi ɗan majalisa...na yi minista."

  20. Labarai da dumi-dumi, Ba zan janye wa kowa ba - Tunde Bakare

    Fasto Tunde Bakare ya ce bai shiga neman takarar shugaban ƙasa a APC ba don ya janye wa wani.

    "Da yawa daga cikin waɗannan 'yan takarar suna da matsala da hukumar EFCC," in ji shi yayin da yake magana kan ƙwarewarsa a harkokin mulki.

    Ya bayyana hakan ne yayin da yake tabbatar da cewa bai taɓa riƙe wani muƙamin siyasa ba, amma ya ce "da yawa daga cikin waɗanda suke da ƙwarewar su suka lalata ƙasa [Najeriya]".