Shugaban kwamatin zaɓen fid da gwani na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu, ya bayyana cewa wasu wakilai na jihohi sun yi ƙorafin samun matsala.
Wannan na cikin dalilan da suka sa kaɗa ƙuri'a ya tsaya cak yanzu haka bayan wakilan Abiya da na Kano da Adamawa sun kaɗa ƙuri'unsu.
Sai dai gwamnan ya ce matsalar ta faru ne tun a wajen tantancewa sannan ya nemi jihohin da ba su fuskanci matsalar ba da su ci gaba da jefa ƙuri'iunsu.
Amma da alama matsalar ta wuce yadda aka bayyana tun farko domin kuwa yanzu haka an tsaya cak da jefa ƙur'ia.
Wakilin BBC da ke wajen, Buhari Muhammad Fagge, ya ce da alama za a iya kaiwa ƙarfe 9:00 na hantsin Laraba ba a kammala wannan zaɓe ba.