Tarayyar Turai za ta fara aika wa Ukraine makamai

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Mun kawo ƙarshen rahotannin a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe za mu kawo sabbin rahotanni a wani shafin daban.

    Mu zama lafiya.

  2. Sweden za ta aika wa Ukraine makamai

    Sweden ta sanar cewa za ta aika wa Ukraine kayan yaƙi da sauran tallafi.

    Da take sanar da matakin, Firaminista Magdalena Andersson ta ce wannan ne karon farko da Sweden ke tura wa wata ƙasa da ke yaƙi kayan faɗa tun bayan 1939 da Tarayyar Soviet ta afka wa Finland.

    Ta ce kayan za su ƙunshi makaman harbe tankoki 5,000 da riguna masu silke 5,000 da hular kwano 5,000 da kuma ƙunshin harsasai 135,000.

    "Na fahimci cewa tsaronmu shi ne kawai idan muka taimaka wa Ukraine ta kare kanta daga harin Rasha," a cewarta.

    Ita ma ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta aika da makamai zuwa Ukraine ɗin karon farko a tarihinta.

  3. Wasu 'yan Najeriya sun isa Poland

    Wasu 'yan Najeriya sun samu damar tsallakawa zuwa Poland mai maƙotaka da Ukraine.

    Wani da ake zaton jami'in jakadancin Najeriya ne a Poland ya wallafa wani bidiyo a shafin Twitter yana mai cewa aƙalla 'yan Najeriya bakwai ne suka isa sansani ɗaya daga cikin waɗanda gwamnatin Poland ta ware.

    "Na samu damar ganin 'yan Najeriya bakwai a nan, yanzu haka suna cin abinci. Idan sun gama za mu ɗebe su zuwa wani wurin daban," a cewar wanda ya ɗauki bidiyon da hukumar 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta wallafa.

    Hukumomi a Najeriya na shawartar 'yan ƙasar su tsallaka ƙasashen Poland da Hungary masu maƙotaka da Ukraine tun bayan Rasha ta fara kai hare-hare a ranar Alhamis.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Makaman da aka harba daga Belarus sun faɗa kan filin jirgi a Ukraine

    Mai ba wa ministan harkokin wajen Ukraine shawara ya ce wani makami mai linzami da aka harba daga Belarus ya faɗa kan wani filin jirgin sama a birnin Zhytomyr.

    "Wannan ne abin da makamai suka hara daga Belarus da misalin ƙarfe 5:00 na yamma...mahara daga Belarus da Rasha sun hari filin jirgi na Zhytomyr," a cewar Anton Herashchenko cikin wani saƙo a Telegram.

    Wakilan Rasha da na Ukraine za su haɗu a kan iyakar Belarus da Ukraine, kamar yadda ofishin shugaban Ukraine ɗin ya faɗa ɗazu ba tare da bayyana yaushe ba.

  5. Shugaban Ukraine ya amince ya tattauna da Rasha a iyakar Ukraine da Belarus

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelinsky ya ce ya amince ya sasanta da Rasha a wani wuri kan iyakar Ukraine da Belarus

    Mista Zelensky ya ce a tattaunawar da ya yi da shugaban Belarus Alexander Lukashenko, Ukraine ta amince ta gana da Rasha ba tare da wani sharaɗi ba a kan iyakar Ukraine da Belarus a kusa da kogin Pripyat.

    Shugaban Ukraine ya ce Mista Lukashenko ya ce ya ɗauki alhakin tabbatar da dakatar da shawagin dukkanin jiragen sama, masu saukar angulu da masu kakkabo makamai mai linzame lokacin ziyarar domin tattaunawar tsakanin ɓangarorin biyu.

    Tun da farko Msita Zelensky ya yi watsi da tayin Rasha na hawa teburin tattaunawa da Belarus. Ya ce ya fi buƙatar a tattauna a wata ƙasa saɓanin Belarus.

    Belarus babbar aminiyar Rasha ce a yaƙin da take da Ukrainer.

    Rasha ta sanar a ranar Lahadi cewa ta tura wakilai Belarus domin tattaunawa da jami'an Ukraine.

  6. Labarai da dumi-dumi, Tarayyar Turai za ta fara aika wa Ukraine makamai

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta European Union (EU) ta sanar da cewa za ta fara aika makamai zuwa Ukraine.

    Wannan ne karon farko da EU za ta yi hakan a tarihinta.

    Da take magana yayin taron manema labarai a yammacin nan, Shugabar Hukumar Turai Ursula von der Leyen ta ce yunƙurin na nufin "samun sauyi".

    Ta kuma sanar da wasu jerin takunkumai da aka saka wa Rasha da Belarus, ciki har da hana jiragen ƙasar bi ta sararin samaniyar ƙasashen ƙungiyar.

  7. Labarai da dumi-dumi, Tarayyar Turai EU ta hana jiragen Rasha bi ta ƙasashen ƙungiyar

    Jirgin Rasha

    Asalin hoton, @aeroflot

    Jiragen Rasha na fuskantar rashin hanya kwatakwata a nahiyar Turai ƙungiyar Tarayyar Turai ta sanar da matakin hana wa jiragen bi ta sararin samaniyar ƙasashen ƙungiyar.

    Tun farko ƙasashen na Turai ɗaya bayan ɗaya suka ce za su rufe sararin samaniyarsu ga jiragen Rasha, ciki har da Jamus na tsawon wata uku.

    Yayin da aka rufe samaniyar Ukraine, yanzu jiragen na da tsirarun hanyoyin da za su iya bi a nahiyar.

    Gomman jirage a filayen jirage na Domodedovo da Sheremetyevo sun soke jigila a yau Lahadi, ciki har da na zuwa Paris, Faransa, da Vienna da Kaliningrad.

  8. Yadda sojojin Ukraine ke gumurzu da na Rasha a birnin Kharkiv

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyon

    Dakarun Ukraine sun ce sun daƙile harin sojojin Rasha a garin Kharkiv na biyu mafi girma a ƙasar bayan ƙazamar fafatawa.

  9. Sojojin Ukraine sun 'fatattaki na Rasha' daga birnin Kharkiv

    Kharkiv

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun Ukraine sun ce sun daƙile harin sojojin Rasha a garin Kharkiv na biyu mafi girma a ƙasar bayan ƙazamar fafatawa.

    Gwamnan yankin, Oleh Synehubov, ya ce yanzu an fatattaki dakarun na Rasha daga garin bayan gumurzun da suka yi a kan tituna.

    Dubban mutane ne suka kwana a gidajen ƙarƙashin ƙasa, yayin da wani mazaunin garin ke siffanta yanayin da wani fim ɗin Amurka mai suna Star Wars.

    "Wata fashewa mai mugun ƙara ta sa kunnuwana sun motsa," a cewar wani.

  10. WeTogether: Matasan da ke son haɗin kan Najeriya

    Da alama tayar da jijiyoyin da dattawan bangarorin Najeriya suka yi ta yi a baya-bayan nan sakamakon tabarbarewar al’amura kan cewa a raba kasar kowa ya kama gabansa, ba zai yi tasiri ba domin kuwa matasa da dama ba su karbi wannan tunani ba.

    Hasali ma matasan na son kasancewar Najeriya kasa daya al’umma daya.

    Ibrahim Hussain Abdulkarim, shi ne shugaban kungiyar matasa da ke son dunkulewar Najeriya da ake kira WeTogether.

    A tattaunawarsa da Usman Minjibir, ya ce rashin shugabanci mai kyau ne matsalar Najeriya amma ba wargajewar kasar ba.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari hirar:

    Bayanan sautiWeTogether: Matasan da ke son haɗin kan Najeriya
  11. Shugaban Ukraine ya amince ya "tattauna da Rasha a iyakar Ukraine da Belarus"

    Volodymyr Zelinsky

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelinsky ya ce ya amince ya sasanta da Rasha a wani wuri kan iyakar Ukraine da Belarus

    Mista Zelensky ya ce a tattaunawar da ya yi da shugaban Belarus Alexander Lukashenko, Ukraine ta amince ta gana da Rasha ba tare da wani sharaɗi ba a kan iyakar Ukraine da Belarus a kusa da kogin Pripyat.

    Shugaban Ukraine ya ce Mista Lukashenko ya ce ya ɗauki alhakin tabbatar da dakatar da shawagin dukkanin jiragen sama, masu saukar angulu da masu kakkabo makamai mai linzame lokacin ziyarar domin tattaunawar tsakanin ɓangarorin biyu.

    Tun da farko Msita Zelensky ya yi watsi da tayin Rasha na hawa teburin tattaunawa da Belarus. Ya ce ya fi buƙatar a tattauna a wata ƙasa saɓanin Belarus.

    Belarus babbar aminiyar Rasha ce a yaƙin da take da Ukrainer.

    Rasha ta sanar a ranar Lahadi cewa ta tura wakilai Belarus domin tattaunawa da jami'an Ukraine.

  12. Putin ya umarci sojojin da ke kula da makaman nukiliya su kasance cikin shiri

    Shugaban Rasha Putin

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya umurci kwamandojin sojin ƙasar su shirya sojojin Rasha masu kula da makaman nukiliya su kasance cikin shiri.

    Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa a fadar Kremlin wanda ministan tsaro da kwamandan sojojin kasar suka halarta.

    Mista Putin ya ce manyan jami'an ƙasashen yammaci sun yi kalamai masu zafi kan Rasha.

    Ya kira takunkuman da kasashen yammaci suka ƙaƙabawa kasarsa a matsayin haramtattu.

  13. An kashe fararen hula sama da 200 a Ukraine

    Hukumomin Ukraine sun sama da fararen hula 210 aka kashe yayin da 1,100 suka jikkata tun lokacin da Rasha ta fara mamayar ƙasar.

    Mai magana da yawun gwamnati Lyudmyla Denysova ta ce "makiya suna tarwatsa gidajen mutane da asibiti da makarantu suna hana ƴaƴan Ukraine ƴancin walwala a ƙasarsu."

    Denysova ta bayar da misalin yadda aka kashe wasu fararen hula da suka kunshi yaro da ya gamu da ajalisansa a harin da aka kai asibiti a Kyiv da kuma wata mata da aka kashe bayan harin makami mai linzami da aka kai a wani gida a Kharkiv.

    Ta ce Ukraine na adana waɗannan hujjojin na munananan ayyukan Rasha domin gabatar da su a kotun duniya ta Hague

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

  14. Baƙaƙen fata ƴan Afirka sun ce ana nuna masu wariya a iyakokin Ukraine

    'Yan Afirka da ke kokarin tsere wa daga Ukraine na ƙorafin fuskantar wariya a kan iyakokin Ukraine zuwa cikin Tarayyar Turai.

    Wata daliba ƴar Najeriya da ke karatun likitancia wata jami'a a Kharkiv, ta ce yi tafiya na tsawon sa'a 11 cikin dare kafin ta isa Medyka-Shehyni, da ke kan iyaka da Poland.

    "Lokacin da na zo nan na ga baƙaƙen fata suna bacci kan titi," kamar yadda ta shaida wa wakiliyar BBC.

    Ta ce jami'an tsaron kan iyaka sun shaida mata cewa ta jira har dai ƴan Ukraine sun wuce sannan. Ba ta iya tantance ko masu gadin kan iyakar na Ukraine ne ko kuma Poland.

    Ta ce ta ga an cika motocin bas da mutane waɗanda ta bayyana fararen fata, da aka amince su tsallaka kan iyaka, yayin da kuma ake zaɓen baƙaƙen fata da suka yi layi suna jiran tsammani.

    Ruqayya na ƙoƙarin shiga Warsaw ne domin samun jirgin da zai dawo da ita gida Najeriya.

    Isaac ya ce ya wuraren ƙarfe 4.30 na safe ya isa kan iyakar Medyba kuma ya ce an faɗa masa cewa sai ƴan Ukraine da ƴan Turkiya sun wuce kafin baƙaƙen fata.

    Jami’an kula da kan iyakokin Poland sun ce suna barin duk wanda ya fito daga Ukraine shiga ƙasar.

    Ofishin jekadancin Najeriya a Poland ya ce ya tura jami’ansa zuwa kan iyakoki domin taimakawa ƴan ƙasar tsallakawa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Ministan harakokin wajen Najeriya ya ce suna koƙari tare da ofisoshin jakadancin ƙasar a Ukraine da Poland da Rasha da Romania da Hungary domin tabbatar da ƴan Najeriya da ke son fice daga Ukraine sun dawo gida, tare da taimakawa waɗanda suka zaɓi ci gaba da zama a ƙasar

  15. Leeds United ta kori kocinta Marcelo Bielsa

    Leeds

    Asalin hoton, Getty Images

    Leeds United ta kori kocinta Marcelo Bielsa bayan abubuwa sun taɓarɓare, musamman kashin da ƙungiyar ta sha hannun Tottenham

  16. Dakarun MNJTF sun kashe ƴan Boko Haram 20 a Nijar

    Aƙalla mayaƙa 20 da ake kyautata zaton ƴan Boko Haram ne aka kashe a kudancin Nijar a wani farmaki da dakarun haɗin guiwa suka kai, kamar yadda Jaridar ActuNiger ta ruwaito.

    Sanarwa daga rundunar dakarun haɗin guiwa ta MNJTF ta ce sojojin sun kai farmaki ne tsakanin ranakun 12 zuwa 15 ga Fabrairu bayan hare-haren Boko Haram sun yi ƙamari a yankin rafin kogin Komadougou na Yobe da ke kan iyakar Nijar da Najeriya.

    Rundunar ta ce sojojinta na ƙasa tare da taimakon na sama sun tarwatsa ƴan Boko Haram a ƙauyukan Bague da Kiassa da Digaya da Boulayi da Boulagana da Jabulam da Abadam.

    ActuNiger ta ce akalla mutum 20 yawancinsu mata aka sace tun a farko Fabrairu a yankin da ke kan iyaka da jihar Borno mai dama da hare-haren Boko Haram.

  17. Aƙalla mutum 200,000 suka tsere Ukraine

    More than 150,000 people have fled Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu sabbin alƙalumma sun nuna cewa kimanin mutum 200,000 suka yi gudun hijira daga Ukraine zuwa makwabta

    Hukumomin Slovakia sun ce cikin sa'a 24 daga 6 na safiyar Asabar, kusan mutum 10,000 suka shiga ƙasar daga Ukraine.

    Ƴan Ukraine sama da mutum 43,000 suka tsallaka Romania a kwanaki uku da Rasha ta ƙaddamar da mamayar ƙasar, yayin da 150,000 suka shiga Poland.

    Ukraine tana kuma iyaka da ƙasashe huɗu - Hungary da Moldova, inda dubban mutane suka tsallaka ƙasashe da kuma wasu da suka shiga Belarus da Rasha.

  18. Shugaban Ukraine ya roƙi ƙasashen duniya su zo su yaƙi Rasha

    Shugaban Ukraine ya roƙi mayaƙa na ƙasashen waje da su haɗa ƙawance a Ukraine domin yaƙar Rasha.

    Shugaba Zelensky ya yi wannan kiran a shafukansa na na sada zumunta inda ya gayyaci ƙasashe da su goyi bayan Ukraine.

    Sanarwar ta ce: "Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky yana kira ga dukan al'ummar duniya, abokan Ukraine, masu son zaman lafiya da ci gaban demokradiyya.

    "Duk wanda ke son tsaron Ukraine, Turai da kuma duniya yana iya zuwa ya taimaki 'yan Ukraine yaƙar masu aikata laifukan yaki na Rasha."

    Shugaban na Ukraine ya sha nanata yadda aka bar ƙasarsa ta kare kanta da kanta

  19. Putin ya yaba wa aikin sojojin Rasha a Ukraine

    Shugaba Putin

    A wani jawabi da ya yi wa al'ummar kasar Rasha ta talabijin, shugaba Vladimir Putin ya yaba tare da godiya ga sojojin Rasha da ya yi iƙirarin cewa suna gudanar da ayyukansu a Ukraine yadda ya kamata.

    Ya ce an ɗora wa sojojin nauyin aikin bayar da taimako ga jamhuriyar jama'ar Donbas - yankuna biyu da Rasha ta amince da su a matsayin masu cin gashin kai.

    Kamfanin dillancin labaran Interfax ya ce Mista Putin ya kuma yi magana da shugaban Azarbaijan game da abin da ya bayyana a matsayin farmakin soji na musamman na Rasha.

  20. Jamus za ta aika wa Ukraine da makamai

    Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya ce kasarsa za ta kai wa Ukraine makamai.

    Olaf Scholz, ya ce hare-haren da Rasha ke kai wa kasuwannin Ukraine ya fara ɗaukar sabon salo.

    Ya ce gwamnatinsa za ta kai makaman da za su lalata tankokin yakin Rasha guda 1000, da makamai 500 da za su kakkabo makamai masu linzami.

    Tun da fari jakadan Ukraine a Berlin Andriy Melnyk ne ya roki Jamus ta kai musu ɗauki.

    Ya ce mutanen Kyiv, za su kare duk wani gini da gidajensu, amma ba su da makamai da yawa, lokaci ya yi da za a taimaka ma su da makamai;

    Shi ma Firaministan Australia Scott Morrison, ya ce zai aika da na shi tallafinga Ukraine, duk da cewa kasarsa ba ta cikin kawancen NATO