Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.
Rahoto kai-tsaye
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Donald Trump ya ce yana yi wa ƴan Ukraine addu’a
Asalin hoton, Reuters
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi Allah wadai damamayar da Rasha ta yi wa Ukraine tare da cewa yana yi wa ƴan kasar addu'a.
Mista Trump ya yi kalaman ne a wani taro da aka yi a
birnin Florida.
Kalamansa ya sha bamban da wanda ya yi gabannin Rasha ta ɗauki
matakin mamayar Ukraine, inda a lokacin da ya yabawa matakin shugaba
Vladimir Putin, na tura dakarun wanzar da zaman lafiya Ukraine tare da cewa
hakan ya dace.
Ya kara da cewa ya yi amanna Amurka za ta iya daukar irin
wannan matakin domin kare tsaron kudancin iyakarta.
Ɗaliban Sokoto a Ukraine sun shaida wa Gwamna Tambuwal halin da suke ciki
Asalin hoton, Sokoto State Govt
Wasu ɗaliban
Najeriya ƴan asalin jihar Sokoto da rikicin Rasha ya rutsa da su a Ukraine sun yi
kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta kwashe su domin suna ganin daman barin ƙasar
zai gagara nan ba da dadewa ba idan lamarin ya tsananta.
Ɗaliban da aka
bayyana guda 22 sun yi wannan kiran ne a zantawar da gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya haɗa ta kafar
zoom da su tare da kuma iyayensu daga gidan gwamnatin jihar.
Sanarwar da
gwamnatin jihar ta fitar ta ce ɗaya daga cikin ɗaliban mai suna Aisha Kabir ta
shaida wa gwamnan cewa halin da ake ciki a Kharkiv ya tsananta.
Rahotanni a
safiyar Lahadi sun ce sojojin Rasha sun kutsa Kharkiv kuma ana gwabza faɗa a
birnin na biyu mafi girma a Rasha.
“Muna jin ƙarar
harbe-harbe, ko da yake ana ƙoƙarin tafiya da mu cikin bus zuwa Romania, amma
direbobin suna jin tsoron za a iya kai masu hari, muna ganin jirgin ƙasa ne ba
ya da hatsari wanda za mu yi sauƙin ficewa.” In ji ɗalibar kamar yadda sanarwar da
mai magana da yawun gwamnan Muhammad Bello ya fitar ta bayyana.
Wani ɗalibin kuma
Shuaibu Muhammad, ya ce suna fuskantar ƙalubale a Krakow na Poland domin ba
isasshen abinci da wurin bacci mai kyau. “Daga Lviv zuwa Krakow tafiyar awa 12
ce, kuma yawancinmu ba mu san kowa ba da za mu yi magana da shi lokacin da muka
iso.
Wasu sun ce suna
fuskantar ƙalubale na yanayin sanyi da rashin tufafin da ya dace da bargon
bacci.
Wata ɗaliba Zarah
Ibrahimn ta bayyana fargabar cewa “ta ji ana faɗi daga gobe za a hana wa ƴan
ƙasashen waje fita Lviv, tana mai jaddada cewa Kharkiv na tattare da hatsari”
A nasa ɓangaren
gwamnan jihar ya yi wa ɗaliban alƙawalin cewa da su da sauran ɗalibai ƴan
Najeriya za su fice daga Ukraine nan ba da dadewa ba kuma su dawo gida lafiya.
Gwamnan ya ce ya
ba ma’aikatar kuɗi ta jihar umarnin ta tura wa ɗaliban da ke cikin mawuyacin
hali tallafin kudi kimanin dala 200 zuwa 300.
Iyayen ɗaliban
sun yaba kan yadda gwamnatin
Sokoto ta nuna damuwarta da kuma tausayin ƴaƴansu tare da jan hankalin ƴaƴansu da
su yi taka-tsan-tsan a yayin ficewa Ukraine.
Ana gwabza faɗa a Kharkiv
Rahotanni sun ce ana gwabza
faɗa a garin Kharkiv bayan da sojojin Rasha suka abka birnin, kamar yadda jami’ai
suka bayyana.
Wasu hotunan bidiyo a kafofin
sada zumunta sun nuna wasu sojojin Rasha a birnin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Akwai kuma wasu hotunan da suka nuna motocin yaƙin Rasha na ci da wuta a birnin.
Sai dai BBC ba ta tantance sahihancin hotunan bidiyon ba
Hukumomi a Kharkiv sun yi kira ga mazauna birnin su zauna a gida su kaucewa fitowa kan titi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Maraba
Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin inda muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya