Labarai da dumi-dumi, Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ya kamu da coronavirus
Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya Muhammad Babandede ya kamu da cutar coronavirus.
Shugaban ya tabbatar wa BBC hakan a safiyar Lahadi inda ya ce sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa yana dauke da cutar.
Ya ce a makon da ya gabata ne ya dawo daga kasar wanda hakan ya ga cewa ya kamata yayi gwajin wannan cuta.
Shugaban ya bayyana cewa tuni ya killace kansa a gida.