Kenya ta haramta yin safarar kayan gwanjo zuwa kasar wanda aka fi sani da suna mitumba a yunkurinta na yaki da yaduwar cutar cornavirus.
Jaridar Daily Nation da ake bugawa a kasar ta ambato sakatariyar kasuwancin kasar Betty Maina, tana cewa: "An dakatar da safarar kayan gwanjo nan take domin kare lafiyar 'yan kasar Kenya da kuma karfafa kasuwar cikin gida."
Mutane da dama na sayen kayan da aka taba yin amfani da su a Turai da Kudancin Amurka da China - saboda sun fi saukin kudi sama da sababbi.
Kazalika 'yan kasar da dama sun dogara da kasuwancin mitumba domin samun na kai wa baka.
A ranar Laraba ne Ms Maina ta gana da 'yan kasuwar gwanjon, inda ta karfafa masu gwiwa tare da shawartarsu da su sayi kayan daga ma'aikatun cikin gida.
Sai dai wasu ba su ji dadin matakin ba. Dan majalisa mai wakiltar Kamukunji a kasar, inda cibiyar kasuwar mitumba take, ya bayyana rashin dadinsa a Twitter.
"Duk da cewa dole ne gwamnati ta dauki matakin kare rayukan al'umma, amma na yi mamakin rufe kasuwar Mitumba. Dubban 'yan Kenya sun dogara da ita domin samun kudin shiga."