Kamfanin dillancin labarai na AFP ya wallafa cewa akalla akwai mutum 2000 da suka kamu da cutar coronavirus a nahiyar Afirka, inda mutum 62 suka mutu sakamakon cutar.
Kasar Afirka ta kudu ce dai take da yawan alkaluman wadanda suka kamu inda mutum 709 suka harbu.
Kasashen Soa Tome and Principe da Kamaru sun sanar da mutuwar farko sakamakon cutar.
'Yan Kamaru na kuma yin alhinin fitaccen mawakin nan dan kasar Dibango Manu wanda cutar ta yi ajali kasar Faransa.
Rwanda ta sanar da samun mutum hudu da suka harbu, inda yanzu haka suke da jumullar mutum 40.
Yanzu haka Najeriya na da wadanda coronavirus ta harba guda 46.
Rahotanni na cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari yana killace, sannan kuma shugaban ma'aikatansa, Abba Kyari ya harbu da cutar.
Daya daga cikin gwamnonin jihohin kasar, Bala Muhammad wanda shi ne gwamnan Bauchi, shi ma cutar ta kama shi.
Ita kuwa Cote
d'Ivoire na da mutum 73 da ke dauke da cutar.
Ghana ma ta samu masu dauke da cutar ta coronvirus a cikin kasar guda 53 ya zuwa yanzu.
A jamhuriyar Niger, mutum daya ya mutu sakamakon cutar.